Connect with us

SIYASA

Talakawan Nijeriya Ba Su Gamsu Da Gwamnatin Nan Ba – Shehu Yusuf Kura

Published

on

Fitaccen dan Jarida wanda ya yi aiki a nan gida Nijeriya
a sassa da dama da kuma wurare daban-daban a wajen
kasarnan, a yanzun haka dan siyasa, shi ne babban mai
taimaka wa Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Yarima Uche
Secondus, kan harkokin yada labarai da wayar da kan
jama’a, a Arewacin Nijeriya. Shehu Yusuf Kura, ya zanta
da wakilin mu, UMAR A HUNKUYI, sa’ilin da ya kawo wata
ziyara a nan Kaduna, inda ya yi magana kan bambancin
mulkin Jam’iyya mai ci yanzun da mulkin Jam’iyyar PDP
a baya, sannan ya yi magana kan halin da kasa ke ciki a
halin yanzun, ya karkare maganan shi da yanda Jam’iyyar
ta su ta PDP ta shirya fitar da kasan nan daga halin da ya
kwatanta na kunci, matsi da rashin zaman lafiya. A sha

karatu lafiya:
Yanzun shekaru
uku kenan da hawan
wannan gwamnatin ta
Jam’iyyar APC, watau
akalla shekaru uku da
saukan gwamnatin ku
ta Jam’iyyar PDP, in
abin a yi kwatanci ne da
gwamnatin naku ta PDP,
wace irin rawa kake ganin
wannan gwamnatin ta
APC ta taka?
A gaskiya wannan
tambaya ce mai saukin
amsawa, saboda Hausawa
na cewa, “In ka shigo gari,
ka saurari daka,” domin ba
ma mu ‘Yan Jam’iyyar PDP
ba, talakan Nijeriya duka, ya
ji ya kuma gani a jikinsa. Shi
kansa Mai girma Shugaban
kasa, Muhammadu Buhari,
a baya taken da yake kamfen
da shi shi ne, ‘jiki magayi,
jiki magayi, jiki magayi,’ a
lokacin ko da yake wannan
kamfen din na jiki magayi,
ana sayar da misali taliyar
macaroni ne a kan Naira
tamanin, ana sayar da
Maggi, Manja da Man gyada
da kusan dukkanin kayan
masarufi ne da sauki da arha
ta yadda talaka zai iya saya.
Ana sayar da litar man fetur
ne a kan Naira tamanin da
bakwai zuwa Casa’in, ana
zuwa aikin hajji a kan Naira
dubu dari bakwai da hamsin,
masu zuwa aikin ibada a
Jerussalam suna zuwa a kan
farashin da bai taka kara ya
karya ba. a yau dukkanin
wadannan abubuwan sun
gagari talaka, ci ya gagari
talaka, tsaro ya gagari
talaka, zaman lafiya ya
gagari talaka. Saboda haka

idan har akwai wadanda za a
tambaya su dora gwamnatin
Buhari a bisa kan mizani, to
talakawan kasarnan ne. to
talakawan kasar nan kuma
sun yi magana a kan wannan
gwamnatin cewa ba sa
gamsuwa kuma ba su gamsu
da wannan gwamnatin ba.
Da yawa mutane
suna cewa, ko ba komai
wannan gwamnatin ta
sami nasara a kan abin
da ya shafi fannin tsaro,
me ke naka fahimtan
ga masu irin wannan
tunanin?
To yanzun misali, ka je
Birnin Gwari ka ce masu
wannan gwamnatin ta sami
nasara a kan tsaro? Ka je
Zamfara ka ce masu an
sami nasara a kan tsaro?
Dazu-Dazun nan nake
gani a Talabijin, Sanatan
da ke wakiltar Zamfara ta
tsakiya, ya tsaya a tsakiyar
Majalisar Dattijai yana
cewa, an gaya ma gwamnati
cewa an shirya za a kai hari
kan wasu kauyuka, amma
har tsawon awanni ashirin
da hudu, gwamnatin ba ta
dauki wani mataki ba, ba
ta tura Jami’an tsaro ba, ba
ta yi komai ba, har sai da
‘yan ta’adda suka je suka
karkashe mutane.
Yanzun a ce a Zamfara,
Taraba, Benuwe, Birnin
Gwari, Borno, Kogi,
Nasarawa akwai tsaro?
Saboda haka wadanda suke
cewa akwai tsaron kila
an sami tsaro ne a wurin
su, a kauyan su, a garin
su. Amma mu cewa aka yi
mana a tarayyar Nijeriya,

