Connect with us

NAZARI

Takaitaccen Tarihin Dakta Mamman Shata Katsina (4)

Published

on

Sashen Nazarin Halayyar Kasa Da Tsara Birane, Jami’ar Gwamnatin Tarayya, Dutsin-Ma
Takardar da aka gabatar a taron kara ma juna sani na kasa da kasa a kan Dakta Mamman Shata katsina, a Jami’ar Bayero, Kano, daga ranar Lahadi zuwa Talata, 2 – 4 ga Satumba, 2018.

Ci gaba daga makon jiya

Sabo (1999) ya ce a lokacin duk Kano ba rediyo, ranar Laraba a nan babban ofis sai guda daya mai kamar lasifika ake kafawa duk unguwa, sai jama’a su kewaye suna sauraro. In dai kana son jin wakar Shata sai ka yi maza ka sami wurin tsayawa kafin lokaci ya yi. Kana kuma iya zuwa ko’ina inda wayar take ka ji. Wakokin: Akawu na Guga mai Biri da Barewawadda ya yi kafin ta Bawa Jankeda ta Mammada Dan Sambo Ketare da ta Barira Musawa da ta A’I kyaftin Zariya su aka fi sanyawa a lokacin. Sai daga baya (1954) aka fara sanya wakar Hakananane Mamman…’ mai taken ‘…da mu aka wakar Sarauniya/ (Doka, 1998)
Al’amarin Dahiru Modibbo da Mamman Shata ya sanya ya dada fifita shi a saman kowane mawaki. Ana amsar wakokin sa fiye da kima don tun ana binsa yana yi ana dauka a na’ura ana kuma gayyatarsa ya yi su dauka, da abin ya rincabe sai suka shirya shi da Dahiru Modibbo din cewa duk inda zakin mawakan ya je yana wasa ya rika aiko masa da kaset ko faifan wakar ko wakokin nan Kaduna, to haka ko aka yi don daga duk inda yake a ciki da wajen kasar nan da ya kwana biyu zuwa uku ya na waka to za ya tado Ibrahim Dannayari, wani marokinsa ya bashi kofin wakokin ya taho Kaduna ya kawo ma Dahiru Modibbo. Ga Dahiru Modibbo kofa bude take ana maraba da wakokinsa ko nawa ne zai aika ko zai kai, sabanin sauran mawaka su ba a cika sanya wakokin su ba a zamanin Modibbo. Hasali ma suna da iyaka ko ka’ida ko irin wakokin da zasu kai. Shi ko Shata ba shi da shamaki a kan wannan, don ko ihu ya yi a faifai ya aika za a amsa a sa ma duniya ta ji.
Modibbo (1972) ya shaida cewa, ‘abin da ya sa muka daukaka Shata fiye da sauran mawaka, jama’a muke wa aiki, jama’a suke kaunar Shata fiye da kowane mawaki a Nijeriya da wajenta.’ Sannan ya ci gaba da cewa:
« Idan za a yi nadin sarauta ko aure na wani mutum mai arziki sai an aiko mani wata biyu ko daya kafin bukin ana roko na in san yanda zan yi in kawo mutumi na (Shata) ko ace ana son a gan shi ba a taba ganin sa ba, ko an gan shi ana son a kara ganin sa, wani ma zai taso ne ya kawo takardar gayyatar sa gareni don tsoron in ya kai ma Shata ba za ya amsa gayyatar ba. Ire-iren wadannan takardu muna da su ajiye basu kirguwa. »
Shima kansa Dahiru Modibbbon ya na shan wahalar Shatan don ‘in sun gayyace shi sau 10 in sun yi sa’a ya je sau 2 sauran 8 din sai dai ya bar su da kunya, domin ya ce, “Ba Shata muka fi so ba, jama’a da ke son Shata muke wa aiki.”
Dokar waccan dama ta sama, ta sai an tace waka aji in zata yi wa mai sauraro amfani ta sa Shata ya kara samun dama ga Dahiru Modibbo, ta kuma sanya kafin mawaka su ankara ya mamaye su. Saboda galibin wakokinsa sun cika wadannan sharudda.
Tun cikin 1966 Shata ya shaida cewa bai san yawan wakokinsa ba (RTK, 1966) A jimlace, wakokin Sarkin Daura (1966 – 2007) sun kai 246. Na Muhammadu Adamu Dankabo kuma sun kai 264. Shi ma Alhaji Hassan Hadi da yake dan gata ne a wurin Shatan, wakokin sa sun kai sama da 200, inda daga ciki ma har Bakandamiyar sa ta musamman ya yi masa, wadda makadin da kan shi ya rada mata sunan (Hassan, 2010) Abin da ake nufi shi ne da yake falsafarsa ta yi yawa waka mai amshi daya sai ya rarraba ta kala-kala. Duk inda ya tsugunna sai ka ji ya yi kari ko ragi akan abin da ya fadi a wata wakar irin ta a baya. To matakin na Shata ya yi nisa, wakokin sn yi yawa, sai dai mu kintata kawai. A cikin littafin sa, Kankara (2013) ya yi kididdigar kwatankwacin yawan wakokin Shatan, inda ya ajiye su a gidan 10,000. Amma wani binciken na shekarar 1970 wakokin Shata da ke a rediyon Kaduna kurum sun fi 8,000 (Sani, 2003)
