Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RA'AYI

Tamkar Andalus, Tamkar Nijeriya (I)

by Tayo Adelaja
September 25, 2017
in RA'AYI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mohammed Ibraheem Zakzaky

Duk wani musulmi yana alfahari da tarihin irin tasirin nasarar magabatanmu na Al-Andalus. Musamman ma dai ni, ina jin lamarin Al-Andalus a cikin jini da bargo, wannan kuwa yana da nasabar kasancewa na Bamalle; saboda Kakannina sun fito ne daga wani yanki da aka fi sani da ‘Magrib’ Yamma. Yankin da a yanzu ya kumshi kasashe kamar, Maroko, Yammacin Sahara, Algeria, Mauritania da Spaniya. Kakannina sun fito ne daga mashahurin garin Chinguetti, inda suka yi tawaga zuwa wurin Sheikh Usman Danfodio, daga inda kuma kakana ya yiwa Malam Musa (ma-rikin tutar Shehu) rakiya zuwa garin Zariya, garin da aka haife ni. Don haka wannan yanayi da muka tsinci kanmu a ciki, sai na ke ji tamkar wani abu ne da ya taba samuwa, kai ka ce wancan zamanin ne na ainihin Al-Andalus, ta hanyar take hakkokinmu da neman hana mana rayuwa kamar sauran mutane. Wannan kaddara tamu, ta yi kamanceceniya da irin wahalar da Musulman kasar Spaniya suka sha, wadanda a hankali aka tursasa musu har sai da aka kore su daga kasarsu, daga gidajensu, daga karshe ma sai da aka share su a doron kasa. Duk wannan aiki ne na ‘jakadun danniya,’ wadanda a wancan zamanin suka yi wata shelata wacce ke kumshe da rashin imani domin cimma muradunsu na son rai. Wannan shelar tasu itace ta zama silar share dukkan wani musulmi daga Spaniya; ta muganyar hanyar da ta sabawa dan adamtaka da al’ada.

samndaads

Zamani ne da tarihi ya tabbatar da cewa an samu wasu al’ummu guda biyu, masarauta mai cikakkiyar iko da karfin soja, a daya bangaren kuma akwai jakadun danniya; yayin da wadannan masarautu suke amfani da kisan mummuke, ta’addanci, kwace da tauye hakki akan mutanen da gazawarsu kawai itace son zaman lafiya da gujewa tada zaune tsaye; kuma wadanda domin su tabbatar da wanzuwar Al-Andalus suka yi ta aminta da yarjejeniyoyi da su ake kwara. Wadannan yarjejeniyoyi babu wacce ‘yan danniya basu karyata ba. Daga karshe dai, musulmin Al-Andalus basu da wata mafita da ta wuce su mika wuya, bisa sharadi kwara daya tak, shi ne a barsu su rayu cikin aminci a matsayin Musulmi. Shi ma wannan sharadin sai da aka karya shi a lokacin da suka ajiye makamansu na yaki. Da wannan aka samu damar murkushe su har kasa. Aka rika farautarsu daga gidajensu, wadanda suka ki ficewa kuma aka kone su da ransu hade da gidajen. ‘yan kalilan din da suka rage a raye, sai da ta kai an kai su bango, suka  dauki tsauraran matakai domin su tsira da imaninsu, sun yi ta amfani da ilmukan da suke da su na kwarewa na gina masallatai, suna gina gidajensu ta yadda zasu samu damar yin salloli cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Sun yi hakan ne a lokaci guda tare da yin taka tsantsan, don kar a gano su, domin idan aka gano su, za a kona su ne da rana tsaka a gaban tururuwar al’umma.

Zamani ne da aka aikata laifukan ta’addanci, danniya, kwace da keta, wanda ba a taba irinsa a tarihi ba. Lokaci ne wanda mashaya jinni ‘yan danniya suka share mutane ma’abota zaman lafiya. ‘yan danniyan da tarihi ya adana cewa ayyukansu su ne kona mata da ransu, kone garuruwa kurmus, tare da kone dimbin littattafai; duk fa sun aikata wannan ne wai don su kawo karshe abin da suka jahilta. Wadannan azzalumai ‘yan danniya su ci gaba da amfani da horon da suke dashi, ba kunya, wurin share alkaryu, rushe al’ummu, tare da bautar da mutane. Wadannan su ne mutanen da alhakin share al’ummun Maya da Inca ke rataye a wuyansu. Duk wani wanda suka tabbatar cewa ba zasu iya yi wa wayo ba, sai su rusa shi kawai. Duniya da dan adamtaka ba su da wani abin zargi wanda ya wuce wadannan ‘yan danniya, irinsu Pedro de Albarado, Hernan Cortez da Nuno de Guzman. Wadanda ayyukansu suka haifar da asarar ilmukan da har abada ba za a sake samunsu ba. Kuma fa duk sun fara irin wannan ne a kan Musulman Al-Andalus, wadanda suke makwabtaka dasu. Har ma ta kai wadannan makasan suna yekuwar ‘Deus Bult!’ sam suka ki su kaunaci makwabtansu kamar yadda Yesu (Annabi Isah) ya umurta.