idan har wani sashe na
Nijeriya ba zaman lafiya
yana mashasshara, kamata
ya yi dukkanin sauran
sassan kasar su ma su ji
mashassharan nan a jikin
su. A lokacin da PDP kenan,
Boko Haram guda daya ce,
mun kuma ci dunun ta har
ma mun kai ta bango, har
ma an yi zabe a Jihohin
Borno da Yobe. Amma sai
ga shi a wannan gwamnatin
har yanzun su na rike da
wasu yankuna na Nijeriya,
kamar yadda shi kan shi
Shugaban kasa ya ce an gaya
masa a hirar da ya yi da
muryar Amurka, don haka,
magana ta gaskiya na cewa
an sami tsaro, to a inda aka
sami tsaron kenan. Kuma
a lokacin da PDP ke mulki,
ai ba a wannan rigimar
a Zamfara, ba a rigima
a Birnin Gwari, ba a yi a
Benuwe, ba a yi a Nasarawa.
To idan har gwamnati an
yi rigima a zamanin ta shi
ne gazawar ta, to wannan
gwamnatin ta fi mu gazawa.
Abu na biyu da wannan

gwamnatin ke tutiyan
samun nasara a kansa shi
ne, yaki da cin hanci da
karban rasahawa, a nan
maki nawa za ka ba ta a
wannan fanin?
Ai zancen bayar da maki
ma bai taso ba, kullum ina
gaya wa ‘yan Nijeriya da
masu karanta Jaridar ku,
wa ya kafa EFCC? PDP ce,
wa ya kafa ICPC? PDP ce, wa
ya kafa dokar yin tsantseni
wajen bayar da kwangila?
PDP ce, wa ya kafa dokar
‘Whistle blower,’ ta in ka
ga ana yin wani abin da ba
daidai ba a ma’aikatar ku ka
fallasa ka tona asiri? PDP ce,
wa ya kafa dokar halastawa
‘Yan jarida su shiga kowane
Ofishin gwamnati su nemi
duk bayanin da suke nema
a kuma gaya masu tilas don
ku gano hakikanin abin
da ke tafiya ku shelantawa
duniya watau a turance,
‘Freedom Of Information
Act’? duk PDP ce. Saboda
haka ba wani da zai zo ya
yi wa PDP gorin yaki da cin
hanci da karban rashawa.
Mu din nan a mulkin
mu na PDP, mun kama
shugaban ‘yan sanda na
kasa bakidaya mun gurfanar
da shi har mun kai shi
kurkuku an daure shi, mun
kori Minista Stella Oduwa,
wacce aka zarge ta da
almunbazarranci, daga baya
ne aka wanke ta aka ce ba
ta da laifi, shi ne har ta zo
ta tsaya a zabe ta kuma ci, a
yanzun haka tana Majalisar
Dattawa. Saboda haka,
zance yaki da cin hanci da
rashawa, kokawan da muke
yi shi ne, a yau idan kai ne
fa, to a gobe ba kai ne ba,
mu da muka yi namu ba nu
na kin jini ga ‘yan adawa
mun rika kama su muna
daurewa yadda muka ga
dama ba, mu na wahalar da
su mu na azabtar da su ba.
Amma yanzun duk wanda
za ka ji ana tuhuma dan
PDP ne, duk wanda za ka ji
ana neman a ci ma mutunci
a ce ya yi sata dan PDP ne,
bayan kuma akwai ‘yan PDP
din da muka yi siyasan da su
ake kuma zargin su da irin
wannan abin, amma ba ka
taba jin an kai su EFCC ko
an gayyace su a kotu ko wani
abu mai kama da hakan ba.
Saboda haka, zancen yaki
da cin hanci da rasahawa da
wannan gwamnatin ke yi
karya ne, karya ne, na fada,
kuma matsayin Jam’iyyar
PDP shi ne, ba yaki suke yi
da cin hanci da rashawa ba,
yaki suke yi da ‘yan adawa,
don sun san ba su yi wa
talaka komai ba, da hakan
suke ganin in ba karya ‘yan
adawan suka yi ba, ba za su
iya fitowa su sake cin zabe
ba.
Akwai wasu misalai
ne da za ka ba ni kila na
ayyukan da kake ganin
Jam’iyyar ku ta PDP
ta yi wanda wannan
gwamnatin ta APC ba ta
yi kamar su ba?
To ai ba wani abin da
wannan gwamnatin ta yi,
yanzun misali dubi hanyar
nan Kaduna zuwa Kano,
wacce na fito kanta a yanzun
haka, yadda ta lalace, daga
Abuja din ma zuwa Kaduna
dubi yadda hanyar ta lalace.
Saboda haka, me PDP za ta
ji ma kunya kan mulkin ta?
Idan zan tsaya lissafa maka
ayyukan da PDP ta yi za ka
rike baki, mu fara daga kan
makarantun allo da aka
kafa guda 150, a nahiyar
Arewacin kasarnan, dubi
layin dogon da muka gina
muka zuba Jiragen kasa na
zamani a kan su misali daga
Abuja zuwa Kaduna.

