Takardar Da Ta Tona Karairayin Amurka
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Takardar Da Ta Tona Karairayin Amurka

byCMG Hausa
3 years ago
Amurka

A karshen watan Mayun da ya gabata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya gabatar da wani jawabi a kan manufofin kasar Amurka a kan kasar Sin, inda ya sha tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da ma shafa wa kasar bakin fenti a kan manufofinta na gida da waje.

Sai dai kome kokarinta, ba ta iya boye ainihin burin da take neman cimmawa na dakile ci gaban kasar Sin daga dukkan fannoni ba. A ranar 19 ga wata da dare, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata takarda mai taken “Kura-kurai da ke tattare da ra’ayin Amurka game da kasar Sin da ma ainihin gaskiyar abubuwan”, inda ta fallasa “yadda yaudara, munafunci da hadarin dake kunshe cikin manufofin Amurka game da kasar Sin” tare da cikakkun bayanai da kuma alkaluma.

Wace ce ke lalata tsarin kasa da kasa? Wace ce kuma ke keta hakkin dan Adam a sassan duniya da ma satar sauraron kusoshin kasa da kasa? Wannan takarda mai kunshe da dogon bayani ta zayyano kura-kurai da ma karairayi kimanin 21 da ke tattare da manufofin kasar Amurka a kan kasar Sin, ta kuma samar da cikakkun bayanai da alkaluman don fadakar da kasashen duniya a kan yadda kasar Amurka ke haifar da rikici ga duniya, da kuma tilastawa wasu kasashe su bi tsarinta a harkokin diplomasiyya, da ma yadda ta fi kowace kasa a duniya wajen lalata hakkin dan Adam da kuma kai hare-hare ta yanar gizo.

Daga cikinsu kuwa, furucin ’yan siyasar Amurka dake cewa wai “Sin na haifar da kalubale mafi tsanani ga tsarin kasa da kasa” na daga cikin munanan karairayi da suka yi, kuma abin dariya ne yadda suka furta cewa, wai “Amurka na kare dokoki da yarjejeniyoyi da ka’idoji da ma hukumomi na kasa da kasa.” Ban da haka kuma, kasar Amurka tana kuma kokarin kafa “tsarin tattalin arzikin Indo-Pasifik”, a yunkurin kafa tsarin ka’idojin ciniki da ke karkashin jagorancinta, tare da tilasta kasashen shiyyar da su katse huldar ciniki da kasar Sin.

Tsarin wanda ke kare moriyar Amurka, ya kuma haddasa cikas ga farfadowar tattalin arzikin duniya bayan annoba. Kome kokarinta, Amurkar ba za ta iya boye burin da take neman cimmawa na dakile ci gaban kasar Sin da kuma neman shimfida tsarin yin babakere a duniya. (Lubabatu)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Arsenal Ta Kammala Sayan Vieira Daga Porto

Arsenal Ta Kammala Sayan Vieira Daga Porto

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version