Umar A Hunkuyi" />

Talakawan Nijeriya Na Cikin Mawuyacin Hali – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci shugabannin Nijeriya da su kara kaimi domin fitar da kasar nan daga cikin mawuyacin halin da take a cikin sa, yana mai cewa, Talakawan kasar nan suna cikin mawuyacin hali.

A shekaranjiya ne ya yi wannan maganar wajen taro na 45 na Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, a Zariya, Jihar Kaduna.

Ya ce, “Mun taru a nan ne domin mu yi wa Sarkin addu’a na samun kyakkyawan karshe da kuma samun lada a wajen Allah a bisa kyakkyawan shugabancin da yake yi wa al’ummar sa da ma kasa baki-daya. Don haka muna yin godiya ga Malaman mu da suke tunatar da mu umurnin Allah na mayar da komai a wajen Allah a kowane irin yanayi na kunci. Muna jin dadi da irin wadannan tunatarwan.

“Muna yin kira ga shugabannin mu da su rika tausaya wa talakawa. Kowa ya san muna cikin mawuyacin hali ne. babu kuma wani abu da ya fi karfin Allah. Namu dais hi ne mu ci gaba da yin addu’o’i, mu kuma yi wa shugabannin mu addu’a. al’ummar Masarautar Zazzau, ya kamata ku kara kaimi wajen yi wa Shugaban kasa da Gwamnan Jihar Kaduna da sauran shugabanni a dukkanin matakai addu’a. bai kamata ku kyale mu da halayen mu ba, muna da bukatar addu’o’in ku domin samun nasara.

Sarkin na Musulmi yana nuna irin damuwar sa ne a kan halin tabarbarewar harkokin tsaro a cikin kasar nan. a ranar Alhamis, wajen taron matsalar harkar tsaro a arewa, da aka yi a Kaduna, ya zargi shugabannin na arewa a kan rashin yin abin da ya dace domin magance matsalolin tsaro din a yankin na arewa, wanda hakan ne ya kai ga kafa rundunar sa kai mai suna, Shege-Ka-Fasa.

Ya zargi shugabannin da cewa ba su yi jagoranci nagari ba, wanda wannan shi ya kai ga kafa rundunar ta Shege-Ka-Fasa, inda ya nemi shugabannin na arewa da su hada kai da kowa a bisa kokarin da suke yin a shawo kan matsalolin tsaro din a yankin na arewa da ma kasa baki daya.

Hakanan a ranar Juma’a, Sultan din ya zargi shugabannin musamman Sarakunan gargajiya da Malaman Addini, a bisa gazawar su wajen bayar da shugabanci nagari, cikin jawabin sa a wajen wani taro sasantawa da yafewa juna a Jos ta Jihar Filato.

Exit mobile version