Idan kuma zan tsaya
ne yi maka bayanin manya
kuma mahimman ayyukan
da muka yi, wadanda komai
adawan mutum bai isa ya ce
ba a yi wadannan ayyukan
ba, hanyoyi da aka gina da
asibitocin da aka gina, ni
din nan sai na kwana ina
yi maka bayanin su. Misali,
PDP ce ta kafa Jami’o’i guda
12 a kasar nan, akwai su
a Katsina, Yobe, Taraba,
Jigawa da sauran su, duk su
na nan, Jami’o’i ne 12 da ba
mai musawa, kuma a yanzun
haka dalibai ne cike a cikin
su suna daukan karatu. In
kuwa zancen hanyoyi ne,
mun gina hanyoyi masu
yawa, akwai hanyar da
muka bayar daga Maiduguri
zuwa Kano, duk ga su nan
sai inda lissafin ka ya tsaya
a duk sassan kasarnan. Mu
muka gina babban filin wasa
na kasa, mu muka gudanar
da zaben gaskiya sau hudu
a jere a kasarnan wanda
ba wata gwamnatin da ta
taba yin hakan. Mu muka
gina Cibiyoyin kamfanin
mai na kasa, NNPC (Mega
Stations), a kowace Jiha
ta kasarnan, don haka idan
ana zancen aiki ne, tabbas
PDP ba ta da wani gorin da
za a yi mata.
Sannan kuma a lokacin
mu abinci yana samuwa ga
talakan kasar nan cikin sauki
da arha, mutane kuma su na
yin aiki su sami kudi, ba mu
kuma rage darajar Naira ba,
amma a yau Naira ta zama
karmami, dala guda, tana
kan Naira 360, wanda ba a
taba shiga cikin irin wannan
halin ba, ‘yan kasuwa su na
kokawa masu saye ma na
kokawa. Saboda haka, har ta
kai talaka ne ke cewa, ‘gara
bara, ya bana.’
A Kadunan nan namu
ne aka ce an yi zabe, wanda
duk da murdiyan da aka
yi da kama karya da sayan
akwatinan zabe da sayan
kuri’u, amma duk da haka sai
da mutane suka fita suka zabi
PDP ta yadda har ta cinye
kusan ko’ina, amma suka
murda suka juya, suka nu
na rashin kunya, suka nu na
rashin mutunci. Saboda sun
san in sun fito da sakamakon
zaben na gaskiya, tabbas
sun ji kunya, za su ji kunya
a duniya za su ji kunya a
Nijeriya. To abin da muke
gaya wa al’ummar Jihar
Kaduna da suka nu na sun
gaji da wannan ballagazar
gwamnatin ta Kaduna,
sun gaji da masifar koran
ma’aikata, da cin mutuncin
Sarakuna, da wulakanta

