Connect with us

RAHOTANNI

Takaita Zirga-zirga: Ya Jefa Yan Gudun Hijira Mawuyacin Hali a Borno

Published

on

Biyo bayan bullar kwayar cutar korona a jihar Borno, wadda a tashin farko masana suka nuna fargaba, kuma hakan ya jawo gwamnatin jihar daukar matakan dakile yaduwar annobar, inda ta sanar da rufe jihar ta hanyar takaita shige da fice a fadin jihar na tsawon kwanaki 14, al’amarin da ya jefa yan gudun hijirar jihar mawuyacin halin ni’asu. Wanda tun kafin hakan, matsugunan sun dade su na fuskantar matsalar ababen more rayuwar yau da kullum.
A baya, hukumar dakile yaduwar cutuka a Nijeriya (NCDC), ta bayyana daukar ingantattun matakan fadakar da jama’a, domin kare kai daga barazanar cutar. Ta nuna muhimancin yin kaffa-kaffa a mu’amalar yau da kullum, tsabtace jiki ta hanyar yawaita wanke hannu, da dai sauran matakan kariya. Al’amarin da wasu ke yiwa kallon ‘harara’ a duhu; idan an kalli halin matsin tattalin arziki, rashin tsarin da matsugunan yan gudun hijirar kasar nan ke ciki, muhalli ne da ke fama cunkoson jama’a, karancin ruwan sha, cibiyoyin kiwon lafiya, abinci da tsabta, yayin da abu ne mai waya.
Bugu da kari kuma, wannan matsalar rikicin Boko Haram ta jefa sama da mutum miliyan daya a jihar kasancewa a sansanonin yan gudun hijira sama da 20 a jihar Borno. Kuma, sama da mutum miliyan bakwai ke fama da bukatar tallafin gaggawa, a yankin arewa maso gabas, idan an hada da sukurkucewar tsarin kiwon lafiya da karancin abinci mai gina jiki wanda ya kawo yawaitar mutuwar kananan yara.
Malama Yakura Babagana, yar gudun hijira ce da ke zaune a sansanin yan gudun hijirar Dalori, mai kimanin yan hijira 9,000 ta bayyana yadda wannan dokar shige da fice, da gwamnatin jihar ta kafa ta jefa su a mawuyacin hali. Ta ce suna cikin mawuyacin hali, saboda a halin da su ke ciki yanzu, suna zaune ne hannu-rabbana; babu abinci kuma babu kudi, sannan kuma tallafin da ake basu, bai zo hannun su ba.
”Wallahi rayuwar mu ta na cikin tsaka mai wuya, a wannan lokacin da aka takaita zirga-zirgar jama’a, kuma ga shi a cikin azumi. Matakin ya jefa yan gudun hijira cikin matsala sosai, sannan kuma ba mu da izinin fita domin neman sadaka ko bashi a wurin masu shaguna kafin a bamu tallafin da aka saba bamu, balle kuma wasun mu su samu damar fita su sayar da hulunan da mu ka saka”.
Ta kara da cewa, ”kuma kungiyar su na bamu tallafin naira 17,000 a kowane wata, amma gashi yanzu ba su bamu ba. Sannan gaskiya hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno ba ta bamu tallafin komai. Kuma ga karancin ruwan sha wa mu ke fama dashi, saboda wanda ake kawo mana a kowace rana baya isar mu”.
A nashi bangare kuma, Alhaji Gambo Gana a sansanin yan hijira na Banki ya bayyana cewa, a baya ma da kowa ke walwala ya matsugunan su ka karasa balle kuma a wannan yanayi wanda aka saka dokar hana zirga-zirga a jihar Borno.
”Haka kuma, rayuwar mu ta dogara ne ta hanyar tallafin da muke samu a hannun gwamnati da kungiyoyin jinkan gaggawa. Saboda haka muna shan wahala a halin da ake ciki; ga azumi ga babu zirga-zirgar jama’a balle mutum ya fita neman sadaka wurin jama’a”. In ji dattijon.
