Takun Saƙar Kachikwu Da Baru: Dole Ne Buhari Ya Sauke Su Daga Kujerarsu –Kwamitin Majalisar Dattawa

Daga Khalid Idris Doya

Shugaban kwamitin albarkatun ɗanyen man fetur na majalisar dattijan Nijeriya Sanata Tayo Alasoadura ya ƙirayi shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da babbar murya da ya gaggauta dakatar da ƙaramin ministan albarkatun man fetur Dr. Ibe Kachikwu da babban manajan gudanarwa na NNPC Dakta Maikanti Baru ba tare da ɓata lokaci ba a cewarsa yin hakan ne zai bai wa majalisar ƙasa damar gudanar da sahihiyar bincike a kan lamarin.

Alasoadura ya ce, musamman ganin cewar majalisar ƙasa tana kan gudanar da bincike kan zargin da ake yi na bada kwangilar biliyan 25 ba tare da samun amincewa gami da sahalewar masu ruwa da tsaki kan sha’anin ba, a bisa haka akwai buƙatar a dakatar da su daga kujerarsu domin samun damar gudanar da sahihiyar bincike.

Ɗan Majalisa Alasoadura wanda ya bayyana haka a wata hira da yayi da manema labarai a ƙarshen makon da ya gabata.

Ya ci gaba da cewa “na tabbatar da cewar mutumin da ya ke  gudanar da aikinsa kullum-kullum a wata ma’aikata ba za a samu zafin gudanar da ingattacciyar bincike a kansa ba; saboda bincike zai hau kan neman wasu bayanai ba lallai ne kuma idan mutumin da ake bincike a kansa ya bari a samu haƙiƙanin rahotonin ba matuƙar yana kan aikinsa. Dole ne a ɗauki matakin da babu wani abun da zai ɓace a sa’ilin da aka fara gudanar da binciken nan”.

Ya ce, a bisa haka dole ne dukkaninsu biyun su bar wannan kujerun nasu, alabashi bayan an

kammala bincike a duba iyuwar dawo das u bakin aiyukansu.

Sanatan, wanda ke wakiltar mazaɓar Ondo ta tskaiya ya kuma ce babban matsalolin da suke jawo rikita-rikita  sha’anin albarkatun man nan ya biyu bayan jifga wa kai aiki ne da shugaban Nijeriya Muhammdu Buhari ya yi, inda ya kasance shi ne babban ministan albarkatun man fetur kuma shine shugaban ƙasa.

Hakazalika Shugaban kwamitin albarkatun ɗanyen man fetur ya kuma nuna cewar dole ne fa Buhari ya yi murabus daga minstan mai ya nemo wanda zai iya riƙe wannan ma’aikatar domin a samu inganta sa’anin yanda ya dace “Ku yi hukunci kan yawan matsalolin da suke addabar ƙasar mu halin yanzu, na yi imanin mai girma shugaban ƙasa ya kamata a maida hankalinsa kan wasu janibobin ya nemo wani ya ba shi kujeran babban ministan albarkatun man wanda zai ke samun rahoton abubuwan da suke tafi akai-akai a ƙalla sau ɗaya a mako, hakan zai rage wasu matsalolin da ake fama da su”. A cewarsa

Da ya ke  tabbatar ma wata kafa adadin kamfanonin da majalisar dattawan ke kan bincike kan wannan kwangila na bilyan 25 Alasoadura ya ce bincikensu zai iya kaisu ga gayyato wasu baya ga kamfanoni guda 40 ɗin da suke kan bincika a halin yanzu “Muna bincike a kansu, saboda muna so mu kai ga gano tushen matsalar, idan kuma gudanar da bincikenmu ya hauro ma da kamfanonin da bamu ambace su za mu gayyace su domin amsa mana tambayoyinmu. Amma yanzu waɗannan 40 ɗin sune muke kan bincika a halin yanzu domin gano sahihin zance”. A cewar shugaban

LEADERSHIP A Yau ta labarto cewar kamfanonin da yanzu haka suke cikin binciken na majalisar ƙasa kan haramtaciyyar kwangilar biliyan 25 sun haɗa da ‘Oando, Sahara Energy, MRS Oil & Gas, AA Rano, Bono, Masters Energy, Eterna Oil & Gas, Cassiɓa Energy, Hyde Energy, Brittania U, North West Petroleum, Optima Energy, AMG Petroenergy, Arkiren Oil and Gas Limited and Shoreline Limited.’

Sauran kamfanonin sun haɗa da Entourage Oil, Setana Energy and Prudent Energy, Trafigura, Enoc Trading, BP Trading, Total Trading, UCL Petro Energy, Mocho, Teɓier Petroleum, Heritage Oil, Leɓene Energy, Litasco Supply and Trading, Glencore, Hindustan Refinery, Varo Energy, Sonara Refinery, Bharat Petroleum da kuma  Cepsa dukkaninsu suna kan fuskantar bincike kan badaƙalar, jerin kamfanonin da aka samu daga sashin hukumar mai ta ƙasa NNPC.

A wata sabuwa kuma, shararren mawaƙin nan, wato Charly Boy a ƙarƙashin gamayyarsa mai suna ‘Our Mumu Don Do’ sun shirya tsaf domin gudanar da zanga-zanga kan wannan badaƙarar kuɗin kwangila na zunzurutun kuɗi hai naira biliyan 25 ba tare da bin ƙa’idojin da suka kamata ba.

Sakatare mai magana da yawun tawagar, Raphael Adebayo ya bayyanawa majiyarmu hakan inda ya ci gaba da cewa gamayyar ƙungiyarsu ta kammala shiri tsaf domin gudanar da jerin gwanon kan rashin ɗaukan mataki cikin gaggawa da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ƙi yi kan lamarin, alhali kuma rahoton ya iskeshi ta hannun mataimakinsa Yemi Osinbanjo da sauran waɗanda abun ya shafa dukka suna da cikakken masaniya kan lamarin.

Mai magana da yawunsun ya ce suna ci gaba da duba lokacin da ya dace ne, amma ya bayyana cewar za su gudanar da wannan jerin gwanon ne a cikin makon nan “mun zura ido muna ga wacce mataki ne fadar shugaban ƙasa za ta ɗuaka kan Kachikwu da kuma shi Baru. Buhari da Baru sun yi sallah a babban masallacin tarayya tare, ya ganshi don haka zamu jira daga nan zuwa talata mu ga wacce mataki za a ɗauka daga nan kuma zamu bayyana matakinmu na fitowa zanga-zanga”. Inji su Charley.

Exit mobile version