Musa Muhammad" />

Taimaka Wa Al’umma Ce Babbar Manufar Mu A ‘Bintaliya Foundation’ –Hajiya Binta

Wannan wata tattaunawa ce LEADERSHIP A YAU ta yi wata mata wacce ta yi fice wajen tallafa wa a al’umma, sannan kuma da irin kokarinta wajen ilimantar da jama’a, musamman a harkar ilimin kwamfuta na zamani, wanda ya kai ma ta kwashe shekaru da dama tana gudanar da makarantar koyon ilimin Kwamfuta a Unguwar Sanuni da ke Kaduna, sannan kuma a haka ta kafa cibiya, wacce daga wannan cibiyar ce ta ke tallafa al’umma ta hanyar da ba su guraben ilimin kwamfuta da kuma sauran bukatu na yau da kullum, ta cibiyar mai suna ‘BINTALIYA FIST FOUNDATION.’

Wannan baiwar Allah, Hajiya Binta Hamidu Haruna ta bayyana wa wakilinmu cewa ita tana ganin abu ne mai muhimmnanci a taimaka wa wadanda ba su da shi, musamman a wannan lokaci da jama’a ke kulle a gidajensu, bisa umurnin Hukumomi don kauce wa yaduwar wannan muguwar cuta ta zamani ta COVID-19.

Ta ce, wannan tunani ne ma ya sa ta ware lokaci da dan abin da Allah ya hore mata na kudi, ta sayi kayan abinci don raba wa al’umma, inda ta ke bi Unguwa-Unguwa, tare da masu taimaka mata suna rabon abin da ya sawwaka ga wadanda Allah ya ciyar, wanda a cikin wannan tattaunawar, Hajiya Binta ta ce ta ware miliyoyin Naira don wannan abu.

Haka kuma Hajiyar ta bayyana mana irin gudumawar da ta ke bayarwa wajen ilimantar da jama’a, maza da mata, manya da matasa ilimin Kwamfuta, inda ta ce tana so ne jama’ar wannan yanki nata su kasance masana a wannan harka, musamman ’yan kasuwa, don su kasance suna tafiya da zamani a harkar su ta kasuwanci.

Akwai muhimman bayanai a wannan tattaunawar da suka yi da Daraktan mu, Musa Muhammad a gidanta da ke Unguwar Sanusi, Kaduna. A sha karatu lafiya.

Da farko za mu so mu ji takaitaccen tarihin ki?

Ni sunana Binta Hamida Haruna, Mahaifi na shi ne Marigayi Alhaji Hamida Haruna. Na girma ne a Unguwar Sunusi da ke garin Kaduna a nan Nigeria, kuma ni nake da makaranta da ake kira da ‘Bintalya Computer Institute’. Na fara ‘Bintaliya Computer institute’ ne tun shekara ta 1998/1999. Yanzu mun yi fiye da shekara ashirin da kafa makarantar.

Ana cikin yin haka, a cikin shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai muka bude wata makarantar don koyar ilimin boko, wato‘Bintaliya International Nursery and primary school,’ sannan daga nan muka yi ta ci gaba har ta kai mu da bude rassa a karkashin Bintaliyan, har muka canja mata suna ta koma ‘Bintaliya group of companies.’

Bayan wannan kuma muka bude cibiya (Foundation), wanda a cikinta mu ke taimaka wa jama’a, musamman marasa karfi, a nan ne duk wani taimako muka ci gaba da yinsa. Saboda mun dade muna yin taimako, tun daga farawar makarantar ‘Computer’ muke bayar da horo ga daliban a fannin kwamfuta, muna koyar da ‘Computer appreciations’ da sauransu

A cikin abubuwan da mu ke koyarwa, akwai abin da za ka koya wanda ya shafi gabatarwar a ilimin Kwamfuta har zuwa karshe, sannan ka cancanci takardar shaidar karatun ka (Certificate), kuma ka karbi takardar Diploma, sannan mu yayeka daga makarantar.

A makarantar ‘Bintaliya International School’ muna koyar wa yara, ta yadda yanzu har an fara yin WAEC, yanzu ma wadansu daga cikin daliban mu suna Jami’a, wadansun su ma sun gama, Alhamdulillah!

Kwana kin baya mun ji an je bikin yaye daliban wannan makarata a babbar Kasuwar Kaduna, wanda a ciki aka nuna cewa ’yan kasuwar ne kawai aka ware aka yi wa wannan horarwar. Ya abin ya kasance?

Eh toh! Ita dai wannan ‘Computer Institute’, kamar yadda na fada maka ta dade tana bayar da ilimin Kwafuta kyauta, wato akwai wadanda ake baa bin nan da ake ce ma ‘Scholarship’, a kodayaushe mukan bayar da ‘Scholarship’ ga mutum 200 a Kaduna, sai abin ya yi ta karuwa har sai da muka yanke shawarar ko’ina za mu koyar da ilimin Kwamfuta ga mutum 500 duk shekara guda a Nigeria, mun fi tsawon sheraka ashirin muna yin hakan.

Daga bayan nan ne sai muka ga cewa karatu sai kara budewa yake ta yi, kimiya da fasaha suna ta kara ci gaba, shi ne wanda ya ba mu damar ganin cewa ya kamata mu koyar da ‘yankasuwa kasuwancin zamani, wanda yanzu shi yake tafiya a duniyar kasuwanci, wanda ake ce masa (Digital Marketing), sannan muka fara abin da ake ce ma (Social Skill usage), wanda ake amfani da su a Whatsapp, Facebook, Twitter ko Instagram domin yin kasuwanci.

Wannan shi ne abin da muka koya wa ‘yan kasuwar, domin su karu da ilimin kwamfuta don harkar kasuwancinsu, saboda su ci gaba da harkar kasuwancin su ta wannan zamanin, kuma su gane halin da duniya ta ke ciki na harkar kasuwanci a yanzu, tun da gaskiya an riga an bar su a baya sosai. Wannan ne ya sa muka koyar da mutum 500, saboda yawancin su ba su da halin su koya, ma’ana halin biyan kudin karatun.

Saboda haka sai muka ce bari mu taimaka da namu taimakon, domin mu koyar da su, mu koya masu ilimin kwmfuta na kasuwanci saboda su ma in sun koya za su ci gaba da yaduwa a cikin al’umma wajen wayar wa da wadansu da ba su da wannan ilimin kai, su ma su koya, don su ma zai zamanto mai amfani gare su, domin za su samu damar yin kasuwanci ta hanyar zamani yadda su ma za su samu abincin kansu.

In na fahimce ki, kamar Makarantar Kwamfutar ta kasu kashi biyu ne, akwai bangaren da ake koyarwa kyauta da kuma bangaren da ake karbar kudi?

Eh, dama ai asali makarantar koyon kwamfuta ce, biya za ka yi ka zo ka yi karatu. To amma, kamar yadda na fada maka a baya, ina kuma da cibiya ‘Foundation’, to ita ce za ta tallafa wa wadanda ba su da shi, sai su nema (Apply), in sun samu sai mu ba su ilimin nan kyauta.

Amma kamar su ’yan kasuwa, ai an ce kyauta ake koya masu?

Eh mana, kamar wannan wanda muka yi na babbar kasuwar Kaduna, ai ita Cibiyar Bintaliyar ce ta ware ta kudi dauki nauyin karatun, domin ta koyar da su. Kamar dai yadda na fada a baya ne, Bintalya tana da Bintalya First foundation, ita wannan First Foundation din ita ce ta tallafa wa wannan mutum 500 din su koya, amma ita ‘Computer Institute’ za ka biya ne ka yi karatu.

Duk da kina wannan aiki na taimakon jama’a, kina yi ne don Allah, inda wasu za su so su yaba maki ta fannoni da dama, kamar dai yadda Hakimin Doka, da ke cikin garin Kaduna ya baki Sarauta ta Garkuwa. Ya kika ji?

Toh, ni babu abin da zan ce sai godiya. Wadannan mutane kullum suna nuna kaunar su ga Bintaliya a kodayaushe, babu abin da za mu ce sai dai mu ce mun gode, Allah ya saka da alhairi. Kuma na san akwai wasu na nan da dama da suke son su kawo taimakon su, kuma muna nan muna jiran su, Allah ya ba su iko.

Ganin halin da ake ciki na yanayi na duniya yanzu, sai muka tarar da ma Shugaban kasa a wani jawabins, ya nemi masu hali da su taika ma wadanda ba su da shi da abin da ya sawwaka. Sai ga shi yanzu na zo na riski kuna bayar da wannan tallafi ta hannun wannan Cibiya ta Bintaliya foundation. Shin ya kuka tsara bayar da wannan gudumuwar da kuke badawa?

Toh, a yanzu babu wanda zai ce ya ki taimako, in dai har zai samu, samuwarsa shike da wiya a yanzu, muna fatan wadannan da suke da hali za su taimaka, kuma ita gwamnati da ta ke taimaka wa Kungiyoyi, za ta dube mu mu ma ta taimaka mana don mu ma mu taimaka wa jama’a, don mun fi kusa da jama’a, kuma mun saba muna yi, kuma saboda daman ba ta tada yi mana komai ba. Duk abin da aka ba mu, za mu bayar da shi ne ga mabukata.

Ya kuke raba naku irin naku taimakon?

Daga abin da muka koyar da al’umma muka samu, domin ana cewa, abin alhairi ba ya kadan. Muna samun kudin shiga ne daga ‘Foundation’ din nan, kuma daga ciki ne muke cirewa mu taimaka wa al’umma.

Ya kuke bada gudunmuwar, shin jama’a kuke tarawa a kofar gida su bi layi, kowa a ba shi nasa, kokuwa ya kuke?

A’a, sanarwa muke yi, za mu kai sanarwa a masallatai, mukan kuma sanar a kafafen yada labarai, domin wasu daga cikin kafafen yada labarai din da kansu ma suke mana taimako, kuma ba wai kudinmu ya sa suke mana ba, suna taimakonmu ne soboda sun ji labarin taimakon da muke yi wa al’umma, kuma yana masu dadi su ma kansu.

Dalilin da ya sa ke nan su ma suka zo suke taya mu sanar da al’umma cewa ga shi nan za mu yi wannan abin, wanda yake da ra’ayi, ya zo ya karba. Su ma kuma kansu babu abin da za mu ce masu sai dai Allah ya saka da alheri, domin duk taimakon juna ne, kuma mu duk inda taimako ya zo, muna karbar shi hannu bibiyu, mu yi fatan Allah ya sa alhairi.

Yanzu a kididdige za ki iya fada mana mutane nawa ne suka ci moriyar wannan Cibiya taku?

Gaskiya ni yanzu ba zan iya fada maka ba, domin na fada maka cewa mun kwashe shekaru muna wanan aiki, soboda sun fi mutum miliyan 20, tun da abin da ya fi kusan shekaru 30 ana yi, tun ina karama, yanzu har na girma ina yin wannan abu, ai ba za ka ce ga adadin mutanen da ka amfanar ba.

Yanzu in mutum ya karanta wannan kokari naki kuma shi mubukaci ne, ya za a yi ya zo ya amfana?

Zuwa suke su yi su yi ta damunmu, shi ya sa bukatar kullum sai karuwa ta ke yi, kuma saboda karuwar muna neman karin kwamfutoci da sauran hanyoyin daukar nauyin jama’a.

Yanzu wace bukata ki ke da ita ga gwamnati?

To ni dai gwamnati daman ban tada sa rai gareta ba, don ba ta taba taimaka wannan cibiya taw aba, domin na fada maka cewa na fi karfin shekara da shekaru ina wanna aiki, ku ma na san tana ji na, ta kuma san da ni, amma ba ta taba taimaka min ba.

Mahaifina, Allah ya ji kansa, yana cewa, kada ka yi tunanin wani ya zo ya taimaka maka, duk abin da za ka yi saboda Allah, ka ci gaba da yi, Allah yana tare da kai. Abin da ya fada min shi ne yake cikin kwakwalwata har yanzu, kuma shi ne nake ci gaba da yi, ba na tunanin wani ya yi min. A kullun ina tunanin Allah ne zai yi min.

A daidai gwargwadon abin da Allah ya ba ni da kuma masoya da suke tare da mu, su ma suna bada tallafin su, da kuma ‘yan uwa wadanda suke kasuwanci, su ma suna kawo taimakonsu, Alhamdulillah! Da shi al’umma take amfana, babu abin da za mu ce sai dai godiya.

Amma duk da haka, idan gwamnati, tun daga ta tarayya, jiha da Kananan Hukumomi suka ga za su iya tallafa mana domin mu isar ma jama’a, to muna maraba da shi. Domin ai wannan aikin da muke yi, tamkar muna rage ma gwamnatin wani nauyi ne. Don haka in suka kawo mana muna mabara da shi. Kuma muna tabbatar masu da cewa za mu bayar da shi yadda ya dace.

Akwai mutanen da suka fi ki a karfin arziki nesa ba kusa ba, amma ba su samu damar yin wannan taimako da ki ke yi ba. Me ke ranki?

Ai komai sai Allah ya ba mutum damar yi, idan Allah bai ba mutum sa’a ba, babu yadda zai yi, ni ma bawai kudin gare ni ba, Allah ne ya ba ni ikon yi. Saboda haka babu abin da zan ce ga Allah sai godiya da wannan ikon da ya ba ni.

Exit mobile version