Taka Dokar Korona: Kotun Tafi-da-gidanka Ta Rufe Kasuwar Wuse Dake Abuja

Kwamitin yaki da yaduwar cutar Korona ta kai ziyarar ba-zata kasuwar Wuse jiya Litinin inda ta ga abubuwan mamaki. Kwamitin ya ce ‘yan kasuwar basu amfani da takunkumin fuska, gwada dumin jiki da kuma wanke hannuwa.

Kwamitin ya damke wasu mutane a cikin kasuwar a motocin haya wadanda suka ki saka takunkumin fuska. An gurfanar da sama da mutum 100.

Idayat Akanni, alkaliyar kotun ta yanke wa mutanen hukuncin biyan dubu bibbiyu ko kuma su yi wa yankinsu aikin makonni bibbiyu. Alkaliyar ta ce an bai wa masu laifin wannan hukuncin ne saboda wannan ne karo na farko da aka taba kama su da wannan laifin.

Exit mobile version