mutane da ake yi a Kaduna,
ku hanzarta yin rajista ku
gyara kuri’un ku, kasa da
shekara guda yanzun ya rage
masu, wannan abin da ku
ka yi wanda duk Nijeriya ta
gani duniya ma ta gani, kun
baiwa APC wa’adi ne, kun
baiwa gwamnatin Kaduna ne
wa’adi, kun baiwa gwamnatin
Nijeriya ne wa’adi, cewa a
badi in Allah Ya kaimu, za a
kasa, za a tsare, za a raka, za
kuma mu tabbatar da cewa
duk wanda ya taba mana
mun kare hakkin mu.
Wane albishir kake da
shi na fatan da kuke yi
na dawowar Jam’iyyar
ku ta PDP kan karagar
mulkin kasar nan a 2019,
musamman dangane da
mawuyacin halin da ake
ciki a yanzun?
To na daya dai a namu
tsarin, duk dan takarar da
Jam’iyyar PDP ta tsayar, shi
da jama’a ne za su yi alkawari
a tsakanin su. Ka ga dai babu
yadda za a ce ana sayan litar
mai guda kan Naira 145
sannan kuma wai gwamnati
tana biyan sassaucin Naira
triliyon daya da bilyan 400,
wannan zalunci ne, babu
yadda za a yi a ce an kara
kudaden makaranta da na
kula da lafiya da ma kusan
komai da komai, bayan kuma
an ciwo mana bashin sama
da triliyon 11 wanda ba mu
ga abin da aka yi mana da
kudin ba.
Saboda haka dan takarar
mu, zai rubuta manufofin
sa da yadda zai gudanar
da ayyukan sa, zai kuma
zagaya ya shaida wa ‘yan
Nijeriya. Ina tabbatar wa da

‘yan Nijeriya cewa a lokacin
mu, da izinin Allah, abinci
da sauran dukkanin kayan
masarufi na yau da kullum
za su yi arha, za kuma a
samu cikakken zaman lafiya,
saboda a yanzun mun gano
ko da a wancan karon, ‘yan
adawa ne suka rika assasa
rigimar ta’addanci na Boko
Haram, wacce har yanzun
kuma ta zo su ma ta gagare
su. To idan mun zo, idan
sasantawan ne za a yi, za
a yin, idan ma kuma yakin
ne za a yi, to za a yi. Amma
dai in Allah Ya so Jam’iyyar
PDP babban abin da za ta
mayar da hankali a kansa
shi ne saukaka matsin da
talaka yake ciki, da kuma
kawo dawwamammen
zaman lafiya. Wannan
abin a Zamfara, Birnin
Gwari, Zamfara, Nasarawa,
Benuwe, Taraba, Borno, Kogi
da sauran dukkanin sassan
da a yanzun ba zaman lafiya,
in Allah Ya so za mu shirya
kammalallen shiri wanda zai
samar da zaman lafiya a cikin
dan kankanin lokaci.
Za a shigo da kayan abinci
domin a yanzun yunwa ake
yi, kowa kuma ya shaida
hakan a jikin sa, yanzun
yunwa ake yi, mutane ba sa
samun cin abinci, yara ba sa
samun cin abinci, mutane su
na cikin bala’i, ka wayi gari
da iyalanka ba ka da abin
da za ka ba su, matarka ba
ta da lafiya, amma sai ido
don ba ka da abin da za ka
iya yi mata, wannan duk
zalunci ne a gwamnatin da
ke ikirarin wai ita mai adalci
ce, in Allah Ya so duk PDP za
ta gyara wannan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: