Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Tambuwal Ya Taka Rawar Ganin Daga Darajar Sakkwato Da Nijeriya – MD Yusuf

by Muhammad
December 1, 2020
in RIGAR 'YANCI
3 min read
Sakkwato
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Musa Muhammad

 

samndaads

An bayyana Gwamnan Jihar Sakkwato, Hon. Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wani ginshiki a jagorancin siyasar Arewa da Nijeriya baki daya, musamman bisa la’akari da irin gudumuwar da ya bayar na ciyar da kasa gaba tun zamanin da ya ke matsayin Shugaban Majalisar wakilai har ya zuwa kasancewarsa Gwamna a Jihar Sakkwato.

Shugaban Kungiyar magoya bayan Tambuwal na Nijeriya, ‘Tambuwal Sabe Nageria’, Alhaji MD Yusuf ne ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.

“Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya shiga cikin jerin fitattun mutane, wadanda suka samu babbar lambar yabo na manyan gidajen Talabijin na Nijeriya a matsayin wadanda suka bada gudumuwa na ciyar jama’ar su gaba, inda ya zama zakaran gwajin dafi, kuma tauraro a tsakanin sauran Gwamnonin Jihohin kasar su 36″, in ji Yusuf.

MD Yusuf ya ci gaba da cewa ” a hawansa kujerar mulkin Jihar Sakkwato na shida, an fara fahimtar irin sauyin juyin-juya-halin da ya zo da shi ne, musamman a fannin Ilimi na Jihar, a lokacin da ya baiwa sashen Ilimi muhimmanci a cikin kasafin kudinsa”.

Kason da Gwamna Tambuwal ya ware wa fannin Ilimi na baya-bayan nan shi ne, Naira Bilyan 47, 880, 096, 366 .25, wanda hakan ke daidai da kashi 24% na jimillar kasafin kudin Jihar ta Sakkwato na Naira Bilyan 202, 444, 458, 429.02, tabbas wannan kyakkyawar shaida ce”.

MD Yusuf ya kara da cewa “duk domin dai kara karfafa wa sashen Ilimi, an kafa tare da kaddamar da wata gidauniyar bunkasa Ilimi ta musamman a karkashin shugabancin Mai Martaba, Sarkin Musulmi, Dakta Muhammadu Sa’ad Abubakar III. Wannan gidauniya wacce aka tabbatar da cewa ita ce irin ta ta farko a tarihin Jihar Sakkwato, ta bayar da damar bayar da gudumawar daidaiku ne domin bunkasa sashen na Ilimi”.

Yusuf ya ci gaba da bayyana cewa, namijin yunkurin da Gwamna Tambuwal ya fito da shi, a yanzun haka ya fara haifar da da mai ido. Daya daga cikin kyakkyawan sakamakon da yunkurin na Gwamnan ya fara samar wa, shi ne yadda a yanzun haka yaran da a baya sam ba sa zuwa makaranta, a yanzun haka sai tururuwa suke suna zuwa makarantun, kamar yanda Hukumar majalisar Dinkin Duniya ta UNICEF ta bayar da shaidar hakan.

Ya kara da cewa, Gwamna Tambuwal ya yi imani da cewa ba ta yadda za a sami nasarar bunkasa sha’anin Ilimi a Jihar ba tare da karfafan iyayen yaran da su nemi ilimi mai zurfi ba. A cikin hikimarsa, Hon. Aminu Waziri Tambuwal, sai ya fahimci wajibcin baiwa hukumar bayar da tallafin karatu ta Skolashif muhimmanci. Ya zuwa yanzun, tabbace yake a karkashin Gwamna Tambuwal an kashe tsabar Naira Bilyan 7.5 domin bayar da tallafin karatu a hanyoyin Skolashif din daban-daban.

MD Yusuf ya ci gaba da cewa, zayyana abubuwan ci gaba da Gwamnan ya yi, ba za su lissaftu ba a dan karamin lokaci, amma dai ya ce, “ba za a taba matawa da gina asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Sakkwato da kuma makarantar Sakandaren ilimin mata ta gwamnati a garin Kasarawa, wani yanki da ke wajen Sakkwato, ya sake sabunta harkokin kasuwanci a yankin”

Shugaban masoya Tambuwal din ya karkare da cewa, “bisa ga wadannan kyawawan nasarori da ya samu, da ma wadanda lokaci ba zai bari mu ambace su ba, ya sanya jama’ar Jihar Sakkwato da sauran ‘yan Nijeriya Maza da Mata ke kira gare shi da ya amince ya tsaya takarar shugabancin kasar nan a shekarar 2023 domin kai Nijeriya ga tudun-mun-tsira, wanda in har haka ta kasance, to muna da sauran kyakkyawar fata ke nan a kasar nan.

SendShareTweetShare
Previous Post

FOMWAN A Bauchi Ta Yi Shelar Karfafa Mata Domin Zama Kan Duga-dugansu

Next Post

Jam’iyyar APC A Kano Na Yunkurin Halaka Ni – Sha’aban Sharada

RelatedPosts

Ebonyi

Kwamishinan ’Yan Sandan Ebonyi Ya Kama Hadiman Gwamnan Jihar Biyu Da Shugaban Karamar Hukuma

by Muhammad
17 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Rundunar 'yan sanda ta kama wasu...

Direbobi

Bakwai Sun Mutu Da Yawa Sun Jikkata A Rikicin Shugabancin Kungiyar Direbobi

by Muhammad
17 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, A kalla mutane bakwai ne suka...

Takalmi

Mata Ta Rafka Wa Mijinta Tsinin Dunduniyar Takalmi Ya Mutu

by Muhammad
17 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Wata mata da ba a bayyana...

Next Post
Sharada

Jam’iyyar APC A Kano Na Yunkurin Halaka Ni – Sha’aban Sharada

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version