Takaddama Kan Bizne Mahaifinsu Ta Sa Ya Kashe Wansa

Wani mutum da ake kira Ejiofor Oyiogu ya daba ma wai dan’uwan shi  Ekene dan shekara 47 wuka, wadda tayi sanadiyar mutuwar shi, a Karamar Hukumar Dunukofia ta jihar Anambra,

Su dai wadannan mutnen’ya’yan wani mashahurin dan siyasa ne wanda bai dade da mutuwa ba.

Ita dai wannan ta kaddamar da tayi sanadiyar mutuwar daya daga cikin ‘ya’yan abin ya faru ta kai ga yi tsamari ne, saboda al’amarin daya shafi kudaden da zasu kashe lokacin rufe mahaifin nasu .

Ya  ci gaba da cewar shi ‘’Ekene yana ta kara dorawa kanen shi  Ejiofor nauyin binne mahaifin nasu

Ya ce shi ,’’ Ejiofor,  bama kamar maganar rufe mahaifin nasu, wadda ta kamata ayi kwana daya kafin wannan al’amari na kashe dan’uwanshi ke damun shi ba, amma maganar nauyin abubuwa masu yawa da aka dora ma shi.

Ita maganar dai ‘’Ta kai kaimi ranar Asabar lokacin da Ekene ya daba wa kanenshi wuka, wanda ya kama wukar, ya yanke shi a wurare daban daban da suka hada da wuya, hannu cibiya, da kuma kai. Shi dai yayan na shi yam utu lokacin da ake kan hanyar kan hanya.

Jami’ar hulda da jama’a Nkeiruka Nwode ta bayyana cewar shi anda ya aikatab laifin ankama shi.

Ta kara da cewar an shaida ma ‘yansanda  aukuwar al’amarin wanda wani daga cikin iyalan gidan, ya yi.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ta bayyana cewar ‘’Wani daga cikin gidan, shi  ne ya kai ma ‘yansanda rahoton aukuwar  shi al’amarin, ita kumarundunar bata bata lokaci ba, sai ta dauki wanda aka yi ma raunukan zuwa asbiti, inda ka tabbatar da cewar ya mutu.’’

Exit mobile version