Tambuwal Ya Yi Alkawarin Sake Fasalin Kungiyoyin Sintiri A Jihar Sakkwato

Daga Bello Hamza,

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayyana cewa, gwamnatinsa za ta tabbatar da yi wa kungiyoyin sintiri na jihar garambawul da kuma sake musu fasali ta yadda za su bayar da tallafin da ya kamata ga hukumomin tsaro a fadin jihar.

Gwamna Tambuwal ya jaddada wannan alkwarin ne a sanarwar mai bashi shawara na musamman akan harkokin watsa labarai, Malam Muhammad Bello, ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a garin Gandi da ke karamar hukumar Rabah ranar Talata.

Idan za a iya tunawa ‘yan bindiga sun yi arangama da ‘yan sintiri inda aka mutum 21 suka mutu a karamar hukumar.

Gwamnan ya ce, yin garanbawul din ya zama dole don a sake fasalin yadda ‘yan sintirin suke gudanar da ayyukansu, musamman ganin irin abin da ya faru a karamar hukumar Rabah da ke Gabashin jihar.

Ya kuma nemi dukkan kungiyoyin ‘yan sintiri a jihar su bayar da hadin kan da ya kamata don samu wannan nasarar, ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasu sakamakon arangamar da aka yi da kuma fatan Allah ya kawo mana kashen matsalar a fadin kasar nan gaba daya.

Exit mobile version