Bello Hamza" />

Taliban Ta Gana Da Manzon Musamman Na Amurka

Kungiyar Taliban ta tabbatar da bayanan da ke cewa wakilanta sun gana da manzon Amurka Zalmay Khalilzad a kasar Katar inda suka tattauna dangane da yadda za a warware rikicin Afghanistan.

Babbar manufa dangane da wannan ganawa da bangarorin biyu da ke hamayya da juna suka yi ita ce samar da kusance a tsakanin jami’an kungiyar ta Taliban, gwamnatin Afghanistan, Pakistan, Amurka da kuma Saudiyya, inda da ke karshen ake fatan gamsar da kungiyar domin shiga tattaunawar zaman lafiya.

Kamar yadda mai magana da yawun Taliban Zabuhullah Mujahid ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a wannan asabar, an yi ganawar ce jiya juma’a a birnin Doha na kasar Katar.

Exit mobile version