Bayan shekara daya kwatsam, su dai wadannan sojojin Nijeriya, suka yiwa gidan mahaifina kawanya na sama da kwanaki uku, sannan suka far mishi, tare da yin amfani da muggan makamai don su share hanya, suka yi ta yiwa mata fyade da kisa yadda suka so. Haka suka kutsa da karfi har suka samu wani daki inda sauran mutane da suka rage suke ciki; a dakin ne iyaye na da ragowar kanne na uku suka samu mafaka. A nan suka farmaki dakin da ruwan harsasai, har sai da suka tabbata cewa kowa baya motsi. Ina waya da mahaifiyata, har zuwa lokacin da na ji wayar da ke hannunta ta fadii kasa, kuma na ji lokacin da sojojin ke fadin ‘this one no die’, sai kuma karar harsasai da suka ci gaba da harbawa. Dukkansu ina jin muryoyinsu a lokacin, suna kisa, amma ko a jikinsu.

A kasa da shekaru uku, Sojojin Nijeriya sun dau haramar kamfen din da suka kasa cimmawa, na son kawo karshen ‘Boko Haram’, wasu makiyan da samuwar ire-irensu sai a karnonin baya, wadanda ke ikirarin cewa ilimi zunubi ne! makiyan da a wancan zamanin burinsu shi ne su lalubo kahon mala’ikan mutuwa, don su busa, a nasu kullallen tunanin, dole ne ma a yi tashin duniya yanzu-yanzu.

Sojojin Nijeriya day a kamata su mayar da hankali wurin yakar wadannan mutane masu cunkusasshiyar kwakwalwa, a yakin da suke ba sassautawa, ba wai kawai sun gaza cimma murkushe su bane, a’a sun iya zuwa da rana tsaka suka kashe kanina Ahmad. Dalibin ya kammala digirinsa na farko a fannin ilmin makamashin sinadarai ‘Chemical Engineering’, babban burin Ahmad shi ne ya ci gaba da karatunsa a matakin digiri na biyu. Da harsashinsu suka kashe Hamid, haziki kuma dalibin da zai shiga shekara ta biyu a fannin ‘Aeronautical Engineering’, wanda sauran masa shekaru biyu ya kammala digirinsa na farko. Mahmoud wanda ke tsananin shaukin zama kwararren mai zane, kuma me burin zama mai zane.

Shekara guda bayan wannan ta’asar, Hammad; wanda Sigmund Freud da Hilgard su ke matukar burge shi, yake kuma nuna shauki a duk lokacin da ake tattaunawa dangane da fannin sanin halayyar jama’a, sojojin Nijeriya suka kashe shi a daki, ba tare ma da ya samu damar shiga jami’a ba. A tare da shi akwai Ali, wanda shi ma kanina ne, a sannan yana samun sauki daga mummunan raunin da ya kusa zama sanadin yanke kafarsa, a dalilin harbin da sojoji suka yi masa lokacin da suka kashe su Ahmad. Dan autanmu shi ne Humaid, wanda har a lokacin dan kankanin yaro ne, wanda kodayaushe yana son yin wasa da sanya tufafi irin na Captain Jack Sparrow, da Ezio Auditore da Firenze. Yayin da yake tsalle-tsalle daga wannan ginin zuwa wancan, daga waccan bishiyar zuwa wannan tagar. Sauran wadanda ke cikin dakin a tare da su, bani da wani cikakken tarihinsu. Amma abin lura anan shi ne, shekaru biyu kenan da aikata wannan ta’asar, kuma an hana mana damar bizne su cikin sutura. Dukkansu an hada su a kabarin bai-daya, a wani wuri da ke Jihar Kaduna.

 

A na iya tuntubar Mohammed ta: mz4real1@gmail.com

Za mu ci gaba….

SendShareTweetShare
Previous Post

Mene Ne Tsarin Manhajar Android (Android system)?

Next Post

Yawaitar Shaye-Shaye Miyagun Kwayoyi Ga Matasanmu!

RelatedPosts

Almajirci: Ya Kare Zai Kashe Ragon Layya?

Almajirci: Ya Kare Zai Kashe Ragon Layya?

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Kalmar 'Almajiri' balarabiyar kalma ce da aka kankareta daga kalmar...

Hon. Bello

Abinda Ya Sa Hon. Bello Kumo Ya Ciri Tuta A Siyasar Gombe

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Irin girman tasirin da Jagorori suke yi a fannonin rayuwa...

Sabuwar Shekara

Wata Mahanga Daga Jawabin Buhari Na Sabuwar Shekara

by Muhammad
3 weeks ago
0

Daga Gidado Ibrahim, Jigo a tsarin shugabanci na Dimokradiyya shi...

Next Post

Yawaitar Shaye-Shaye Miyagun Kwayoyi Ga Matasanmu!

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version