Nasir S Gwangwazo" />

Talakan Najeriya Ba Mai Yawan Bukatu Ba Ne – Osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya ya bayyana cewa, a fahimtar da ya yiwa talakawan Najeriya sun sha bamban da na sauran kasashen duniya kasancewarsu ba masu yawan zuwa da bukatu ba ne, inda bukatun nasu kadan ne.
Osinbajo ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke jawabi ga magoyan APC a fadar shugaban kasa, lokacin da a ka shirya mu su liyafar girmamawa.
Mataimakin shugaban kasar ya tunano cewa, abubuwan da ya gani a lokacin ya ke zagaya jihohi domin yakin neman zabe abu ne da ke tabbatar ma sa da hakan, domin abu ne da ke nuna cewa har yanzu ’yan Najeriya su na yarda da shugabanninsu kuma su na taimaka mu su.
“Ba su tambayar abinda ba zai yiwu ba. Don hakan ne mu ka jihohi da dama a kasar, inda mu ka irin dimbin ayyukan da ke damfare da su ke bukatar a aiwatar da su kuma mu ka auna irin karfin da mu ke da su na yiwuwar aikatawa.
“Abinda mutane ke bukata ba wanda ba zai yiwu ba ne, domin ba mai yawa ba ne.
“A gaskiya ma ni ban ga kasar da ’ya’yanta ba su da neman bukata ko ta halin kaka irin ‘yan Najeriya ba. Su na da karamci komai talaucin da ke damun su.
Osinbajo ya ce, akwai bukatar gwamnatin Shugaba Buhari ta sake kusanta da talakawan kasar sosai.
“Na ji a raina cewa lallai akwai bukatar mu sake bauta wa jama’a. abinda kawai su ke bukata shi ne a ba su dama su fadi albarkacin bakinsu a tattauna da su.
“Yakamata mu nemi hanyar da za mu rika saka su a cikin al’amura ta yadda za su zama kusa da mu.
“Daya daga cikin korafin da su ka yi a kan mu shi ne ba ma kusantar su mu tattauna da su kai-tsaye yadda ya dace. Don haka ba su san me mu ke ciki ba, mu ma ba mu san me su ke ciki ba. Wannan matsalar za mu gyara yanzu.”
Mataimakin shugaban kasar ya kuma amince da cewa, matakin da gwamnatin APC ta faro a 2015 na kusantar ’yan kasa ya yi kaura bayan da gwamnati ta yi nisa a fadin kasar, wanda hakan ya sanya hukuma ta rasa goyon bayan wasu gurare, musamman ma saboda tasirin kafafen sadarwa na zamani.
Daga nan sai ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta yi gyara kan hakan, domin dinke wannan baraka ta hanyar shigo da wasu sababbin hanyoyin saduwa da talaka kan shirye-shirye da tsare-tsaren gwamnati.

Exit mobile version