Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da biyan Naira Miliyon 209,596,633.00 a matsayin bashin kudin karatu da Kuma na harkokin
yau da kullum na da ke karatu a Jami’ar Manzoura. Kamar yadda babban Daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Kano Abba Anwar ya shaidawa Jaridar
Leadership a Yau Lahadi
Haka Kuma Gwamnan ya amince da fitar da Naira Miliyon 48,220,002.00 a matsayin kudin makaranta da harkokin yau da kullum na dalibai shida dake
karatu a Masar. ” Inda jimmalar kudin Jami’o’in ya kama Naira Miliyon 257,812,635.00.
Sanarwar ta ci gaba da cewar an fitar da kudaden ne domin sakakawa dalibai halin da suka tsinci kai aciki alokacin annobar Korona. Yace, Gwamna
Ganduje ya kuma jaddada aniyar Gwamnatinsa na sake duba tallafin karatun daliban.
Idan za’a iya tunawa daliban Jami’ar Manzoura sun rubuta takardar neman gafarar Gwamna Ganduje bayan da aka cire su daga cikin wadanda Gwamnatin
Kano ke daukar nauyin karatun nasu a ahekarar data gabata sakamakon wata rashin fahimta data faru tsakanin Hukumar Makarantar da Gwamnatin Jihar
Kano.
A cikin wasikar, an bayyana cewa ” dalibai 37 ne ke karatu a Jami’ar Manzoura, wadanda aka kora tun da farko sakamakon Rashin gahimtar data faru
tsakanin Hukumar Jami’ar da Kuma bangaren Gwamnati. Wanda kuma wannan rashin fahimta mai yawan gaske ta jaza tada jijiyar wuya wanda hakan ne
yasa Gwamnati dawo da mu gida. Inji daliban.