Tarayyar Turai Za Ta Tallafawa Nijeriya Wajen Kare Hakki Bil’adama

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta yi alkawarin tallafawa Nijeriya da dukkanin abin da ya kamata kan sha’anin kare hakkin bil’adama.

Jagoran tawagar kungiyar ga Nijeriya, Ambassada Ketil Karlsen, shi ne ya bayyana hakan a yayin tattauna tsakanin Nijeriya da Tarayyar Turai din wanda ma’aikatar hulda da kasashen waje ta Nijeriya ta shirya a ranar Talata a Abuja.

Karlsen, ya tabbatarwa da ‘yan jarida sakamakon zaman na su da ministan hulda da kasashen waje na Nijeriya, Geoffrey Onyeama, da wadansu masu ruwa da tsaki kan kare hakkin bil’adama, inda ya ce sun zauna ne domin duba matakin da ya kamata su dauka a gaba.

Ya tabbatar da cewa wannan shi ne zama na biyar na tattauna yadda za a kare batun hakkin bil’adama da kuma ‘yan Nijeriya marasa galihu a kasarnan. EU ta ce tana daukar batun kare hakkin bil’adama da muhimmanci wajen hulda da Nijeriya, inda ya ce suna haduwa domin tattauna ci gaban da za a kawo bangaren da shirya ma wadansu taruka.

“A Nijeriya, muna kan shirya wadansu taruka dangane da kare hakkin bil’adama, kuma muna ganin ci gaba.” In ji shi.

Exit mobile version