Hassan Garo" />

Tafiya mabudin ilmi: Daular Tsar Ta ’Yan Bolshebics

Ina zaune a gida bayan na dawo daga zagayen zumunchi na gaisuwar sallah aka kirani a waya ake fadamin takardar izini na ta tafiya Rasha ta fito, na cika da murna da farinciki saboda dalilai biyu, na farko nasan tsananin wahalar zuwa kasashen da ake kira ‘Iron Curtain’ na gabashin turai, wanda in banda arzikin kallon kowa na gasar Kwallon kafan duniya lallai bisar Russia akwai wahala sannan kuma ina cike da murna saboda ban san iyakacin littattafan da na karanta a matsayina na dalibin tarihi (history) zuwa karance-karancen litattafai da sauran shirye-shirye akan Rasha ba.
Mun tashi daga Tashar jirgi ta Legas muka hau Air maroc zuwa Casablanca, wanda daga nan ne kuma zamu hadu da sauran matafiya mu dauki hanya a abin da ake kira (transit)
A Casablanca mun yi kusan awa biyar a ‘transit’ kafin mu dauki hanya. Bisa al’ada ta ko yaushe zan yi tafiya na kan zabi zama a Tagar jirgi ne (ko da kuwa ‘boarding pass’ dina bai nuna hakan ba, na kan roki wanda yake da kujerar tagar mu yi musanyen kujera) saboda tsawon tafiya na kan kalli majigin talabijin din jirgi na rika lissafin ‘Latitude, metres, degrees da maps’ har zuwa karshen tafiyarmu, to kuma da yake dai a jikin majigin duk za ka ga birane da kasashen da ake ta wucewa haka kuma za ka iya rika leka wa ta tagar jirgin kana ganin garuruwan idan ma ba hazo ake ba har zaka iya sa’ar ganin dazuzzuka, rairayin hamada da tsaunuka, tituna, gine-gine da sauransu dai na birnin.
Mun fara da wuce Birnin Tangier na bakin tekun meditteranian na Maghrib, birnin karshe a nahiyar Afirka. Ana wa Tangier lakabi da Birnin masoya saboda camfa birnin da akayi cewar in dai an kulla alkawarin aure a birnin to kuwa lallai mutu ka raba, maana duk auren da aka kulla alkawarinsa a Tangier to kuwa auren baya mutuwa, wannan nema yasa daga koina a duniya masoya samari da yammata ke cidadawa birnin in sun daidaita kansu domin wanzar da alkawarin, za ka ga yawanci ma samarin kan kyale zoben alkawari ‘Engagement ring’ har sai an je Tangier ne zai sanya a yatsan budurwarsa
Ta tagar jirgi ina iya ganin Birnin Tangier da ragowar yamma a bakin tekun maliya. Tangier birni ne da yake tsit ga tsabta ga furanni ko ina sannan kuma iskar tekun meditteranian din kan kwaso rairayin soyayya ‘Lobe sands’ cakude da dusar kankara tana bade fuskokin masoyan a bakin tekun.
Mun tsallaka gabashin Turai ta takeun Meditteranian mun fara isa birnin Mallorca na yankin Andulus muka wuce Albacete har muka je helkwatar baskue Balencia har wala yau na ga mashigar ruwannan ta Bilbao inda aka je karshen yakin nan na crusade wanda kiristocin Rum suka yanka miliyoyin musulmi (An ce tun daga Cordoba zuwa Sebille zuwa Bilbaon gawarwakin musulmi ne na lokacin iyakar ganinka) ina iya ganin mashigar Bilbao da aka ce saboda tsananin shekar da jinin musulmi da aka yi a wajen, Balarabiyar Tangier da Rabat idan ta je diban ruwa a bahar maliya tana iya gane jirkicewar ruwan zuwa kalar ja ja ja na jinin musulmi.
Mun wuce Kauyen Barcelonan Kataluniya shimfide kaman tabarma a bakin ruwa, har munyi tafiya mai nisa muna hango hasken fitilun Garin.
Mun fita daga Spaniya muka ratsa Switzerland ta birnin Basel, kafin mu wuce ta saman Budapest din Kasar Hungary.
Mun ratsewa Kieb din Ukrainiya ta kudu muka bullowa Birnin Moscow a tsananin sanyi wajajan karfe 3 na dare, lokacin da mu ka zo Moscow Airports da ace rufe min ido aka yi kawai na tsinci kaina a Moscow zan iya dauka birnin Dubai aka kaini, don tsarin cikin Tashar Jirgin ‘escalators, lobby passages, lifters da rails’ duk irinsu daya da Dubai din, kai hatta ma wurin wucewar fasinjoji, wurin tsayuwar ‘yan tasi da ma titin da ya fita daga tashar jirgin zuwa cikin gari duk iri daya suke.
Da yake mun zo latti haka mun tarar jiragen saman da za su kaimu Birnin Leningrad, St Petersburg (inda masaukin Super Eagles na Nijeriya yake) daga Moscow duk dakunan sun cika saboda masu cidadawa Birnin, ala tilas muka hakura muka tafi tashar jirgin kasa ta nan Moscow inda muka yi tafiyar kusan awa goma zuwa Leningrad din
Abokan tafiyata yawanci ba su ji dadin tafiya a jirgin kasar nan ba saboda gajiyar da muka debo tun daga Legas, amma dai abin ka da mai son yawon bude ido ‘Edplorer’ ni dadi ne ya kume ni na samu dace da ganin ‘Russian country side’.
Wani abu da ya kara bani al’ajabi da saukar mu a Rasha shine yadda a take na fahimci duk da tsananin sanyi da suke ciki gaba dayan tsawon darensu Awa ukku ne rak, maana zakaga Karfe 11:00 na dare a Agogo amma kuma rana bata fadi ba, sai sha dayan dare ake maghriba, kenan in abin mu yi gwari gwari ne su suna Azimtar awa 21 ne a rana maimakon mu da muke azumtar awa 13 zuwa 14, kaman ace ne lokacinmu na buda baki zai koma 12 na dare, ka ga kafin a gama sallar maghriba, isha’i da tarawih tuni alfijir ya keto babu maganar Sahur ma sam.
Insha Allahu a kashi na 2 da na 3 na rubutuna zan yi magana akan zamantakewar mutanen Rasha, dangantakarsu da baki, tarihi da siyasarsu da kuma ziyarce ziyarce da na yi wurarensu na Tarihi
Hassan Garo, ya rubuto ne daga Kano

Exit mobile version