Takaddama Tsakanin Mai Gabatar Da Mai Laifi Da Lauya A Kan Faisal Maina

Faisal Maina

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Dangane da ci gaba da sauraron karar Faisal, Lauyan Hukumar EFCC ya bayyana cewar Faisal ya tsere zuwa kasar Amurka, sai dai Lauyan mai kare mai laifi ya ce ba haka lamarin yake ba, saboda ai an kama shi a Sakkwato ne.

A ranar Alhamis kuma sai ga takaddama tsakanin mai gabatar da mai laifi da mai kare shi dangane da batan dabon da Faisal Maina ya yi.

Yayin da lauyan Hukumar EFCC Mohammed Abubakar yake bayanin cewar ai Faisal ya tsere zuwa kasar Amurka, shi kuma lauya mai kare mai laifi cewa ya yi an kama shi ne a Sakkwato.

Alkalin babbar kotun tarayya ta Abuja, mai shari’a Mista Agban, ya bayyana cewar shi kan shi ya rude, saboda kuwa bai san ba’asin maganar wanda zai amince da ita ba, tsakaninsu.

“Mista Agban ya yi tambaya shin maganar wa zai amince da ita akan al’amarin gaskiya tsakanin mai gabatar da mai laifi da kuma wanda yake kare shi ?”.

Lokacin da aka cigaba da sauraren al’amarin shari’ar Faisal, Lauyan Hukumar EFCC, Mista Abubakar, ya bayyana wa mai shari’a cewar ana ta yin kokari na ba da umarnin kama Faisal, amma kuma har yanzu ba a samu cimma nasara ba.

Lauyan ya cigaba da cewa, “bayanan da Hukumar take da su, Faisal dai ya gudu zuwa kasar Amurka.” Amma a cewar Alkalin, ya samu labarin ‘yan sanda sun cafke Faisal a Sakkwato.

Sai dai kuma shi lauyan ya bayyana “dukkan labaran da aka ji dangane da al’amarin tamkar wani kanzon kurege ne, ko kuma zuki -ta- malle.”

Mista Abubakar ya yi karin bayani inda yake cewa dukkan fasfuna biyu na Faisal na Nijeriya da kuma na Amurka, duk suna hannun Hukumar kamar dai yadda hakan yana daga cikin sharuddan ba da belin. Amma bayanan da ke hannun hukumar su ne; Faisala dai ya yi kokari ya tsere ya bar Nijeriya, inda ya yada zango a kasar Nijar daga can kuma sai Amurka.

Ya kuma kara yin bayani mai nuna cewa ba kamar yadda ake ta jita- jita ba, shi Faisal ba ya hannun rundunar ‘yansanda ta Sakkwato, ko kuma Hukumar tsaro ta DSS kamar dai yadda aka ta yada maganganun da basu da tushe.

An kama shi a Sakkwato‘’ Amma kuma Lauya mai kare mai laifin Anayo Adibe, ya ce yana iya cewar ya yi magana akan wanda yake karewa cewa an kama shi yana kuma hannun ‘yansandan Sakkawato.

Bugu da kari, ya bayyana cewar akwai wasu maganganu daga kafofin watsa labarai da suke nuna rundunar ‘yansanda ta Jihar Sakkwato ta tabbatar da kama shi. Mista Adibe ya bayyana cewar Faisal ya kira shi a waya ranar da aka kai shi ofishin ‘yansanda na Sakkwato, sannan ya yi kokarin tuntubar Faisal a waya, sai dai hakar shi bata cimma ruwa ba, a domin ya kulle wayar sa.”

Bugu da kari ya bayyana su ‘yansanda sun ki bayyana wasu abubuwan da za su taimaka masu dangane da shi wanda suke neman.”

“Don haka wannan zuki ta malle ce,har ace shi wanda ake tuhuma da aikata laifin ya tsere zuwa kasar Amurka, inda ya kara bayanin cewa “Muna tsoron wani abu zai iya faruwa dangane da rayuwar shi Faisal, shi yasa muka ba ita kotun shawarar ta yi bincike akan ko ina ne ya makale.”

Shi kuma Alkalin ya bayyana cewar a halin yanzu yama rasa maganar da zai yi aiki da ita, har ma ya kai ga amincewa da ita, don haka ne ma ya dage sauraren ita karar har zuwa 31 ga watan Maris na wannan shekara ta 2021, inda kuma a wannan ranar ce zai yanke hukunci wanda lauya mai kare shi shigar inda yake neman wanda yake neman cewra yana bukata, ba wanda yake karewa damar a cigaba da sauraren dalilin da za a bayyana na kare shi.

Sai dai kuma shi Alkalin mai shari’ar, tamakar ma ya rufe duk sauraren wata magana wadda ta shafi Faisal, sanadiyar kuwa yadda ba kasafai ba ne, yake kawo kan shi kotun ba.

Exit mobile version