Takarar Gwamna: A. A Sule Ya Samu Tikitin APC A Nasarawa

Duk da kai ruwa rana da aka yi ta yi tun daga ranar  Lahadi har zuwa Litinin, an kasa gudanar da zaben sakamakon korafi da ‘yan takarar suka rika yi game da cewa, Gwamnati tana kokarin yin dauki dora.

An yi ta tantance masu kada kuri’un saboda zargin magudi, kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya ya tsaida gudanar da ayyukan zaben. Dole ta sa  aka kwana, kashe gari Litinin aka dora daga inda aka tsaya.

An kada kuri’un ba tare da rigingimu ba,  mutum 2341 ne suka yi rajista sannan 2337 suka kada kuri’an.

‘Yan goma shadaya ne suka taka rawa a gaban dubban masoya. Kuma kowa ya yagi rabonsa

Injiniya A. Abdullahi Sule ne  ya sami kuri’a mafi rinjaye,  926

Wadada Ahmad danyaya, 519

Mataimakin Gwamna, Silas Agara,  356

Zakari Ede,  88

Jafar Muhammad, 105

Muhammad mai kaya,  8

Hasan Liman, 4

Shehu Tukur, 9

Shu’aibu Kigbu, 10

Jemes Bala Angwazo, 7

Halilu Umar Enbulanza, 246

Bayan kammala isar da sakamakon zaben da Malamin zaben, Alhaji Abdullahi Adamu Andaka,  ya ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali kamar yadda ake so, kuma Jam’iyyar APC ita ke da nasara a babban zabe 2019.

Shi ma daya daga ‘yan takarar Barista Hasan Liman, ya yi jawabin godiya a madadin dukkanin ‘yan takarar. Haka zalika, shi ma dan takarar da ya lashe zaben ya yi kira ga sauran ‘yan’uwansa su hada karfi da karfe  su yi wa Jam’iyya aiki su kai ga nasara.

 

Exit mobile version