Connect with us

NAZARI

Takaitaccen Tarihin Dakta Mamman Shata Katsina (3)

Published

on

Sashen Nazarin Halayyar Kasa Da Tsara Birane,

Jami’ar Gwamnatin Tarayya, Dutsin-Ma

Takardar da aka gabatar a taron kara ma juna sani na kasa da kasa a kan Dakta Mamman Shata katsina, a Jami’ar Bayero, Kano, daga ranar  Lahadi  zuwa Talata, 2 – 4  ga Satumba, 2018.

Ci gaba daga makon jiya

Buwayar Shata Daga Bakinsa

Ana zaune a Mazoji ta kasar Musawa ana hira cikin 1950, da borin wakar ya kamo shi sai ya nuna baryar darni na kofar gidan Mamman Gyaure ya ce ‘in sun kai su miliyan daya, to a zaro su dai-dai da dai-dai a rika a jiye su zai yi wa kowanne waka’. Sai aka ce ai an san ya wuce haka (Kankara, 2013) A cikin wasu wakokinsa yana yawan koda kansa da nuna buwayarsa. Misali, a cikin wakokin: Bakandamiya (1959-1989) da Na-Yalwa mai ban sha’awa Alhaji mai ban Haushi(1962)/ A cikin Alo alo….’ Yakan ce: 

Jagora :‘Na sa sulken yaki,

Iya kiban da za su buga,

Ba za su fada min ba,

Na shiga Bakandamiya(1962)

Yakan kuma ce: ‘…na ci Bauchi, na bugi Barno da ‘yar gangar nan(1975)Shata ba ya yin hawan gwaji ko kurga kafin ya yi waka (Shata, 1997; Sasuwai, 2011; Sa’I, 2014; Koko, 2014). Ma’ana a zauna a shirya abu a ji idan ya yi dadi ko yadda ake so sa’annan a tafi a gabatar da shi. To Shata ba ya yi ma waka haka. Da ya sadaukar da amshin waka a wajen yaransa shikenan sai su kama su yi ta yi shi kuma su bar shi da nashi aikin.An fi mamar makadin ba zato ba tsammani a wurin waka, daga inda aka mame shi za ya dauka ya fara waka, to ta nan za a gane ba ya yin kurga.

Idan mawakin ya shiga fage za ya fara waka, to komin tsawon mawaka ganin su yake ‘yan kanana kamar wadanni.  Ya taba ce wa su Gambo Garangozai wanda ya kada masa ganga ‘in mutum ya yi gardama game da wakata to a sami damin karan dawa ko na gero, a samu kato ya zauna ya rika dauko mani kowanne zangarni na karan dai-dai da dai-dai ni kuma zan iya yi wa kowanne waka har su kare’. Garangozai ya ce ‘ranka ya dade ai ka fi haka’. Shatan ya ce,  ‘wai ko mutum na gardama ana iya gwadawa a gani’ (Gambo, 2010; Kankara, 2013).

Muddin ya zauna a fagen waka, to da ya dauko wata ya na yi, sai ya ga kuma ga kimanin guda 10 can gefe, suna ta kokowa kowacce tana so ta iso wurinsa ya fara yin ta tukun. Ganin su yake da idanu kuru-kuru ba wai ba.  Makada Shata ya fahimci makadan fada da na noma da na maza sun koma gidan sa, ma’ana, sun fara kaucewa daga gidan su na asali su na komawa makadan jama’a, kamar su Kurna da Musa Dankwairo da Dan Anace,  da sauransu (Shata, 1984) .

Babu shakka, daga Shata waka ta kare saia yi abin da ba za a rasa ba. Shi ma da kansa ya taba fadi cewa daga gareshi waka za ta yi sassarfa, karfin ta za ya ragu. Gashi yau an ga hakan .

