Gwamnatin tarayya ta ɗauki ɗamarar kawar da talauci a tsakanin ‘yan Nijeriya nan da shekaru biyar wanda ya ninku fiye da sau biyu tun bayan da gwamnati mai ci ta ɓullo da tsare-tsaren da suka jefa mutane da dama cikin halin ƙuncin rayuwa.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen buɗe taron tattalin arzikin Nijeriya karo na 31 mai taken #NES31 a Abuja.
- TRCN Ta Koka Kan Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya
- Uba Sani Ya Amince Da Biyan Naira Biliyan ₦2.3 Ga Tsofaffin Ma’aikata Da Iyalansu
Bagudu ya ce gwamnatin na da ƙwarin gwiwar cewa nan da shekarar 2030, za a kawar da talauci da rage raɗaɗin talauci zuwa mafi ƙasa.
A cewar Bankin Duniya, talauci a tsakanin mazauna karkarar Nijeriya ya kai kashi 75.5 cikin dari, wanda ke nuna ƙaruwar rashin daidaito da kuma tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar.
Ministan ya ce, gwamnati ta kuma kuduri aniyar inganta hasashen tattalin arziki da inganta sauye-sauyen da zai sanya Nijeriya ta samu ci gaba mai ɗorewa.
Bagudu ya jaddada cewa, gwamnatin da shugaban kasa Bola Tinubu ke jagoranta tana ba da fifiko wajen samar da ayyukan yi ta fuskar fasahar zamani, noma, tattalin arziki da ƙirƙire-ƙirƙire.