Takwas Sun Mutu A Harin ’Yan Bindiga Jihohin Ribas, Ebonyi Da Anambra

Daga Rabiu Ali Indabawa,

’Yan bindiga sun yi barna a jihohin Ribas, Ebonyi da Anambra, inda suka kashe akalla mutane takwas. ‘Yan fashin, wadanda suka kashe mutane biyar a Jihar Ribas da wasu uku a Anambra, sun kuma kai hari kan wani ofishin’ yan sanda a jihar Ebonyi inda suka bankawa wani gini da motoci hudu wuta.

Kashe-kashen na Jihar Ribas sun biyo bayan mamaye garin Zor-Sogho da ke Karamar Hukumar Khana. An gano cewa, ‘yan fashin wadanda suka afka wa jama’ar, sun yi harbi mai karfin gaske kuma a cikin hakan sun harbe mutum biyar yayin da suka jikkata wasu. Wata majiya ta ce ‘yan fashin sun gudanar da aikin ne da misalin karfe 10 na dare.

Ya ce lamarin ya tayar da hankalin al’umma, ya kara da cewa mazauna garin da yawa sun tsere cikin daji saboda tsoro. Kungiyar ‘Ogoni Debelopment Initiatibe’ (OYDI) ta yi Allah wadai da kisan wadanda aka kashe din, tana mai bayyana shi a matsayin na dabbanci. Kodinetan kungiyar na kasa, OYDI, Imeabe Sabiour Oscar, ya alakanta lamarin da kungiyar asiri, yana mai cewa har yanzu matasa a Ogoni suna buyo a karkashin wannan haramtacciyar hanyar don aikata miyagun laifuka.

Ya ce: “Mun yi mamakin yadda a wani lokaci muke wa’azin zaman lafiya, wasu bata garin matasa za su ci gaba da daukar bindigogi don kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. “ wannan ba rahoto ne mai kyau ba kwata-kwata.

A gare mu, zaman lafiyar al’ummominmu shi ne mafi mahimmanci. Muna ba matasanmu shawara su guji tashin hankali su rungumi zaman lafiya ko kuma su shirya fuskantar fushin doka.

“Muna kuma amfani da wannan damar wajen yin kira ga gwamnati, hukumomin tsaro da su binciki wannan lamarin don tabbatar da cewa irin wannan aikin ba’a maimaita shi ba. “Muna son wadanda ke bayan wannan lamarin a kama su da kuma hukunta su domin mu samu zaman lafiya a tsakanin al’ummomimmu.”

Amma ‘yan sanda a jihar sun ce ba a sanar da su batun ba. A jihar Anambra, wasu ‘yan bindiga sun afkawa wata coci a Azia, Karamar Hukumar Ihiala, inda suka kashe wani mutum tare da wasu mutum biyu. An kashe mutumin, mai suna Ken Ekwesianya, tare da matarsa da ‘yarsa a harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambara, Mohammed Haruna, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya, ya ce ana ci gaba da bincike don gano yadda lamarin ya faru. “Ana ci gaba da bincike don gano yadda lamarin ya faru kuma ana ci gaba da kokarin don kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki tare da gurfanar da su a gaban shari’a,” in ji shi. Wasu ‘yan bangar da ba a san ko su wanene ba sun kai hari hedkwatar ‘yan sanda reshen Onicha da ke Isu, wani gari a Jihar Ebonyi.

An tattaro cewa’yan dabar, da misalin karfe 3:25 na yamma sun cinna wuta a daya daga cikin gine-ginen da ke harabar ofishin ‘yan sanda da motocin sintiri hudu. Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Lobeth Odah, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce ana zaton maharan ‘yan kungiyar ‘Indigenous People of Biafra (IPOB)’ ne.

Odah ya ce, wani jami’in dan sanda daya ya samu rauni ta hanyar saransa da adda sakamakon harin. Ta ce: “A yau da misalin karfe 3:25 na yamma, wasu‘ yan iska wadanda ake zargin mambobin kungiyar ‘Proscribed Indigenous People of Biafra,’ (IPOB) sun kai hari hedkwatar Onicha, Isu a Karamar Hukumar Onicha ta Jihar Ebonyi, sun cinna wa dangaren hagu wuta suka kone wasu gine-gine da motocin sintiri hudu.

“Wannan ya biyo bayan barazanar da haramtacciyar kungiyar da ke zargin cewa ‘yan sanda na kare makiyayan da suke zargi da alhakin kashe daya daga cikin mambobinsu, Nwite Njoku”. “Wani dan sanda ya samu rauni ta hanyar sara da adda, a yayin harin kuma yana asibiti yana amsar magani.

“A halin yanzu, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Ebonyi, CP Aliyu Garba ya tafi rangadin tantance yankin tare da ganawa da masu ruwa da tsaki a cikin yankin don neman hanyoyin da za a gudanar da bincike kan lamarin.

Exit mobile version