Tambuwal Ya Sa Hannu A Kasafin Kudin 2021

Hannu

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto

 

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato a daren jiya ya sa hannu a daftarin Kasafin Kudin 2021 na naira biliyan 176 a matsayin doka.

 

Da yake jawabi a wajen taron, Tambuwal ya yabawa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato kan kwazon da suka nuna na amincewa da Kasafin Kudin a matsayin doka.

 

Ya ce jajircewa da sadaukar da kai da ‘Yan Majalisar suka nuna wajen sauke nauyin aikin da ke kan su ga al’ummar Jihar Sakkwato ya nuna yadda suka hada dai wajen ciyar da jama’a gaba ba tare da bambamcin siyasa ba.

 

Gwamnan ya ce abin yabawa ne yadda masu shata dokokin suka kawar da bambamcin siyasa domin amfanin talaka duk da bambamcin siyasa da ke akwai amma suka sa aiki da ci-gaban jama’a sama da komai.

 

Tun da farko Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Hon. Aminu Muhammad Achida ya bayyana cewar sun aminta da Kasafin Kudin 2021 bayan bita da bin didddigi a cikin lokaci bayan Gwamnan ya gabatar da Kasafin Kudin.

 

Ya ce Majalisar ba ta yi kari ko ragi a kasafin na biliyan 176, 685 ba da bangaren Zartawar Gwamnati ya gabatar ba yana cewar Majalisar ta gamsu kwarai ainun da muhimman nasarorin da aka samu wajen aiwatar da Kasafin Kudin 2020.

 

Ya ce duk da kalubalen kudi da aka samu wajen aiwatar da ayyuka a Kasafin Kudin 2020, Gwamnatin Jiha ta samu gagarumar nasara a fannin ilimi, kiyon lafiya, raya karkara, samar da ruwan sha, shimfida hanyoyin mota da sauransu da dama.

Exit mobile version