Muhammad Awwal Umar" />

Tallafin CBN: Simple Link Network Na Yunkurin Dawo Da Martabar Noman Alkama A Neja

Tallafin CBN

A yunkurin gwamnatin tarayya na dawo da martabar noman alkama a kasar nan, ta hanyar shirin tallafin CBN ga manoma, Simple Link Network Egency ta himmantu wajen raba fom ga manoman alkama a Neja domin samun saukin ba da tallafin ga manoma.

Shugaban Simple Link Network a Neja, Ambasada (Dr) Nura Hashim ya bayyana ma wakilin mu cewar jihar Neja na daya daga cikin jahohin da ke noman alkama a kasar nan, amma sakacin da gwamnatocin baya su ka yi na rashin karfafa guiwar manoman yasa noman alkama ya ja baya, amma zuwan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na dawo da martabar noma a kasar nan, yasa shirin ba da tallafin noma ga manoma ya koma hannun babban bankin Najeriya ( CBN) dan samun isar da tallafin a hannun wadanda su ka da ce.
Yanzu haka Simple Link Network ta fara raba fom kyauta ga manoman dan samun cikakken bayanan su, ta yadda za mu saukin raba kayayyakin da ake nufin baiwa manoman a karkashin kungiyar manoman alkama ta jiha. Ba mu ware ba, dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar nan lungu da sako za mu tabbatar sun anfana da shirin.
Babban burin mu dawo da martabar noman alkama a jihar nan, wanda ita kanta gwamnatin jiha ta tabbatar mana cewar a shekara mai zuwa za ta samar da hekta dubu daya dan noman alkama, wanda ina da tabbacin cewar wannan kudurin zai samar da gurabun ayyuka da dama a gida da wajen kasar nan.
Kamar yadda muke fata muna sa ran daga watan Nuwambar nan mai kamawa bayan mun tantance manoman za mu samar da lokaci dan horar da su ta yadda za su samu saukin noman yadda ya dace, a yunkurin mu mun tsara cewar ita bankin CBN ce za ta samar da ‘yan kasuwa ko kamfanonin da za su yi alkaman a hannun manoma idan an noma ta yadda za a saukakawa manomi saukin shigar da ita kasuwa ba tare da sun fada hannun macutan ‘yan kasuwa ba, ita kanta CBN ta samu saukin mayar da kudaden da ta fitar dan ba da tallafin.
Saboda haka kofa a bude ta ke ga dukkan manoman da ke sha’awar noman alkama a jihar nan, har yanzu muna cigaba da rabar da fom domin muna da jami’ai a dukkan sassan jihar nan. Kamar yadda na fadi a baya ba wata kungiyar da muka amince ta karbi kudin fom a hannun kowani manomi, sannu a hankali za mu cigaba da wayar da kan manoma dan samun anfanin wannan tallafin. Inji shi.

Exit mobile version