A hannu guda kuma, matsugunan da na bincika a cikin birnin Maiduguri, sun nuna matukar damuwa da halin da su ke ciki, sakamakon saka dokar hana zirga-zirgar. Sannan kuma sun bukaci gwamnatin jihar ta kawo musu daukin gaggawa, sun ce suna tsoron kilu ta jawo bau a wannan mawuyacin hali da su ke ciki.
Bugu da kari kuma, Gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Asabar ya kafa wani kwamitin mutum 16, domin raba wa masu karamin karfi kayan abinci don saukaka musu halin matsin da dokar rufe jihar ya jawo, dokar ta tsawon kwanaki 14.
Hakan ya zo a wata takardar manema labarai, mai dauke da sa hannun Malam Isa Gusau, jami’in hulda da jama’a, a ofishin Gwamna Zulum. Yan kwamitin su ne kwamishina a ma’aikatar kasuwanci, ta muhimman ayyuka, ta matasa da wasanni, sai mai ba gwamna shwara kan lamurran mata, tsare-tsare da ci gaba, da sauran su.
Malam Gusau ya kara da cewa, wannan kwamitin a karkashin kwamishina a ma’aikatar ayyukan gona a jihar Borno, Engr. Bukar Talba, ya bayyana cewa aikin raba kayan tallafi na gwamnati, kawai zai kunshi masu karamin karfi ne kawai masu bukata sosai, kuma Gwamna Zulum da kan sa zai rinka kula da yadda aiki ke gudana, a lokacin makatin takaita shiga da ficen don dakile yaduwar cutar koronan.
Haka kuma, shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta SEMA a jihar Borno, Hajja Yabawa Kolo, ita ce za ta rike mukamin sakataren kwamitin. Inda tuni kwamitin ya fara aiwatar da aikin da aka dora masa.
Kamar yadda kwamitin yaki da cutar korona a jihar, ya nuna mutum 15 ne su ka kamu da cutar, ciki har da dan gudun hijira daya- biyu kuma sun rasu.
A kokarin ta na dakile yaduwar annobar cutar korona, gwamnatin jihar Borno ta dakatar da jama’a kai ziyara zuwa sansanonin yan gudun hijira na tsawon makonni hudu a duk fadin jihar.
Matakin yana zuwa a matsayin kan-da-garki kan barkewar annobar korona a jihar mai yan gudun hijira kimanin miliyan 1.5 a sansanoni 23 a fadin jihar.
Hajiya Kolo, ta yi karin hasken cewa, gwamnatin jihar ta dauki matakin ne a matsayin daya daga cikin ingantattun matakan kariya daga yaduwar cutar korona a matsugunan yan gudun hijirar zuwa wasu sassan jihar. Sannan ta ce, daukar matakin ya zama dole saboda yadda cutar ke ci gaba da fantsama a wasu kasashen da ke da makwabtaka da jihar; Kamaru da Chadi.
Bugu da kari kuma, shugabar hukumar SEMA ta baiwa jami’an da ke kula da lamurran sansanonin yan gudun hijirar Gamboru-Ngala, Damasak, Kalabalge, Banki, Bama da Monguno umurnin cewa daga yanzu kar su kara barin wasu yan gudun hijira daga waje su shiga sansanonin.
Kolo ta ce, “Saboda mun sani kan cewa akwai kalubale da dama kewaye damu dangane da rahotanin yadda wasu su ka kamu da wannan cuta ta korona a wasu kasashen Kamaru da Chadi, wanda kuma mun hada kan iyaka da wasu garuruwan wadannan kasashe”.
“Saboda haka ba ma fatar tsunduma cikin wannan yanayi na wannan cutar mai wuyar sha’ani, wadda hatta manyan kasashe sun gagara murkushe annobar cutar cikin lokaci”.
”Sannan muna daukar matakin dakile matsalar ne daidai iya karfin mu, domin dakile yaduwar kwayar cutar a jihar Borno”.
Saboda haka, samun mutum na farko da ya kamu da kwayar cutar a sansanin yan gudun hijirar abu ne mai daga hankali matuka. Duba da yanayi da tsarin mazaunan yan gudun hijirar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: