Idan kina tunanin kasancewar ki babbar ya wani aiki ne mai wahala, ki yi tunanin wannan yarinyar mai shekaru 22 da aka bayyana da suna Le Le wacce kotu ta umurce ta da ta kula da kaninta dan shekara 2, saboda iyayensu ba za su iya daukan nauyin su ba.
Kafofin sada zumunta na kasar Sin sun cika da mamaki a lokacin da labarin ya bayyana cewa, wasu ma’aurata sun kai diyarsu kotu don tilastata kulawa da dan uwanta domin ba za su iya ba.
An ruwaito cewa, wasu ma’aurata wadanda suka yi shekaru da yawa suna rayuwa kan alawus din ‘yarsu sai kuma suka yanke shawarar samun da na biyu. Lokacin da suka fahimci cewa ba za su iya biyan kudin dawainiyar sabon yaron ba, sai suka nemi ‘yar ta su ‘yar shekara 22 da ta goya yaron a madadinsu.
Le Le ta ki yarda da maganar iyayenta, domin ta ce ita ce ta tallafawa kanta a kwaleji kuma tana da burin gina wa kanta rayuwa, lokacin da ta samu labarin daukin nauyi dan uwanta daga iyayenta. Abin sha’awa shine, ta rasa karar a yayin da kotu ta umurce ta da sake daukar nauyin yaron.
Labarin ya haifar da takaddama a yanar gizo tare da mutane sama da miliyan 74 da ke ba da amsa a dandalin ‘Weibo’ na kasar Sin. Da yawa suna ganin hukuncin bai dace da yarinyar ba kuma ya kamata iyaye su kiyaye haihuwar da na biyu alhalin ba za su iya daukar nauyin kula da shi ba.
A cewar kafar labarai ta ‘China Eggz 2’, tun lokacin da kasar Sin ta soke dokar haihuwar tara sama da, ma’aurata da yawa suna da ‘ya’ya da yawa ba tare da yin la’akari da nauyi na kula da su ba.