A iya tuna wakokinsa da dama inda a cikin wasu diyan wakarya ambaci buwayarsa. Wakoki irin su: Ku tashi ku falka ‘yan Arewa….’ (Disamba, 1966) da ta‘Yan Arewa mu bar barci, Najeriyar mu akwai dadi (Janairu, 1967) da ta Ku je ku huta farar hula, tunda Soja sun amshe mulkinsu (Disamba 1984) da ta Mu je gidan Ilimi ABU (Asabar 23/1/1988),duk akwai bayanin buwayarsa a cikinsu.
A cikinsu akwai wakar Nagode Shehu Maigidaje (1975) ma ya nuna tauhidi da buwayarsa domingaba dayanta dayanta Allah (SWA) ne. Duk wakokin sa na bege bayan rai (ko ta’aziyya) na tauhidi ne, su na nuna kaskanci ga Ubangiji ne, kamar a wakar Allah jikan Ciroman Gombe (1975), Dokta Mamman Shatan ya ce:
Jagora: Ni kam mutuwa tai man gaugawa,
Ta dauke Ciroman Gombe.
Kowa yammutu bai sauri ba,
Mu da mu ke nan ba mu dade ba,
Sai mun zo Chiroman Gombe.
Wakokin Bello Maitama na tauhidi ne, gaba dayan su, wasu ma tun a amshi ya ke nuna hakan. Har ma gashi amshin wata wakar shi ne: Maitama Bello Maganin Abu Allah kanen Ali (1981) To hakama wakokin Malam Ahmadu Bello (1964, 1966) da ta Bahillace Ja’e Dan Ali (1975) duka ya na surka tauhidi da yanda girman Allah Ya ke a cikin su. Nunatauhidi a wakar sa shi ke tabbatar da buwayar sa ga waka. Wakar Abu na Abu (Batsari, 1966, 1972) ma jigon ta na nishadi ne amma akwai wuraren da ya nuna tauhidi da tsoron Allah a cikin ta, inda ya ce:
Jagora: Tunda ka ji zugar mai waka,
Ka ki fadan dattijo,
Ko lafira kar ka bide ni.
Ya nuna ya shiga taitayin sa kuma ya gane akwai makoma wani wuri in an gama wannan rayuwar. Wakokin Domin Sayyadina Tijjani (1962) da ta Na Tsaya ga Annabi Muhammadu (SAW; Afrilu 1968) gaba dayansu na tauhidi ne da tunanin makoma gobe kiyama.
A fagen da basira ko wakar Shata ta ci gaba ba za a manta da TAN (TabansiAudioNigeria) da EbeleAguna da KayodeRecords masu daukar wakokinsa na garmaho suna aikawa da su Legas, daga can akai su Japan a wanke ba. A kuma tuna cewa a zamanin zaman Kano, daga can ya rika samun damar tafiya kudu watau Kurmi da wasu sassan gabashin arewa da wasu kasashen ketare irin su Gwalkwas (Ghana), Nijar, Jamhuriyar Benin, Aibari Kwas da sauransu, ko da ya ke daga baya ya yi wasu tafiye–tafiyen na musamman a lokacin ba ya na zaune a Kano ba. A Kanon ma dole a sanya Neja da KingsGarden da Wapa cikin lissafi don wasu wurare ne inda ya rika halarta har ya rika yin wasu wakokinsa na sahun gaba a jerin kundaye na wakokinsa da suka shahara a tsakiyar zamaninsa.
Zaman Dahiru Modibbo a NBC/RTK da shi kansa gidan Rediyon wani fifiko ne ga makadin. Idan ana labarin abubuwa ko wuraren da Shata ya sami galaba a sana’ar sa ta waka, sai an yi zancen zamansa Kano, bare da su Galadiman Kano Tijjani Hashim da Malam Ado Middle ko Ado Bayero su su ka zaunar da shi can har Sarkin Kano Sir Muhammadu Sanusi ya amince da shi. Zamansa Kano ya dada daga darajar wakokin sa ya kuma zaburar da shi tunda nan ne zucciyar arewa. Ba ma ta Shata ba, komi mutum ke yi in har ya je Kano to ya gama shahara. In kana waka ka je Kano har ta amsu a can, to wakar ka ta gama amsuwa ko’ina ma. Sannan dadin karawa sai gidan sarautar su ka kuma fifita Shatan sama da sauran mawakan fada. Afa tuna a Kano makadin ya zama abin girmamawa sosai (1954-1959). Ya dada gagara ya zama wani ‘gamda’are’, in ji sakkwatawa. Za mu ci gaba a mako mai zuwa.
Advertisement

labarai