Connect with us

ADABI

Tarihi: Mulkin Fulani A Kano, Da Gwagwarmayar Rikon Sarauta

Published

on

Cigaba daga makon jiya

Fitinar Wasu Kabilu Mazauna Tsaunika

A wannan lokacin dai na Mulkin sarkin Kano Marigayi Abdullahi dan Ibrahim Dabo fitinar wasu kabilu mazauna tsaunika ta bijiro.

An ce sarkin Bauchi Ibrahim ya gwabza yaki dasu, amma sai ya hadu da raunin dakarunsa a kansu, tilas ya koma gida don sake shiri.

To ganin haka kuma, sai kabilun ya zama kamar sun samu karfin guiwar cigaba da takurawa jama’a ne, inda suka rink’a tura mayakansu garuruwa suna kamo mutane a matsayin bayi gami da kwace dukiyoyin su.

Abu kamar wasa, sai ya zama wannan ta’asa ta kwararo izuwa yankunan Kano, har ma an kaiwa wasu rundunoni da Sarkin Kano Abdullahi ya ajiye a yankunan hari.

Don haka, koda Sarki Abdullahi yaji haka, sai yace sam bazai kyale ba.

Wannan yasa ya tara ‘yan majalisarsa domin neman mafita akan cewa ‘shin zasu fara zuwa don kaiwa waɗannan kabilu harin yaki ne, ko kuwa gari ya kamata su soma kafawa inda za’a jibge rundunar yaki?’

A nan ne shawara ta tashi akan cewa a soma kafa gari kafin akai yaki. Hakan kuwa a ka yi.

Sarkin Kano Abdullahi dan Ibrahim Dabo ya aike aka gina gari, sannan ya tashi da runduna mai yawa izuwa garin.

Bayan ya dan huta ne sai yayi haramar yaki, ya fito daga garin da aka gina masa tare da tunkarar wadannan arna mazauna saman duwatsu.

An ce kafin ya karasa ɗdin ne sukaci karo da sarkin Bauchi Ibrahim, sannan dukkansu suka dunguma izuwa wani gari mai suna Duwa, suka yaki dakarun garin tare da tarwatsa su. Suka kuma k’one garin gaba dayansa, sannan kowanne sarki ya koma birninsa.

Bayan sarkin Kano Abdullahi ya komo Kano daga wancan yak’i na Duwa, bai jima ba sai ya sake hada runduna ta musamman sannan ya jagorAn ceta suka nufi yankunan arnan kan duwatsun nan, suka isarwa wani gari nasu mai suna Daraja, nan ma suka fada masa da yaki.

A ka yini ana gwabza yaki, dakaru na kai suka da sara da takubbansu ga abokan hamayyarsu, sai dai kaga wasu sun fadi k’asa matattu, wasu kuwa sun zube magashiyan da munanan raunika. Daga bisani dai, Sarki Abdullahi yayi nasara akansu.

Sannan dai bai gaji ba ya k’arasa wani garin nasu mai suna Tufai nan ma da niyyar ya yak’esu, amma sai ya tarar mutanen garin sun k’one gidajensu da kansu kuma sun gudu sun bar garin.

Ganin haka, sai kuma ya k’arasa wani garin mai suna Banga, inda ananma ya tarar babu kowa a garin. Mutanen garin sun bar gidajensu da dukiyoyinsu sun fice daga gareshi.

Don haka sai sarki ya umarci a sauka a garin don a huta.

Ashe wai mutan garin sunji labarin yaki ne shine suka gudu baki ɗdaya suka bar dukiyarsu.

Aikuwa An ce Sarki Abdullahi ya tara gagarumar ganima daga wannan gari.

A wannan dare da sarki Abdullahi da jama’arsa suka saukadon su huta a garin banga, sai basu samu hutun ba, ashe wai tarko aka dana musu don su fada a mamaye su, tunda kuwa arnan sun tara dakaru masu yawa sun lake, sai da dare yayi sannan suka kawo sumame.

Haka kuwa aka kwan ana buga kazamkn fada, amma dai cikin ikon Allah duk da haka arnan basu samu galabar yaki ba. Sarki Abdullahi da rundunarsa ne suka ci nasarar tarwatsa su.

A wani waje mai suna Sirfa aka hadu da mutanen dutsen warji tare soma gwabza yaki.

Mutanen sun samu gagarumar taimako daga wani sarkinsu, amma cikin ikon Allah anan ma saida aka sake tarwatsa su.

Da sukaga an soma cin galaba akansu, sai suka soma ja da baya suna hawa saman dutsen inda gidajensu yake, ita kuwa rundunar sarki Abdullahi tana binsu sannu a hankali tana kashe su.

A haka har sai da suka kai kansu wani kogon dutse inda babu wurin ficewa, sai kuma suka nemi a dakata da yaki, suka kuma nemi a basu tsaro, ko kuma ace alkawarin ba za’a kai musu hari ba.

Su ma kuma suna masu alkawarin ba zasu sake tayar da fitina ba ko zaluntar musulmai.

Abinka da jarumin Shugaba, Sarki Abdullahi mai koyi da halin ma’aiki Annabi Muhammad (s.a.w) Sai sarkin yace anyi musu duk abinda suke so.

Kadi Muhammad Zangi ya ruwaito a littafinsa “Takyidil Akbar” cewa yana cikin wannan runduna tare da sarki Abdullahi, “haka muka sauko daga saman wannan dutse sannan muka shige izuwa wani wuri kusa da garin Gwaram mai suna Aru, arnan nan suna ta lekenmu daga saman datse suna mamaki”.

A ka ce mutane kadan ne suna rage a garin Aru a lokacin da rundunar sarki Abdullahi suka riski gsrin, sauran duk sun tsere.

Wadanda suka rage din suma zuwa sukayi ga sarki Abdullahi suna masu tuba da eman kuduta daga gare shi.

Nan take suma aka shimfida musu dokokin dake k’unshe cikin yarjejeniyar zama lafiya, suka ce “munji kuma mun karba”.

Sarki kuwa yace “to kun kuduta”.

Daga nan sai sarki ya tashi da jama’arsa suka komo Kano.

Sai dai bai gama huce wannan gajiya ba ya samu labarin cewa wadancan arna dukkansu sun karya yarjejeniyar da aka kulla dasu..

Da Sarkin Kano Abdullahi ɗan marigayi sarki Ibrahim dabo yaji arna mazauna saman duwatsu sun cigaba da tayar da fitina ga makwabtansu, sai yace “tunda wadancan mutane sun karya alkawari, tilas mu koma garesu da yaki.”

Nan take ya shiga shirin hada gagarumar rundunar yaki.

An ce duk wani babban barde, ko wani kwararre a fagen fama dake kasar Kano karkashin ikonsa sai da sarki Abdullahi ya gayyato shi, sannan ya tattarasu ya jagoranci runduna izuwa garin Daraja.

Za mu cigaba a makon gobe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: