Tagomashin Da Babban Bankin Nijeriya Ya Samar A Fannin Ilimin Zamani

Rubutun Ajami

Daga Kelvin Gilbert

Babu wata tantama Babban Bankin Nijeriya CBN a karkashin shugabancin Gwamnan Bankin Mista Godwin Emefiele, ya taka muhimmmiyar rawa, a bangaren bunkasa ilimin zamani, inda hakan ya nuna a zahiri, ba a taba samun hakan ba a tarihin Bankin.

Har ila yau, Bankin ya kuma samar da dauki ta hanyar samar da shirye-shirye iri -iri wajen habaka tattalin arzikin Nijeriya wanda suka hada da kirkro da bayar da rance da kudi da suka kai Naira biliyan 100 da samar da daukin Naira biliyan 100 ga fannin kiwon lafiya.

Sauran daukin sun hada da, fannin kirkirar fasaha CIFI, inda fannin ya samu Naira Tiriliyan daya da kuma samar da dauki a fannin shirin aikin noma na Gwamnatin Tarayya wato Anchor Borrowers da ke a karkashin kulawar CBN.

Wannan ya nuna a zahiri cewa, Bankin ba wai kawai ya na sa ido ne kan hada-hadar kudade a kasar nan ba, inda hakan ya nuna cewa, Bankin ya na kuma ci gaba da yin namijin kokari wajen tsamo fannin na ilimin a kasar, musamman ganin cewa, fannin shi ne kan gaba wajen habaka samar da ci gaba.

Bugu da kari, an ruwaito Babban Bankin Duniya ya yi nuni da cewa, bunkasa rayuwar al’umma shi ne ginshiki ga ko wacce kasa, musamman domin a cimma burin rage radadin talauci tare da samar da ilimin zamani don a kara habaka rayuwar ‘yan kasa.

Tabbas, zuba jari a fannin ilimin zamani na daya daga cikin ginshiki bunkasa rayuwar al’umma tare da yin amfani da ilimin wajen bunkasa tattalin arziki.

Shekaru da dama da suka shude an yi watsi da fannin ilimin zamani a kasar wanda ba a taba gani ba a kasar, inda a wani nazarin bayanai na CBN ya nuna cewa, fannin ilimin zamani a kasar ya samu koma baya a shekaru goma da suka gabata.

Idan aka buga misali da takardar kididdigar bayanai na Bankin CBN, daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2020, ‘yan Nijeriya sun kashe wuri na gugar wuri, har Dala biliyan 28.65 wajen zuwa yin karatu a ketare.

Hakazalika, yawan dalalolin da k kashe wa wajen zuwa neman ilimin zamani a kasar waje, hakan ya janyo asusun ahiya na kasshen waje, a yanzu sun yi kasa zuwa dala biliyan 33.39, inda kuma hakan, ya shafe kudaden musaya na waje.

Har ila yau, bayanai na kididdigar bayanai da aka samo daga gun Webometrics, ya dora jami’ar Ibadan kan adadin 1,196, inda kuma jami’ar Cobenant, suka kai yawan of 1,314.

Ma’ana, babu wata jami’ar a kasar nan ba da suka kai mataki na kashi 10 a cikin dari a duniya haka kuma ka’idar UNESCO ta zuba kudade a fannin ilimin zamani shi ne, zuba kashi 26 a cikin dari na kasafin kudi da kuma kashi 6 na tattalin arzikin kasa, inda kuma kididdigar bayanai da aka samo daga gun UNESCO, ke nuna cewa, kimanin ‘yan Nijeriya su 76,338 suka je karo ilimin zamani a shekarar 2018, inda wannnan ke nuna cewa, wannan adadin ya nuna shi ne, mafi yawa da aka taba samu nahiyar Afirka.

Sai dai, kasafin kudin da ake kebe wa fannin ilimin zamani a kasar nan, bai wuce yawan kimanin kashi 5.3 a cikin dari ba, inda kuma idan aka yi dubi kan yawan adadin ‘yan kasar, wannan adadin ya yi kadan matuka, ganin cewa, fannin na ilimin a zamanin, ya kai yawan kashi 1.94 a cikin dari na tattalin arzikin kasar wanda a kwatar shekara ta daya, ta 2021 da kuma a shekarar 2020 ya kai kashi 1.86 a cikin dari.

Bugu da kari, koma bayan da aka samu a kasar a fannin habaka ilimin zamani ya janyo an kasa cimma kai wa mataki irin na duniya, inda hakan ya janyo ‘yan kasar da dama fita zuwa kasashen duniya domin neman ilimin zamani, haka fannin ilimin zamani a a kasar nan, na bukatar a zuba kudade da yawa a fannin.

A bisa kokarin na CBN a karkashin shugabancin gwamnan Bankin ba CBN don bunkasa fannin aikin noma a kasar Emefiele ya samar da daukin a fannin habaka ilimin zamani a kasa, musamman don jami’oin su kai matakin manyan jami’oi 100 a duniya.

Wasu daga cikin aikin sun hada da, kebe Naira biliyan 63 da CBN ya yi domin gina ingantattun Cibiyoyin a jami’oin tara mallakar Gwamnatin Tarayya a kasar nan, musamman domin a kara habaka kwasa-kwasan daliban jami’oin ta hanyar shirin koyon sana’oin hannu na (TIES).

Emefiele, a jawabunsa a taron kungiyar shuwagabannin jami’oi ta kasa AbCNU karo na 35 ya sanar da cewa, hadakar za ta kasance tamkar wayar da kan daliban jami’oin da aka yaye ne wajen rage dogaro da Newman aikin Gwamnatin, yadda za su rungumi sana’oi kanana da matsakaita MSME, inda MSME zai taimaka wajen cine gibin da da ake da shi a tsakanin matasa da kuma kara habaka tattalin arziki.

Emefele ya kara da cewa, CBN ya kirkiro da shirin na bunkasa jami’oin ne na koyon sana’oin hannu wato (TIES) tare da bayar da horo da kuma samar da kudaden ga wadanda aka yaye.

Ya bayyana cewa, shirin an tsara shi ne kan yadda daliban jami’oin da aka yaye su za su koyi sana’oi da kuma samun kudade a cikin sauki don inganta fasahar da suka koya.

Bugu da kari, jawabinsa a kwanan baya a yayin da yake kaddamar da wasu ingantattun Cibiyoyi a jami’ar Amadu Bello ABU da ke a garin Zariya Emefiele ya sanar da cewa, aikin na daya daga cikin daukin da CBN ke samar wa domin kara bunksa fannin ilimin zamani a kasar.

Ya ci gaba da cewa, Cibiyoyin anbtsara gudanar da su kashi -kashi, inda a kashi na farko, suka kunshi jami’ar Nsukka, jami’ar Ibadan da kuma jami’ar ABU Zariya wadanda tuni, an kammala su kuma jami’oin za su iya fara yin amfani da su.

Gwamnan ya kara da cewa, sauran sun hada da, jami’oin Legas, Fatakwal, Jos, Bayero da ke Kano da kuma jami’ar Maiduguri.

Ya bayyna cewa, Cibiyoyin a tanadi dakin taro mai daukar yawan mutane da suka kai 500, na’urar sadarwa ta zamani, dakin karatu na fasahar zamani, inda ya kara da cewa, idan Cibiyoyin suka fara gudanar da aiki, shirye – shirye kamar su, kula da asusun Kasuwanci da hada-hadar kudade a kasuwar duniya FAGFMR da kuma bin ka’idar mahukunta, za su taimaka wa Cibiyoyin.

Hakika babu wata tantama, kan irin wannan kwarran matakan da Bankin ba CBN a fannin na inganta ilimin zamani a kasar, musamman don a taimaka wa daliban jami’oin da aka yaye su.

Gilvert, masani ne na tattalin arzikin kasa da ke da zama a yankin Garki a babban birnin tarayyar Abuja.

 

 

 

 

Exit mobile version