Connect with us

LABARAI

Tambuwal Ya Bai Wa ’Yan Jarida Cikakken Hadin Kai A Sakkwato –Shuni

Published

on

Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Sakkwato, Kwamred Isa Abubakar Shuni ya bayyana cewar Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta baiwa ‘yan jarida cikakkiyar damar gudanar da aikinsu ba tare da kowane irin katsalandan ba.
Ya ce Tambuwal yana baiwa Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar hadin kai a kodayaushe domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Shuni ya bayyana hakan ne a jawabinsa na maraba a wajen Babban Taron masu ruwa da tsaki (NEC) na kungiyar na shekarar 2018 wanda aka gudanar a Sakkwato a karshen mako.
“Wannan shine karo na farko da ake gudanar da Babban Taron Majalisar Zartaswar Kungiya a Sakkwato don haka ya zama wajibi a yabawa Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal kan daukar nauyin bakuncin taron wanda ya shiga cikin kundin tarihi.” In ji Shuni.
Ya ce daga cikin alfanun da kungiyarsa ta samu a Gwamnatin Tambuwal akwai kammala aikin canza fasalin Cibiyar ‘Yan Jarida ta Jiha wanda Gwamnatin Aliyu Wamakko ta assasa da kuma daukar nauyin Makon ‘Yan Jarida wanda aka gudanar a wannan shekarar.
Shuni ya kuma bayyana gina masallacin salloli biyar a harabar cibiyar da daukar nauyin karatun manbobin kungiyar domin samun ilimin aikin jarida da kuma samar da filin wasar kwando ta Badminton da bohol domin samar da wadatattun ruwa a matsayin kadan daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu a karkashin jagorancinsa.
Fitaccen dan jaridar ya bayyana cewar akwai cikakken hadin kai da fahimtar juna a tsakanin manema labarai a Jihar Sakkwato wadanda ya ce suna aiki a matsayin ‘yan gida daya al’umma daya.
“Muna bukatar uwar kungiyar ta kasa da ta rika sanya manbobin mu a cikin shirin bayar da horo da sake bayar da horo da sauran ayyuka da shiraruwan kungiyar domin manbobin mu su kara samun kwarewa da gogewa a kai. “Ya bayyana.
A jawabinsa Shugaban Kungiyar na Kasa, Kwamred Abdulwaheed Odusile ya kalubalanci Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta daina bayar da uzuri kan kashe-kashen da ke faruwa a sassan kasa ta hanyar gurfanar da wadanda ke da alhaki domin su fuskanci hukunci domin kare Nijeriya da al’ummarta yana cewar tsaron lafiyar al’umma hakki ne da ya rataya kacokam a wuyan Gwamnati.
A taron Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya aminta da kukan da al’ummar Nijeriya ke yi kan bukatar canza Shugabannin Hukumomin Tsaro na kasar nan a bisa ga kasawar su wajen tsaron rayukan al’umma da dukiyoyin su.
Gwamnan ya kuma bukaci kafofin yada labarai da su kansu manema labarai da su daina amfani da damar da suke da ita wajen yada labaran kanzon kurege wadanda ke haddasa husuma da tashin-tashina a kasa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: