Tallafin mai na lakume naira biliyan 11.20 a duk mako daya bisa yadda farashin mai ke kara tashi sama. Tun daga ranar 5 ga watan ne lokacin da gangan danyan mai ya kai dala 60, ake tsammanin farashin litar mai daya ta kai naira 200, bisa yadda hukumar kayyade farashin mai take kayyade farashin man ta yadda kasuwa ta kaya.
A halin yanzu dai, ana sayar da mai a tsakanin naira 160 zuwa naira 165 a kowacce litar mai a garin Legas. Ana tsammanin farashin mai a halin yanzu ya kamata ya kai naira 190 ga kowacce lita, amma ana sayar da shi kan naira 162 wanda ya nuna cewa ana bayar da tallafin naira 28 ga kowacce lita. Idan aka kwatanta ga man da ake amfani da shi a kowacce rana na lita miliyan 57 wanda kowani lita akwai tallafin naira 28, wannan na nufin a tallafnin mai yana cinye naira 1.60 a kowacce rana, yayin da yake lakume naira biliyan 11.20 a mako a tsakanin ranar 5 zuwa 12 ga watan Fabrairu.
A cikin makon da ta gabata ce, aka fitar da rahoton cewa kowani lita ana kashe masa naira 179.67 fiye da naira 158.53 wanda ake kashewa a baya, wanda ake tsammanin karuwar zuwa naira 202.67 a kan kowacce lita daya daga naira 181.53 na kowacce lita a baya. A shekarar da ta gabata ce, gwamnatin tarayya ta fara kayyade farashin mai ta yanayin yadda kasuwan gangan danyan mai ta kama a duniya. Inda ya yanzu gangan danyan mai yana ci gaba da hauhawa wanda dole shi ma a sami karuwar farashin mai. A yanzu dai, ana sayar da gangan danyan mai a kan dala 543.25, kwatankwacin naira 157.99 idan aka canza kowacce dala a kan naira 390. An dai samu karuwar dala 0.88 a kan kowacce lita, inda a ranar Litinin kowacce gangan danyan mai guda daya ta kama dala 63.31.
Kamfanin mai ta kasa (NNPC) wanda shi kadai ne ke shigo da mai a cikin kasar nan, amma duk da hakan ‘yan kasuwa suna ci gaba da kalu balantar hakan, inda suke nuna cewa duk da gyara bangaran da aka yi hakan bai canza zani ba.
A makon da ta gabata ce, karamin ministan mai, Cif Timipre Sylba ya bayyana cewa, ‘yan Nijeriya su shirya jin radadin karin farashin mai tun da dai ana samun karuwar danyan mai. A cewarsa, dole ne a samu karain farashin mai.
“Mun yi shirin tun karar kalubale a matsayinmu na ‘yan kasa. Daga yau, kamfanin NNPC ba za ta kara daukan wani tallafi ba. domin mun san cewa babu kudin tallafi daga cikin kasafin kudi. A ina za a sami kudin, saboda na tabbata kamfanin NNPC ba za ta ci gaba da gudanar da abubuwan da ta yi a baya sakamakon ba a shirya musu hakan ba. A matsayinmu na ‘yan kasa, dole ne mu shirya jin radadin karuwar farashin mai.”
A cikin rahoton kamfanin NNPC wanda yake fitarwa a wata ya bayyana cewa, karuwar rarraba man a fadin kasar nan ya kai jimillar lita biliyan 1.72, wanda a rana ana samun rarraba litar mai guda 57.44 a duk kulluma. Kamfanin ya bayyana cewa, zai ci gaba da saka ido a kan rarraba man a cikin fadin kasar nan.