Tamowar Yara: Babban Kalubalen Da Ke Gaban Hukumomi Da Gwamnatoci

Matsalar tamowar yara na daya daga cikin barazanar da ake fuskanta a arewacin Najeriya wanda a dalilin haka kullin yara suna mutuwa da yawan gaske duk da irin matakan da aka ce ana dauka daga lokaci zuwa lokaci.

Shi dai wannan ciwa ko lalura yana kama kananan yara wanda in ba a dauki mataki na gaggawa ba ana rasa ransu ba tare da bata lokaci ba, wani lokaci ana dora alhakin hakan akan rashin kula ta iyaye da kuma gwamnatoci da hukumoni.

Sai dai kuma duk da irin wannan baarzana da ake fuskanta game da wannan annobar, wani lokaci a maimakon abin ya rika raguwa sai ma ka ga ya kazanta fiye da lokutan baya, ko menene dalili?

Wani abin tambaya me yasa wannan babar matsala ta yi katutu a arewacin Najeriya duba da irin makudan kudadan da hukumomi da gwamnatoci suke kashewa domin ganin bayan wannan annoba?

Akan wannan babar matsala masana sun yi tarurrukan karawa juna sani, sannan suna cigaba da gudanar da tarurruka har gobe domin kawai a shawo kan wannan matsala.

Abin tambaya anan me yasa wannan matsala ta yi yawa da kamari a jihar Katsina wanda hakan tasa har bincike ya nuna cewa jihar ta Katsna tana sahun farko wajan fuskantar matsalar tamowar yara duk da irin kudi da magungunan da gwamnati ke badawa wajan samar da sinadarin dan kwamaso wanda ke zama garkuwa ta wannan ciwo?

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2015 ya ce jihar Katsina ita ce uwa ma bada maman akan wannan lalura ta tamowar yara, ciwo mai azama da saurin kashe yara, idan har ba a samu kulawa ta musamman da wuri ba.

Sakamakon wannan bincike yasa kusan kowane lokaci masana akan wannan fanni sun fi maida hankalinsu a jihar Katsina domin ganin sun bada muhimmiyar kulawa da zata iya rage mace-macen kananan yara ko kuma kawo karshe wannan Bala’i.

Bisa la’akari da haka a kwanakin baya wata kungiyar kasa da kasa mai kula da lafiyar jama’a ta hanyar amfani da kafafen yada labarai ta shirya taron karawa juna sani a jihar Katsina, inda masana suka tattauna batutuwa da dama akan yadda za a ga bayan wannan matsala tare da ba misalin wasu daga cikin cibiyoyin kula da masu wannan laliura.

A jihar Katsina dai akwai kananan hukumomi goma sha biyar da aka zaba domin bude cibiyoyin kula da masara lafiya akan matsalar tamowar Yara, wanda kuma shiri  ne na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Katsina da kuma hukumar kula da asusun kananan yara na majalisar dinkin duniya.

Wannan shiri ya dauki lokaci ana gudanar da shi, wani lokacin kamar an samu saukin abin amma daga baya sai ka ji wani wuri ya balle, haka kuma akwai matsaloli da ake fuskanta nan da can wanda hakan ba karamin koma baya yake kawowa a cikin aikin ba.

Wasu jami’an lafiya sun bayyana yadda ake karkatar da sinadarin dan kwamason wanda suka ce yana taimakawa wajan kawo ci baya akan yunkurin gwamnati na kawar da wannan babar matsala.

Sai dai kuma bincike ya nuna cewa tuni an dauki matakin ganin an daina karkatar da wannan sinadari na dan kwamaso, bayan da aka gudanar da wani bincike da ya hada da kungiyoyin farar hula da kuma hukumomin da abin ya shafa.

A taron da masana harkar kiwon lafiya da ya shafi kula da kananan yara da aka gudanar a jihar Katsina an kawo hanyoyin masu kaiwa tudun mun tsira akan wannan matsala sai dai an bayyana cewa dole sai jama’a sun bada ta su gudunmawa kafin haka ta cimma ruwa.

Masanan sun bayyana kafafen yada labarai a matsayin wani ginshiki da zai zama abokin tafiya wajan ganin karshen wannan matsala saboda haka dole ne kafafen yada labarai su kara ninka kokarinsu wajan wayar da kan jama’a musamman mutanen karkara da su dauki matakin kaucewa kamuwar yara daga wannan cuta.

Akan haka, masanan sun zagaya daya daga cikin cibiyoyin da kula da yada masu lalurar tamowa da ake karamar hukumar Mani domin gani da ido ance ya kori ji, wannan cibiya dai cike take da yara kananan masu fama da wannan matsalata tamowa amma dai ana kuka da su da kuma ba su magunguna tare da sinadarin dan kwamaso.

Jami’an lafiya a wannan waje sun bayyana yadda ake kara samun tururuwan jama’a zuwan amsar wannan sinadari na dan kwamaso inda suka ce abin yana kara yawa musamman a lokacin damina, amma dai lokacin bazara ko sanyi ana samun raguwan yara masu dauke da wannan lalura.

Alhaji Mamman Sani na daya daga cikin jami’an da ke kula da wannan cibiya ya bayyanawa jami’an kungiyar kasa da kasa da ke hadin gwiwa da kafafen yada labarai akan kula da lafiyar jama’a cewa a matakin gwamnatin jiha suna kokari so sai wajan samar da wadataccen sinadarin dan kwamaso musamman a wannan gwamnati da abin ya koma kai tsaye da gwamna Aminu Bello Masari a mai makon wasu jama’a da suke tafiyar da abin a baya.

Ya ce wannan mataki da aka dauka ya taimaka wajan hana karkatar da wannan sinadari a wannan karamar hukuma ta Mani duk da cewa suna da wasu sauran cibiyoyin a wasu garuruwa amma ba su da wani korafi na karkatar da wannan sinadari ta hanyar da ba ta da ce ba.

Mamman sani ya ce duk da kokarin da gwamnati ta ke yi a matakin jiha da kuma karamar hukuma suna da wasu matsaloli da suke kawo masu cikas wajan tafiyar da wannan mahimmin aiki, wannan matsala kuwa ita ce ta ruwan sha.

A cewarsa suna da matsalar ruwa a dukkanin cibiyoyin kula da masu wannan matsala ta ciwon tamowa saboda haka wani lokaci sai sun yi amfani da kudinsu domin sayan ruwan da za su yi amfani da shi a cibiyoyin.

“idan da ace muna da wadataccen ruwa sha, kudin da za mu yi amfani da su wajan sayan ruwa sai mu yi wani abu da su, amma yanzu dole sai mun sayi ruwa saboda aikin ba zai tafe ba dole sai da ruwa tsaftattace” in ji shi.

A bangaran masana da suka shirya taron karawa juna sani game da wannan matsala da wasu cututukan da ke barazana da rayuwar yasa kanana kuwa, an koyar da sabbin dibarun yadda za a wayar da kan jama’a su kara gane mahimmacin kula da lafiya musamman a karkara ta yadda za su kaucewa kamuwar yara daga ire-iren wannan matsala.

Babu shakka an ilimantu kwarai da gaske kuma an dora dan ba, na yi aiki hannu da hannu da sauran hukumomin kula da lafiya domin cigaba da wayar da kan jama’a game da wannan baban bala’I da kuma kara zaburar da hukumomin da abin ya shafa domin su yi abinda ya kamata ta bangaransu a samu nasarar da ake bukata.

Sannan an tattauna kalubalan da ke gaban jami’an yada labarai game da tirjiyar da suke fuskanta wajan samun bayanan da za su taimakawa aikinsu ya tafi cikin nasara, wanda shima aka bayyana a matsayin baban kalubale.

Ba a tashi taron ba, sai da aka samu matsaya wanda zata zama tsani kuma ginshiki da zai taimakawa dukkanin bangarorin su yaki wannan muguwar cuta sannan jama’a na karkara su kara sanin abinda ya kamata su yi kafin yaransu su kamu da wannan matsala.

Haka kuma idan sun kamu kuma sun gama karbar sinadarin dan kwamaso ga irin abinci da ya kamata su cigaba da ba su, idan kuma sun ga wata matsala sabuwa ga matakin da za su dauka cikin gaggawa.

Exit mobile version