Wani dan siyasa da aka sanya wa suna bayan sanannen dan siyasar Jamani kuma shugaba, Adolf Hitler ya lashe kujera a zaben Namibiya, amma ya ce ba shi da shirin mamaye duniya.
Mista Adolf Hitler Uunona, wanda aka zaba da kashi 85 cikin 100 na kuri’un, ya fadawa jaridar Bild cewa, “ba shi da wata alaka da akidar ‘yan Nazi(‘yan Hitila). Ya lashe kujerar ne a tikitin jam’iyyar SWAPO mai mulki, wacce ke mulkin Namibia tun samun ‘yancin kai daga Afirka ta Kudu ta wariyar launin fata a 1990.”
Namibia, tsohuwar mulkin mallakar Jamani da aka fi sani da Jamhuriyar Afirka ta Kudu ta Yammacin Afirka, har yanzu tana zaune ne a wurin karancin al’ummar jamani, da karancin tituna, wurare da mutane har yanzu sunaye da Jamani.
Ya ce, “Mahaifina ya sanya min sunan wannan mutumin ne ba tare da sanin abin da Adolf Hitler ya tsaya ma wa ba. A lokacin da ni ke yaro ina ganin sunan ne a matsayin cikakken suna na al’ada. Tun ina saurayi na fahimci cewa wannan mutumin yana son cinye duniya ne baki daya.”
dan siyasan ya ce, matarsa na kiransa Adolf, ya kara da cewa, yawanci ana kiransa ne da Adolf Uunona, amma loakci ya kure da zai sauya sunansa a hukumance.
Ya kara dea cewa, “Kasancewar ina da wannan sunan ba yana nufin ina so in mamaye Oshana ba ne, hakan nufin wurin da na ci zaben ne kawai. Haka zalika, ba yana nufin ina kokarin neman mamayar duniya bane.”
Uunona ya samu kuri’u 1,196 a zaben da ya gabata idan aka kwatanta da 213 ga abokin hamayyarsa, inda ya mayar da shi kan kujerar majalisar yankin wanda a baya ya ci a shekarar 2015. An gajarta sunansa da “Adolf H” a cikin jerin sunayen ‘yan takarar da aka buga a cikin jaridar gwamnati, amma sunansa ya bayyana cikakke akan shafin yanar gizon sakamakon zabe.