4.2 Buwayar Shata Daga Wakokinsa

Kafin 1948 ake jin wakokin Shata a arewa-maso-gabas (Niamey, 2018), zamanin da ya ke tashensa (Basiru, 2004; Hassana, 2014). A duk fadin arewa babu gidan rediyo, saboda haka ya yi daruruwan wakokin da ba a dauka ba. A wannan zamani inda duk aka kira shi buki sai ya yi kwanaki daga 3 zuwa 14 ya na waka, sai ya yi abinda ya kama daga kala 40, ko 100 zuwa sama. Wannan magana tana a tsakanin 1936 zuwa 1944 (Kankara, 2018b).  Jim kadan sai wasu mutane a Kano su uku; Tabansi, wanda ya bude Tabansi Records(TabansiAudioNigeria) a titin Abeokuta Sabongari, da Kayode da Ebele, a shekarun 1948 zuwa 1961 suka bude gidajen rediyo masu zaman kan su. Sai suka rika daukar wake-wake ana kaisu kasar Japan da Gwalkwas ana wankewa. Tabansi ya fi sauran shahara ga sana’ar.  Lokacin garmaho mai fashewa suke amfani da shi. Su sha hidimar daukar wakokin Shata na wancan lokacin (Kankara, 2013)Su suka yi fafutukar daukar wakokin sa a wancan zamani, inda har bayan zamanin garmaho ma ya shuda, sai aka juye wakokin a faya-fayan rediyo aka adana a gidajen rediyon kasar nan da wajen (Kankara, 2013)

Sai kuma aka shigo zamanin majigi. Su Alhaji Iro Gawo Katsina, su su ka yi yawo suka ragade arewa suna nune-nunen majigni, su na kuma karakainar daukar wakokin Shata. Fitattar wakar sa ta lokacin ita ce : Ya yi gyada ya yi auduga Baban Larai(1952). A lokacin, wakokinsa sun shiga zukatan jama’a, kamar inda ya ce:

Jagora : Aradu na san halin giya,

Ashe giya tana daidaita diyanDuniya,

Giya shegun banza,

Mai sa mutum ya ce shi Sidi ne,

Mai sa hawan kaho babu magani,

Mai sa mutum yawo kodare ya raba.

A wani zancen mai kama da wannan kuma Shata ya tafi Mashi cikin 1950 ya tarar ana caca kasa-rika, har ya yi ma ‘yan cacar waka waddaIro Gawo din dai ya dauka a garmaho. Amshin wakar shi ne Hakananne Mamman …’ inda yake cewa:

Jagora : Na sauka Mashi na tarar da arna na kati,

Caca mai sa da da uba fada,

Caca mai sa wa da kane fada,

In ban da caca,

Mutum ya kwan bakwaiyana hutawa,

Ya kwan bakwai ya na aiki,

Ya kwan bakwai ba ya komi

Ya kwan bakwai ya na shagali,

Na ga Garba na fada da ubanai

A dai cikin 1952 su Sani Kwantagora da Adamu Gumel da Malam Sa’idu Ango Zariya watau Jatau Na-Albarkawa (ma’aikatan karamin gidan rediyon Zariya) suka fara daukar wakokin Shata a nan Zariya. Hakan ya faru ne saboda aikin zabi-sonka da suka rika gabatarwa. Daga cikin ma’aikatan da ke faman daukar wakokin Shatan har da Alhaji Musa Musawa da Alhaji Lukman da Sha’aibu Makarfi. A wannan lokaci ba a bude gidan rediyon NBC Kaduna ba.

Jim kadan kuma a shekarar 1952 zuwa1954, watau tun zuwan Sarauniya na farko wata sabuwar hikimar ta shigo, duk garin Sarki sai a kai waya wadda ake kira wireless a kafa a kofar gidan Sarkin, kamar dai yanda ake ajiye injin wuta, a sanya masa waya a kewaye shi. To, daga can gidan rediyon da aka bude sai a rika watso shirye shirye (Hauwa ‘yar Bori, 1998). Da yake shirye shiryen inyamurai da Turawa ake sanyawa sai Hausawan arewa ba su damu da shi ba, tun da basu jin abin da ake cewa (Sabo, 1999) Alal misali a nan birnin Kano, a nan babban ofishi na gaban gidan Sarkin Kano aka kafa wayoyin. Sai a ranar Lahadin kowanne mako da karfe 2:45 na rana zuwa 3:45 da kuma karfe 9:00 zuwa 10:00 na safe ake sanya wakokin Shata.To, kafin wannan lokacin ne fa za ka ga jama’a su na tururuwa, suna zuwa daga gari-gari a taru wurin don a saurari wakokinsa (Sambo, 1999). Daga baya sai aka fara rarraba wannan waya ga hakimai, watau lokacin kai ya fara wayewa. Kurtun da batirin mashin ake hada shi a kai duk ranar da za a yi labarun Hausa ko za a sanya wakokin Shata. Za mu ci gaba a mako mai mzuwa. 
Advertisement

labarai