Zubairu M Lawal" />

Taimakon  Juna Kan Janyo Zaman Lafiya Tsakanin Al’umma – Malama Hauwa

Da ta ke jawabi wajen taron kungiyoyin matan kabilu da su ka taru domin samun fahimtar juna da hanyoyin samar da zaman lafiya tsakanin alumman Nijeriya, Malama Hauwa Sode’inde, ta ce; taimaka wa juna shi ne ginshikin samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ta ce; idan ku na tare da kishiya a gida idan har ki na taimaka ma ta, to za ta kasance mai kaunar ki kuma idan ku na taimaka wa junanku, babu wanda zai ji kanku bare a ga ku na tashin hankali.

Ta ce; abubuwan da yanzu ya ke faruwa a kasarmu Nijeriya ba komai ya ke kawo shi ba face karancin tausayi. Za ka ga mutane sun shiga wani hali, amma masu arziki ko gwamnati ba su taimakawa.

Idan ba ku taimaka wa jama’a, ta yaya za ku yi magana su saurare ku tunda sun san ba ku taimaka masu da komai?

Saboda haka idan mu na bukatar samun zaman lafiya da hadin kan juna dole sai mun taimaki junan mu, kada mu rika nuna bambamci tsakanin mu. kar mu ce wanan kabilar mu ne , wanan ba kabilar mu ba.

Kuma kada mu ce wanan addini mu ne zamu taimake ta wanan ba addini mu ba ba za mu taimake ta ba.

Tace ; addini ya haranta wanan idan kaga mutum yana bukatar taimako ku taimake shi. Taron da sashin yada labarai na Majalisar Dinkin Duniya ta shirya ya samu halartan mata daga sashi na kabilu dabam dabam a jihar Lagos.

Taro ya tattauna hanyoyin da mata za su bi, domin samar da zaman lafiya a kasa da kuma hanyoyin kasuwanci na taimakon kai da kai.

Malama Hauwa itace Shugaban gidauniyar HAUK wanda ta ke fafutukar gani mata sun mike tsaye suma ana damawa dasu a harkokin kasuwanci dama siyasa a Nijeriya.

Tace dole mata su hada kai su taimakawa junansu damuwar ya mace ta ya mace ce. Ko ina kikaga mace ko wani irin yarece Yar uwan ki ce saboda jinsi daya ne ke da ita.

Mu hada kai saboda hadin kanmu zai samar mana da cigaba ta ko wani sashi.

Tace ; mu cigaba da tallata manufofin mu na hadin kan mata duk inda mu ke mu janyo yaran mu mata mu koyar dasu Sana’ar hannu saboda sune  iyaye nan gaba.

Mu koyar da su kaunar juna saboda su tausayawa na bayan su. Su bai wa yara tarbiya ingantaciya.

Exit mobile version