Taimakon Kasar Sin Na Ingiza Ci Gaba A Nahiyar Afrika
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taimakon Kasar Sin Na Ingiza Ci Gaba A Nahiyar Afrika

byCGTN Hausa
1 year ago
Sin

Kafofin yada labarai a kasar Habasha sun ruwaito a jiya cewa, yankin masana’antu na Kombolcha (KIP) da kasar Sin ta gina a kasar, ya samar da kimanin dala miliyan 28 na kudin shiga daga fiton kayayyaki zuwa ketare, cikin watannin 9 na farkon shekarar kudi ta kasar ta (2023/2024) da ta fara daga ranar 8 ga watan Yulin 2023.

Wannan ci gaba abun burgewa ne matuka, ganin yadda dukkan abubuwan da aka fitar, an samar da su ne a harabar yankin na KIP na kasar Habasha. Samar da yankin da kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina, wani bangare ne na burin Habasha na zama cibiyar samar da kayayyaki a nahiyar Afrika, kuma da alama ta dauki hanyar cimma wannan buri nata, da taimakon kasar Sin.

  • Sin Ba Ta Da Masaniya Game Da Dalilin Philippines Na Kin Amincewa Da Daidaiton Da Aka Cimma Kan Batun Sashen Tudun Ruwa Na Ren’aijiao
  • Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN: Sama Da 80% Sun Soki Yadda Japan Ta Gurbata Tarihi Cikin Sabbin Littattafan Da Ta Buga

Yayin da ake fama da hauhawar farashin kayayyaki da ma raguwar darajar kudaden kasashe musamman na Afrika, masana na cewa samar da kayayyaki a cikin gida, wata ingantacciyar dabara ce ta shawo kan matsaloli da dama. Tabbas Habasha ta samarwa kanta mafita, godiya ga kasar Sin. Zan bada misali da wasu batutuwa 3.

Na farko, samar da kayayyaki a cikin gida. Yadda wannan yanki na KIP ke samar da kayayyaki a cikin gida, tabbas zai ragewa al’ummar kasar radadin hauhawar farashin kayayyaki. Ba su kadai ba ma, har da kasashe makwabta da nahiyar baki daya. Wannan lamari zai kara inganta kyautata rayuwar jama’a.

Na biyu, fiton kayayyaki. Wannan zai bunkasa karfin kasar na shiga kasuwannin duniya da ma kara haskata a dandalin kasa da kasa. Haka kuma zai kai ga bunkasa lamarin da zai bata karin damarmakin samun karin ci gaba ta fuskar kasuwanci da ababen more rayuwa tare da janyo jarin waje.

Na uku, samar da guraben ayyukan yi. Cikin watannin 9, wannan yankin masana’atu da Sin ta gina, ya samar da karin guraben ayyukan yi sama da 850 ga mazauna wurin. Daya daga cikin manyan abubuwan dake haifar da rashin ci gaba kasa da ma rikice-rikice shi ne yawaitar masu zaman kashe wando, amma da zarar aka samu ayyukan yi, to ya kan toshe kafofi da dama masu tarnaki ga ci gaban tattalin arziki da zaman takewar al’umma.

A ganina, dangatakar Sin da kasar Habasha, ba samar da hanyar bunkasa tattalin arziki kadai ta yi ba, har ma da samarwa kasar irin dabarar kasar Sin ta samun ci gaba. Mun sani cewa, kasar Sin ta bullo da wata sabuwar hanyar ci gaba da ba a taba gani ba a duniya, inda take juya yawan al’umma da albarkatun da take da su a cikin gida zuwa hanyoyin bunaksa ci gabanta ba tare da mulkin mallaka ba. Hakika hulda da kasar Sin alheri ce, kuma na yi imanin sauran kasashen Afrika za su iya bin sawun Habasha don tabbatar da ci gabansu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Badakalar Fiye Da Biliyan 8: EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika 

Badakalar Fiye Da Biliyan 8: EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika 

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version