Connect with us

LABARAI

Tallafin Korona: Kungiyar ‘Yan Kasuwa Ta Shiyar Funtuwa Ta Yaba Wa Sanata Mandiya

Published

on

Kungiyar gamayyar ‘yan kasuwa ta yankin Funtuwa kanana hukumimi 11 sun yabawa Sanata Alhaji Bello Mandiya a bisa kokarinsa na tallafa wa ‘yan kasuwa a yankin.

Wannan yabon ya fito ne daga bakin shuwagabannin kungiyar, a lokacin da suka kira taron ‘yan jarida a ofishin kungiyar dake Funtuwa a jihar katsina, Shugaban kungiyar na Funtuawa zone Alhaji Ibrahim Sulaiman Sheme ya ce, kiran taron ya zama wajibi agare su ganin yadda Sanatan yankinsu ya yi namjin kokari wajen samar wa kungiyarsu bashin da Gwamnatin tarayya ta samar na rage radadin Cutar korana  ya ce, babu shakka wannan cutar da ta addabi duniya har da Nijeriya ta gurgunta mafi yawanchin ‘yan kasuwar su saboda rufe wadansu kasuwanni da akayi wannan ya jefa mafiyawancin ‘yan kasuwarmu  rasa jali da durkushewar kasuwanci, wannan dalilin ne gwamnatin tarayya ta samar da wannan bashi domin rage radadin. Alhaji Dan Sulaiman ya ce, basu taba samun Sanata kamar Alhaji Bello Mandiya ba domin kokarinsa ne ya samar ka yayan kungiyarsu har mutum 58 bashin kudi na kimanin Naira 500,000  ga kowanne dan kasuwa don inganta kasuwancin su, sun gode kuma ya ce, suna tare dashi duk inda ya nufa a siyasa kuma.

A lokacin da yake tofa albarkacinsa mataimakin Shugaban kungiyar ta jihar Katsina Alhaji Musa Shugaba Funtuwa ya yaba wa Sanatan bisa kokarinsa na taimakon ‘yan Kasuwar, Alhaji Musa Shugaba ya ce, Sanatan da ya samo masu bashin sai ya nemi kungiyarsu don tallaba masu ya ce, bashi ne ‘yan Kasuwa a kace a ba don basu rancen kudin a lokacin da Sanatan ya kira ga Shuwagannin yan Kasuwar ya gaya masu cewar zai ci gaba da taimakon ‘yan Kasuwar mazabarsa dama jihar Katsina baki daya zai ci gaba da kawo ribar demokaradiyya a yankin. Alhaji Musa Shugaba ya ce, su ‘yan kasuwa , suna tare da Sanata ganin yadda yake kaunar ‘yan kasuwar yankin babu wani Sanata da ya ke yin abinda Bello Mandiya ke yi don haka suna yi mashi fatan alheri da godiya wajen irin kokarinsa na ciyar da yankin su gaba wajen kawo manyan ayyuka yace an bar yankin Funtuwa a baya wajen rashin samun wata babbar Makaranta kamar irinsu (Polytechnic, da Unibersity) amma daga zaben Alhaji Bello Mandiya a Sanata kowa ya san irin kokarin da ya yi na kawo Jami’ar aikin gona a Funtuwa wannan abun a yaba ne kuma sun gode Allah ya kara maimaita mashi kujerar shi ta Sanata a shekarar 2023 kuma suna tare da shi da kuma dukkan kungiyar ‘yan Kasuwar na kananan hukumomi 11.

A nashi jawabin Shugaban yan Kasuwa na karamar hukumar Malumfashi Alhaji Muntari Bube Malumfashi ya ce, yasan Sanata  tun yana karami domin unguwarsu daya a Gangarawa Malaumfashi, Mutumin kirki ne mai son taimakon jama’a mai cika alkawari ya ce, ya taba fitowa takarar dan majalisar wakilai a mazabar Kafur da Malumfashi a wancan lokacin amma bai samu ba ashe amfanin da zai yi masu bana kananan hukumomi biyu bane zai taimaki kananan hukumomi 11 babu shakka zaben Alhaji Alhaji Bello Mandiya a Sanata abin jin dadi ne kuma shi mutum ne ba kamar sauran ‘yan siyasa ba  domin bai son gulma ko zagin wani abinda yasani ya zai yi ya taimaki al’umma.

Alhaji Muntari Bube ya ce, zuwan shi majalisa a matsayin Sanata ya samar ma yara aiki a gwamnatin tarayya kamar aikin Dan sanda da cibil difes, da Soja da dai sauran aiyuka, da taimakon Marayu da matasa da zarar anyi rasuwa zai je ta’aziyya kuma ya bada abinci domin taimakon Marayun da aka rasu a ka bari don haka suna godiya kwarai agareshi  akan yadda yake taimako a koda yaushe kuma zaiga sakayya insha Allahu.

Shugaban ‘yan Kasuwa na karamar hukumar Funtuwa Alhaji Sule Garba shima ya yabama Sanata Alhaji Bello Mandiya wajen taimakon da ya keyi a koda yaushe da yadda ya taimaki ‘yan kasuwa su  58 da bashin Korona 19 na Naira kusan 500,000 yace suna mika godiya ga gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Massari shima yaba kungiyar ‘yan Kasuwa ta jiha da takardun cikewa na bada bashi har guda 1000 kuma ya inganta Kasuwar Funtuwa hade da tashar mota ya maida su na zamani ga taimakon ‘yan kasuwa a koda yaushe da Maigirma Gwamnan keyi lalle ya zama gwamnan ‘yan Kasuwa, don haka suna mika godiyarsu agaresu wajen kokarinsu na taimakon ‘yan kasuwa Alhaji Sule Garba yayi kira ga sauran Gwamnoni da Sanatoci su yi koyi da wadannan mutane guda biyu gwamna Masari da Sanata Mandiya don haka su ‘yan Kasuwa suna tare da su kuma duk abinda suka tsaya a shekarar 2023 suna tare dasu kuma suna kara godiya wajen yadda suke taimakon ‘yan kasuwa da sauran al’umma na yankin Funtuwa da jiha baki daya.

 
Advertisement

labarai