Muhammad Awwal Umar" />

Takaddamar Fili:  Rundunar ‘Yan Sanda Na Bincike Kan Hukuncin Kotu

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya na ci gaba da binciken wani hukuncin kotu da aka samu kan rikicin fili da ya shiga tsakanin Alhassan Ali Barde da Alhaji Hamza Yanga Buba kan wani fili a tsohon Shango wanda da ake kira Brighter.

Takardar hukuncin wanda rajistaran kotun daukaka kara da ke Abuja, Adamu Isah ya sanya wa hannu, mai lamba FHC/ABJ/CS/336/2015. Ta bayyana cewar kudurin lauyan mai shigar da kara, Barista Isah Galadima Suleiman (ESK) inda ya bukaci rushe duk wani gini da aka assasa a fili mai taken MTP 119. Don haka kotun ta umurci dukkanin masu wani gini a filin mai taken MTP 119 da ya gaggauta ta shi dan mika shi ga masu kara Ali Bade da jama’arsa.

Hukuncin kotun wanda aka zartar da shi tun ranar 12 ga watan Nuwamban 2014 ya dai baya da kura.

Kwamitin binciken na jami’an ‘yan sanda ta yi zamanta a radar Sarkin minna, ta bayyana cewar tazo bincike ne akan inda aka samu wannan hukuncin da alkalin da ya yi hukuncin.

Wanda aka kira dan bada shaidar sun hada da Alhassan Ali Bade wanda ke karar, sai Alhassan Angulu da Ali Chekgenbye mai unguwar Chekgenbye da ka fi sani da Suke Kahuta, mai Unguwa Shaba na Sabin gari da yace masarautar minna tayi mai canjin wajen aiki daga unguwar Sabin gari zuwa tsohuwar Shango da aka fi sani da Brighter baya da fili a unguwar kuma gadon komai a unguwar yana magana ne a matsayin mai unguwa.

Idan dai ba a manta ba akan wannan rikicin ne rundunar ‘yan sanda tayi awon gaba da wasu daga cikin masu unguwannin zuwa Abuja a kwanakin baya. Zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ta mayar da hankali kan jin inda aka samo wannan hukuncin da babban kotun daukaka kara da alkalin da ya yi hukuncin, duba da cewar lauyan wanda ake karar ya bayyana cewar kawai abinda ya sani kan wannan batu kotun da ke minna a karkashin tsohuwar mai shari’a Fati Lami Abubakar tayi watsi da karar duba da cewar babu nagartaccen Shaidan daga masu karar, bai san lokacin da aka daukaka karar ba kuma bai san alkalin da ya yi shaidar ba.

 

Exit mobile version