Connect with us

LABARAI

Takara A APC: Sanata Dariye Ya Mayar Da Fom Dinsa Daga Kurkuku

Published

on

Garkamammen Sanata Joshua Dariye, wanda ke zaman kaso na shekaru 14 kan kama shi da aikata laifukan satan dukiyar al’umma a lokacin da yake mukamin Gwamnan Jihar Filato, ya mika fom din da ya cike na neman tsayawa Jam’iyyar APC takara a zaben da za a yi a shekara mai zuwa.

Sakataren yada labaran Jam’iyyar ta APC ne a Jihar ta Filato, Mista Chindo Dafat, ya tabbatar da hakan.

“Da gaske ne, Joshua Dariye ya karbi fom din neman yin takara a karo na uku. Yana cikin masu hankoron tsayawa APC neman kujerar majalisar dattawa a Filato ta tsakiya.” Ya kara da cewa, “Ya cike fom din har ma ya maido mana da shi.

“Sakataren mazabarsa ne ya zo ya sa hannu ya karba masa fom din. an kuma cike shi, magoya bayansa ma suna can suna ta yi masa kamfen kafin zaben na fitar da gwani.

A cewar sa, Dariye zai fafata ne da wasu ‘yan takaran su uku- Zakari Dimka, Sam Piwuna da Manji Pompori.

Sakataren ya ce, har yanzun Dariye yana da magoya baya a Filato ta tsakiya duk da halin da yake ciki, ya kara da cewa, “Tsohon gwamnan yana iya cin zaben na fitar da gwani daga gidan yarin.”

Ya ce, Dariye ya daukaka kara kan tsare shi din da aka yi, yana kuma iya samun nasara saboda suna ta yi masa addu’a.

“Baya ga yiwuwan samun nasarar na shi a daukaka karan da ya yi, muna kuma yi masa addu’an samun yafiya,” in ji shi.

Kan ko a shar’ance, Dariye yana da hurumin tsayawa takaran? Dafat ya ce, “Ba wata doka da ta hana shi ya sayi fom. Duk wanda ya zo neman sayan fom zai samu. Wannan magana ce ta tsarin mulki. Kotu ce kadai za ta iya cewa bai da hurumin hakan.

“In har Dariye ya ci zabe alhalin yana kurkuku, ai ba shi ne na farko da ya yi hakan ba. Iyiola Omisore, daga Jihar Osun ya taba cin zaben majalisar dattawa alhalin yana kurkuku,” in ji Dafat.

Sai dai Jam’iyyar PDP ta kwatanta lamarin da “Abin mamaki, bakon abu, abin kunya.”

“Abin da ban takaici, a ce an baiwa fursunan da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 14  fom domin ya tsaya a takarar zabe. Wannan akwai wasa da hankali a ciki,” in ji Mista Ben Shignugul, mataimakin shugaban Jam’iyyar ta PDP a Filato ta tsakiya.

“Amma sashe na 107 karamin sashe na 1 (d) na tsarin mulkin Nijeriya na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska ya bayyana cewa, ba wanda ya cancanci tsayawa takara, in har an taba daure shi a tsakanin shekaru 10 kafin tsayawansa zaben, ya kasance an daure shi ne kan ya aikata wani rashin gaskiya,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: