Daga Ibrahim Muhammad Kano,
Tsohon Gwamnan jihar Kano Dokta Rabiu Musa Kwankwaso Wanda Yayi rashin mahaifinsa Hakimin Madobi.Alhaji Musa Saleh Kwankwaso a safiyar ranar Juma’a ya bayyana cewa marigayin yayi musu tarbiyya ta jajircewa da tsayawa akan gaskiya.
Yace tun suna yara mahaifin basu yasa dukkanninsu makarantar boko data Islamiyya ya basu tarbiya ingantacciya wacce tarbiyar ita ce take binsu har yanzu da suka shiga kusan kowace kasa a Duniya, amma wannan tarbiya tana nan tare dasu ba za’a jisu a cikin wasu abubuwa marasa kyau ba, Wanda hakan nada alaka ne da irin kyakkyawar tarbiyyar da mahaifin nasu ya basu.
Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, suna godewa mahaifin nasu da yi masa addu”ar Allah ya saka masa da alheri domin kamar yadda aka shaida musu a shekara ta 1956 aka haife shi a kuma cikin wannan.shekarar kuma ya zama sarkin Kwankwaso bayan kimanin shekara 20 ya zama maji dadi ya kuma zama Hakimin Madobi wannan ya bada dama ya zauna da mutane lafiya wanda bai zama musu wata matsala da suke siyasa wanda zai musu gori da wani laifi kwaya daya ba.
Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya ce, kafin rasuwarsa suna tare da shi a daren Alhamis suna maganganu amma cikin dare jiki ya yi zafi kuma wayewar gari Juma’a 25-12-2020 Allah ya yi masa cikawa suna addu’a Allah ya jikansa ya yi masa gafara suna fata suka Allah kyautatawa tasu in tazo.
Kwankwaso ya godewa dukkan mutane da suka zo jana’iza da wanda ke zuwa dan taya su alhini da fatan Allah ya sake musu da alkhairi.