Tallafa Wa Manoma Mu Ka Sa A Gaba -Akongs Dankande

Tun daga lokacin da gwamnatin tarayya a karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa gaba na ganin ta bunkasa noman shinkafa a daukacin jihohin Nijeriya hard a Abuja, wasu kungiyoyin da aka kafa su, domin ciyar da noma gaba, suka tashi tsaye, dominganin manoma a Mijeriya, sun fita daga mtsalolin da suke fuskanta,ta yadda gwamnatin tarayya  za sami nasara a shirin da akasa wa gaba, da ya shafi bunkasa noman shinkasa a Nijeriya baki daya.

Wakilinmu BALARABE ABDULLAHI, ya sami dammar zantawa da babban jami’in kamfanin BAYER ,MSTA  AKONGSDANKANDE inda ya bayyna wa wakilinmu dalla-dalla na yadda suke tallafa wa manoma da sauran hanhoyi ma su.

Ga yadda yadda hirarsu  ta kasance da wakilnmu:

Wannan cibiyar a ina mustuguninta ya ke?

Babu shakka babban ofishinmu ya na kasar Jamus.

 

Wasu abubuwa ku ke tallafa wa manoma da su?

Abubuwan da mu ke tallafa wa manoma da su sun hada da maganin feshi da iraruwan shukawa ma su inganci da in manomi ya yi amfani da su bisa tsarin da mu ka bayyana ma sa zai sami amfanin gona fiye da Laba goma sha hudu, wato buhuna 140.

 

Mene ne dalilin shigowarku nan Nijeriya?

Da farko mun shigo Nijeriya ne saboda mun lura gwamnatin Nijeriya a karkashin Muhammadu Buhari, da gasket a ke yin a bunkasa bangaren noma, musamman in an lura da matakan da gwamnatin na ke dauka, sai mu ka lura tan a bukatar cibiyoyi irin na mu, da zai tallafa wa manoman Nijeriya da sabbin dabarun nomad a kuma kayayyakin noma na zamani da manoma za su amfana da noman da suke yi.

Kuma mun lura a duk kasashen Afirika, babu kasar da ke da manoma kamar Nijeriya, amma manoman na fuskantar matsalolin rashin amfana da noman da suke yi,a dalilin haka ne mu ka sami izinin gwamnatin Nijeriya, mu ka shigo da nufin ganin mun tallafa wa manoman wannan kasa na birane da kuma na karkara da a can ne ake noma.

 

Kun fahimci ainihin matsalolin da suke addabar manoman Nijeriya? 

Lallai mun fahimci wasu daga cikin matsalolin, kuma matsalolin na bayyana ma ku a baya, amma a kwai matsalar nau’o’in takin zamani da suke amfani da su a gomakinsu da rashin yin binciken nau’in kasa kafin asa taki da kuma rashin binsu sau da kafa daga fara noman da suke yi, zuwa kammala nomamsu, wadannan nan kadan ne cikin matsalolin da suke addabar manoman Nijeriya, wanda tun a shekarun baya mun warware ire-iren wadannan matsaloli a wasu kasashe na duniya.Watokamar yadda manomin da ken a noma shinkafa a Indiya ke samun buhu 140 a Hekta daya, haka mu ke son manomi a Nijeriya shi ma ya amfana a cikin sauki.

 

Wasu matakai ku ke bi na ganin kun sami manoman da suke karkara, ta yadda za su amfana da tsare-tsaren ku?

Babbar hanyar da mu ke bi shi ne saduwa da kungiyoyin manoma da su ke da alaka ta kai tsaye da daukacin manoma ako wace jiha,misali ka ga a yau ai kungiyar manoman shinkafa mu ka ziyarta, mun zauna da su, sun fahimce mun kuma fahimci wasu matsaloli dab a mu sani ba kafin mu zauna da su.

 

Zuwa yanzu a Nijeriya wasu jihohi ku ke da niyyar tallafa wa manoma a karkashin wannan cibiya ta ku?

Zuwa yanzu mu na jihohin da suka hada da Kano da Jigawa da Kaduna da Nasarawa da kuma jihar Neja,wadannan jihohi su ne na farko da mu ka fara da su, nan kuma za mu shiga wasu jihohi in Allah ya yadda.

 

Wau abubuwa za ku fi mayar da hankalinku, na ganin kun tallafa wa manoma a Nijeriya?

Abubuwan da za mu fi sa wa a gabanmu, shi ne ganin mu na amfani tare da alaka da kungiyoyin manoma kai tsaye, bisa yaddar gwamnatocin jihohin   da mu ka shiga, tu ni mun fahimci ba za mu iya yin amfani ko mu’amala da manoma kaintsaye ba, shi ya sa mu ka fi mayar da hankalinmu da alaka da kungiyoyin manoma da suke shuka daban-daban.

 

Ka’dojin da ake sa wa da nufin tallafa wa manoma, na kawo cikas ga mafiya yawan manoma, me ya banbanta ka’idojinku da sauran ka’idoji da ake sa wa manoma kafin a ba tallafi ko kuma dangwale?

Ai tuni mu ka duba wannan matsala,kuma tun da na ce ma ka da kungiyoyin manoma mu ke alaka, ai ko ka’idojinmu da sauki kwarai da gaske ba su yi kama da sauran cibiyo ma su kama da namu basu.

 

Baya ga Nijeriya, a Afirika, wasu kasashe  ku ka shiga domin tallafa wa manoma?

Lallai mun shiga kasashe da yawa baya ga Nijeriya, mun shiga kashen da suka hada da Kamaru da Nijeriya da Abidjan Mali da Senigal. A duniya kuma mu na hulda da kasashe 150, kuma duk manoman da suke wadannan kasashe suna hulda da mu a yau.

 

A cikin kasashen da ka bayyana ma na, wace kasa ce aka fi karbarku da hannu biyu?

Ka ga kamar kasar Abidjan an karbe mu da hannu biyu, shi ya sa mu ka bude babbar ofishinmu na Afirika a wannan kasa, kuma sun ci gaba fiye da bayan d azan yi ma ka,haka Mali da Bokina-Faso zance Auduga da sauran noma sun sami ci gaba, a dalilin tallafi da kuma shawarwarin da mu ke ba su.

 

In har manoman Nijeriya  suka rungume ku da hannu biyu, wani tunani ka ke yi wa bangaren noma a Nijeriya a shekaru ma su zuwa a nan gaba?

Ai babbar maganar ita ce, a Nijeriya an sami shugaban kasar da ke da niyyar bunkasa noma, ga kuma manoma ma su basira tare da kasa mai inganci, babu ko shakka a ‘yan shekaru ma su zuwa Manoman Nijeriya za su bunkasa moma a wannan kasa,wanda zai haifar da yalwataccen abinci A daukacin al’ummar da suke Nijeriya.

 

Exit mobile version