Bankin TAJBank wanda yake gudanar da kasuwancinsa ta tare da kudin ruwa ba, ya jaddada cewa yana kokarin inganta ilimi a Nijeriaya. Wannan ya zo a dai-dai lokacin da aka kaddamar da sabon makarantar Saint John Paul School da ke cikin Jihar Akwa Ibom.
Ministan Niger Delta, Sanata Godswill Akpabio wanda shi ne babban bako a wajen kaddamar da makarantar, ya yaba wa bankin bisa kadirinta na tallafa wa bangaren ilimi wanda ya bayar da kudade domin samar da ababen more rayuwa a wannan makaranta. Ya kara da cewa, yana kira da sauran bankuna da su yi koyi da bankin wajen tallafa wa ilimi a cikin kasar nan. Akpabio ya bukaci bankin ta yi kokarin bude rashe a a Uyo a duk lokacin da suka sami lasisin bude rassa a ko’iya a fadin duniya.
Wakilin bankin a wajen taron, Mista Nasir .T. Usman ya bayyana cewa, shugabannin Saint John Paul School Akwa Ibom sun yi kokarin cike gibin da ake samu a bangaren ilimi a Nijeriya, domin haka sun cancanji a samar musu da abubuwan da suke bukata nan take. Ya bayyana cewa, sakamakon irin shawarwarin da makarantar ta samu a cikin watan tara, sun samu nasarar bai wa dalibai ingantaccen ilimi tun lokacin kafuwarta. Ya kara da cewa, a cikin shakara daya da bankin TAJBank ya samu nasarar cimma nasarori masu tarain yawa.
A cikin ‘yan kwananin nan, bankin ya samu lambar yabo daga kamfanin gudanarwa na jaridar Leadership bisa irin namijin kokari da bankin yake yi a fadin kasar nan a bangaren harkokin kudade musamman ma a kan mutane marasa karfi.
Bankin ya fara gudanar da ayyukansa ne a ranar 4 ga watan Disambar shekarar 2019, wanda a wata da ta gabata ce bankin ya cike shekara daya da kafuwa. A cikin kayayyakin da bankin ya samar a cikin makarantar sun hada da kayayyakin kimiyya da fasaha da kayayyakin rubutu da takardun karatu wanda aka bai wa wannan makaranta domin kara inganta ilimi a cikin jihar.