Daga Mahdi M. Muhammad,
A ranar 15 ga Disamba, 2020 ne fitaccen bakin nan na TAJBank, bankin da ba ya huldar bayar da bashi da ruwa, ya yi bikin cikarsa shekara daya da kafuwa, inda aka gudanar da wani kasaitaccen biki a otel din Wells Carlton da ke Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya.
Wadanda su ka halarci taron, sun kasance mambobin Hukumar gudanarwar bankin ne, da kuma shugabannin gudanarwa, gami da sauran ma’aikata. Bikin ya kuma kasance wata dama, inda a ka karrama wasu ma’aikatan farko da sauran fitattun ma’aikata.
Shugaban Hukumar gudanarwar, kuma wanda ya kafa bankin na TAJBank, Alhaji Hamid Joda, ya yaba da kwazo, hankali da jajircewar ma’aikatan, musamman wajen cimma nasarori da dama cikin dan kankanin lokaci na shekarar.
Daga nan ya sake nanata tsarin ‘Mantra’ na Banki na 10/10, kuma ya bukaci ma’aikatan su ci gaba da ba da irin wannan himma a shirye-shiryenta na shekara mai zuwa na aiki don tabbatar da cewa bankin ya ci gaba da ba da ayyuka na musamman ga abokan ciniki, wadanda su ka zama sanannu sosai.
Cikin nasa jawabin, daya daga cikin kashin baya, kuma wadanda suka kafa bakin, Malam Sherif Idi, ya bayyana cewa, ayyukan da aka yi masu amfani a cikin watanni taran na, abubuwa masu matukar birgewa, don haka ya bukaci ma’aikatan da su rike irin wadannan kyawawan ayyuka a lokacin da bankin zai shiga wasu shekaru biyu masu zuwa. Ya kuma yaba wa masu hannun jarin saboda hakurin da suka nuna da kuma amincewa da alamar, kuma ya nuna farin cikin cewa Bankin zai biya haraji a shekararsa ta farko da fara aiki.
A cikin shekara guda da gudanar da ayyukansa, Bankin ya cimma nasarori da dama, wadanda suka hada da kaddamar da TAJDpress (Kai kananan bankuna cikin kauyaku da lunguna) a fadin jihohin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma. TAJMall, wata babbar cibiyar kasuwanci ta 1 a Nijeriya don harkar kasuwanci ta yanar gizo mai muhimmanci, tare da mai da hankali kan samar da kayan da ayyuka, don saduwa da bukatun abokan hulda a duk fadin kasar na da ma duniya baki daya.
Bankin na TAJbank ya kuma ya samu lambar yabo na bankin Islama da ya tsayu da kansa wajen ci gaban kasa, wato ‘GIFA Awards 2020’.