Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Takarar Shugabancin Majalisar Dattijai: ‘Yan Hijirar Borno Sun Azumin Kwana 5  Don Ndume 

by
3 years ago
in RAHOTANNI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

‘Yan gudun hijira sama da 10 ,000, daga matsugunai daban-daban da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno, suka gudanar da azumin kwana biyar tare da addu’o’i na musamman ga Sanata Muhammed Ali Ndume, domin samun nasarar dare mukamin shugaban majalisar dattijai ta tarayya, zubi na 9th.

Wanda kuma yan gudun hijirar suka bukaci uwar jam’iyyar APC ta kasa kan ta yi amfani da tsarin dimukuradiyya wajen zabar shugaban majalisar, kuma wanda ya cancanta tare da sanin hakkokin jama’a- musamman wadanda kungiyar Boko Haram ta tilasta wa kauracewa yankunan su, ta dalilin matsalar tsaron da ta addabi jihar Borno da arewa maso-gabas baki daya.

A zantawar sa da LEADERSHIP A YAU JUMA”A, ranar Laraba, a birnin Maiduguri, babban limamin masallacin yan gudun hijirar Bakassi, wanda ya kunshi kimanin mutum 39, 000, Malam Usman Mohammed ya bayyana cewa, Musulmi da Kiristocin sansanin sun yi hadin gwiwa da junan su wajen gudanar da addu’in samun nasara ga Sanata Ali Ndume; wajen dare kujerar shugabancin zauren majalisa, saboda gudumawar da yake baiwa yan hijirar.

Labarai Masu Nasaba

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Alfanun Koyon Harsunan Kasashe Ga Daliban Kimiyya – Farfesa Gwarzo

Har wala yau kuma, malamin ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima tare da daukwacin jigajigan jam’iyyar APC dake jihar Borno da baki dayan arewa maso-gabas kan su dunkule wuri guda tare da goya wa Ali Ndume baya- mutumin da ya bayyana a matsayin na kowa da kowa, wajen kasancewa shugaban majalisar dattijan Nijeriya mai zuwa.

Imam Usman ya bayyana cewa, saboda duk da barazanar kai hare-haren mayakan Boko Haram a garin Pulka da ke karamar hukumar Gwoza; ranar zabe, amma bai hana al’ummar jihar Borno fitowa kwan su da kwarkwatar su wajen yiwa Muhammadu Buhari ruwan kuri’a tare da yan takarar jam’iyyar APC ba. Sannan da kokarin da Ali Ndume, wajen ganin shugaban kasa da jam’iyyar ta samu gagarumin rinjaye a jihar Borno fiye da kowacce jiha.

Bugu da kari kuma, suma yan gudun hijirar sansanin’ Arabic Teacher’s Billage’ da na karamar hukumar Gwoza da ke jihar, kuma mahaifar Sanata Ali Ndume, suna gudanar da makamancin azumin tare da addu’o’in. Wanda malaman suka fara gudanar da azumin kwana biyar tare da addu’o’in samun nasara ga dan su.

“Mun zabi kimanin yan gudun hijira 10, 000, daga sansanonin gudun hijirar Bakassi da na ‘Arabic Teacher’s Billage’ domin mu gudanar da azumin kwana biyar tare da addu’o’in samun nasara ga Sanata Ali Ndume, saboda ya samu nasarar kasancewa shugaban majalisar dattijai a zubi na 9”.

“Har wala yau kuma, muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da baki dayan yan majalisu da kusoshin jam’iyyar APC na wannan yanki, su mara wa Sanata Ali Ndume baya dimin daga bartabar wannan shiyya ta arewa maso gabas”.

Da take tofa nata albarkacin bakinta, shugabar mata a sansanin yan gudun hijirar Bakassi, Halima Bukar, kuma yar asalin karamar hukumar Guzamala, a jihar Borno, wadda ta bayyana kwarin gwiwa dangane da nasarar Sanata Ali Ndume, a matsayin zabi mafi dacewa ya shugabanci zauren majalisar, kuma babbar dama ga raunanan yan gudun hijirar Borno da Arewa maso gabas baki daya.

Hajja Halima ya kara da cewa, Sanata Ndume hazikin mutum ne wanda gwarzantakar sa ta bayyana a tsakanin tsarar sa, kuma muddin ya kasance shugaban majalisar, ko shakka babu, yankin arewa zai bunkasa ta dalilin muhimman kudurorin da yake dasu na bunkasa yankin da ingantattun ayyukan raya kasa.

 

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Bayanai Game Da “Taruka 2” Na Kasar Sin

Next Post

Zaben Gwamnoni: INEC ta fara rarraba kayan zabe a Yobe

Labarai Masu Nasaba

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

Fashewar Gas: An Zakulo Gawarwaki 9 A Ginin Da Ya Rushe A Kano

by
1 day ago
0

...

Alfanun Koyon Harsunan Kasashe Ga Daliban Kimiyya – Farfesa Gwarzo

Alfanun Koyon Harsunan Kasashe Ga Daliban Kimiyya – Farfesa Gwarzo

by Khalid Idris Doya
1 day ago
0

...

Ranar Iyali Ta Duniya: Ma’aikatar Jinkai Za Ta Kai Wa Iyalai 30 Daukin Kuncin Rayuwa

Ranar Iyali Ta Duniya: Ma’aikatar Jinkai Za Ta Kai Wa Iyalai 30 Daukin Kuncin Rayuwa

by
2 days ago
0

...

Rikicin Ukraine Ya Haifar Da Karin Tsadar Kayan Abinci A Nijeriya —Rahoton NBS

Rikicin Ukraine Ya Haifar Da Karin Tsadar Kayan Abinci A Nijeriya —Rahoton NBS

by
3 days ago
0

...

Next Post

Zaben Gwamnoni: INEC ta fara rarraba kayan zabe a Yobe

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: