Abubakar Abba" />

Takin Zamani: Bankin AfDB Ya Jaddada Aniyar Aiki Da AFAP A Afirka

Shugaban Bankin Raya Nahiyar Afirka AfDB Dakta Akin Adesina ya jaddada aniyar bankin na yin aiki da Cibiyar samar da takin zamani (AFAP) don karfafa samar da takin zamani wajen samar da takin ga matsakai da nabyan manoma dake yankin Afrika.

Shugaban Bankin Raya Nahiyar Afirka AfDB Dakta Akin Adesina ya sanar da hakan ne alokacin kulla yarjajeniya da Cibiyar ta AFAP, inda ya yi nuni da cewa, an samu chanje-chanje da dama a fannin yin noma a Afrika da kuma samar da takin zamani, inda Shugaban ya kara da cewa, akwai bukatar AFFM ta dan gusa ga bayar da taimako ga kananan manoman dake a yankin na Afirka.

Shugaban Bankin Raya Nahiyar Afieka AfDB Dakta Akin Adesina ya ci gaba da cewa, akwai bukatar a kara karfafa samar da kudade da kayan aiki noman rani.

Dakta Akin Adesina ya yi nuni da cewa, fannin aikin noma yana samar da dimbin ayyukan yi.

Shi ma a nasa jawabin a wurin taron Babban Darakta na sashen AFAP dake a Nijeriya Ebrima Faal ya sanar da cewa, dokar kasa ta samar da ingantaccen tajin zamani NKC ta shekarar 2019 ta kara karfafawa gwamnati gwaiwa wajen mayar da hankali a fannun, inda ya yi nuni da cewa, shirin yazo akan gaba idan akayi la’akari da irin natakan da gwamnati take dauka don kara kwarin gwaiwar sarrafa takin zamani a gida.

Bugu da kari, a shekarar data gabata, masu ruwa da tsaki sun gana a dakin taro na Babacar N’Diaye mallakar bankin AfDB dake a shalkwatar Avidjan da kasar Cote d’Iboire kan yadda za’a zuba kudade wajen samar da takin zamani a Afrika ta Yamma.

A taron, mahalartan sa sun tattauna kan bukatar a samar da kudade ga fannin samar da takin zaman, inda AFFM ce ke bayar da tallafi tare da kungiyar samar da takin zamani ta Afrika ta Yamma.

Babban sakamakon kulla yarjejeniyar a tsakanin kungiyar samar da takin zamani ta Afrika da kuma (ECOWAS), wacce anyi tane bisa nufin karfafa samar da takin zamani a yankin an shirya tsaf, don wanzar da matakin a yankin.

Jami’in a AFFM, bayan doguwar tattaunawa ta kwana biyu, kan samar da kwakwarar mafita, yace a wannan lokacin ya rage mana muyi amfani da kafar yanar gizo don tabbatar da cin nasara ga abinda aka sanya a gaba ya zamo gaske.

Shi ma Shugaban OCP a Nijeriya Mohammed Hettiti ya amince da ra’ayin Adesina, inda ya ce, Nijeriya da kuma sauran kasashen Afrika, akwai bukatar su rage karancin nakasun da suke fuskanta akan kasar noman su ta hanyar rungumar yin amfani da takin zamani da kuma yadda a ke yin amfani dashi.

A cewar Shugaban OCP a Nijeriya Mohammed Hettiti, takin zamani yana taka muhimmiyar rawa wajen habaka amfanin gona ga manoma, amma tare da hadin sauran jayan aikin noma kamar samar da Iri da sauran su.

Sai dai, burin ya kara karuwa na takin zamani, inda hakan ya sanya kwararru a fannin da suka fito daga Cibiyar bunkasa takin zamani ta kasa da kasa (IFDC) da Cibiyar gudanar da binciken aikin noma ta Afrika Tsakiya (CORAF) da kuma masu ruwa da tsaki masu zaman kansu su ke kan yin aiki kafada da kafada don kirkirar kafar yada bayanai ta zamani wajen samar da Irin noma da kuma takin zamani.

Jiga-jigai a fannin samar da Iri da takin zamani a Afirka ta Yamma suna kan mataki na karahe na tsara kafar yanar gizo da zata taimaka wajen shawo karshen kalubalen da ake fuskanta wajen da kayan aikin noma ga manoma.

Ofishin Hukumar USAID dake a yankin Afirka ta Yamma ce ta samar da kudade ga shirin FFEG ta hanyar aikin yankin noma na (EnGRAIS) tare da yin hadaka kan gudanar da bincike a fannin noma, samar da ilimi da kuma samar da ci gaba (PAIRED).

Exit mobile version