Connect with us

ADABI

Tarihi: Mulkin Fulani A Kano, Da Gwagwarmayar Rikon Sarauta Gabatarwa

Published

on

Sarki Sulaimanu dan Aba Hama shine sarki na farko a jerin sarakunan fulani na Kano tun bayan da fulanin suka jagoranci yakin jihadi tare da karde iko da kasar Kano baki daya.
Sai dai kamar yadda aka sani, kowanne mulki ya kanzo da kalubale mabanbanta. Don haka rubutun zai kalli yak’unan da sarakunan fulani suka gwabza da abokan hamayya masu son daukar fansa daga garesu, ko kuma ace masu son kwace kasarsu ta haihuwa daga hannun fulani baki.
Haka kuma, zamufi maida hankali ne akan rikice-rikicen da suka auku daga zamanin Sarkin Kano Sulaimanu izuwa yakin basasar Kano, da kuma zuwan turawa birnin na Kano.

Sarkin Kano Sulaimanu
A zamaninsa ne aka halaka tsohon sarkin Kano Alwali bayan ya dawo garin burum-burum da zama daga zariya inda ya fara yin hijira.
Wasu sunce Mallam Bakatsine Sarkin Kano Sulaimanu ya tura domin yaje ya halaka Sarki Alwali, amma wasu na ganin Mallam Jamo ne jagoran rundunar ba Mallam Bakatsine din ba.
Amma dai abu mafi inganci shine, wannan runduna ta isa garin burum-burum, tayi gagarumin fada da rundunar Sarki Alwali, a karshe ta samu nasarar halaka sarkin acikin garin burum-burum inda ya fake, tare da komowa Kano da ganimar yaki mai yawa.
Sheikh Abdullahi Ibn Fodio (Kani ga limamin yakin jihadi shehu Usmanu dan fodio) ya ziyarci Kano a zamanin mulkin sarkin Kano Sulaimanu, a watan azumin Ramadana, har ma An ce shine wanda ya nuna alkiblar masallacin Kano na jumu’a dake kofar fadar Sarki, sannan shine yayi jagorancin sallar nafila bisa rashin lafiyar Rana (khusufin Rana) daya faru a wannan watan na Ramadan.
Tarihi ya nuna cewar Sheikh Abdullahi dan fodio ya zauna a Kano na wani lokaci, ya kuma karantar da mutane ilimin addinin Islama, tare da rubuta wani littafi garesu mai suna ‘Diya’ul Hukamah’ domin taimakonsu wajen sauke nauyin mulkin daya hau kan jagorori bisa bukatarsu da suka nuna gareshi. Sannan yayiwa Kano addu’a matuka dangane da yalwatar arziki da nema mata tsari daga dukkan sharri.
An ce shekaru goma sha uku Sarki Sulaimanu yayi yana mulkar kanawa, amma ba’a samu fitintinu sosai ba a lokacin mulkinsa.
K’ari akan yakin kashe sarki Alwali da akayi a zamaninsa sai yakin da akayi da maguzawan wani gari mai suna Fagam. Inda sarkin yahau da kansa akaje akaci garin da yaki tare da kamo fursunoni da ganimar yaki.
Baya da wannan kuwa sai boren da sojojin tumbi suka tayar, inda suka rinka tare mutane suna musu fashi. Suma sai da aka je kansu da yaki sannan aka samu lafiya.
Sai dai, akwai wani mai suna Dantunku a zamanin, wanda ya rinka tara sojoji da shirin yak’i a boye ba tare da masarautar Kano ta sani ba har sai da sarki sulaimanu ya rasu sannan ya soma daga kara..
Sarki sulaimanu ya rasu ranar wata lahadi da dare, a karshen watan shawwal.
Da fatan Allah ya gafarta masa amin.

Mulkin Sarki Ibrahim Dabo dan Mamuda
Bayan Allah ya karbi ran sarkin Kano Sulaimanu dan Hama bafillatani na farko a jerin sarakunan Kano, sai Sarkin Muminai na lokacin Muhammadu Bello ya aiko da takardar nadin Ibrahim Dabo a matsayin Sarki, tare da umarnin sauran malumman nan da suka jagoranci yakin jihadi su cigaba da kasAn cewarsu a matsayin rukunin masu zartaswa wanda sarki bazai aiwatar da wani lamari ba sai da sahalewarsu.
Koda yake, izuwa wannan lokaci An ce akwai wadanda Allah yayiwa rasuwa misalin Mallam Abdurrahman wanda aka nada dan danuwansa Mallam Jibrila mai suna Ummaru a muk’aminsa, sai kuma Mallam Jamo wanda shima Mallam Ibrahim Dabo ya soma zamowa magajinsa bayan rasuwarsa kafin kuma Sarki Sulaimanu ya rasu har a zakeshi a matsayin sarki.
Baya da haka, sai kuma wadanda aka tura shugabanci suka bar Kano izuwa wasu sassan, misalin mall mam Amadu da aka nada Sarkin Gaya, da kuma Mallam Muhammadu Bahr Ajami dan Alhaji da aka tura ya zama sarkin Dawaki.
Mallam Sulaiman Ango shi aka nada Wambai a masarautar Kano, yayin da Mallam Muhammadu Sani yake a matsayin Waziri, amma bayan rasuwarsa sai aka daga likkafar wambai ya dawo waziri.
Bayan Sarki Ibrahim Dabo ya hau karagar mulkin Kano, sai ya turawa ‘yanuwansa sarakunan garuruwa da takardu yana mai sanar musu sarautar daya samu. A bisa haka ma ya turawa Dantunku takarda yana mai sanar dashi cewar yanzu fa shine sarkin Kano, amma sai Dantunku ya maido da ba’asi na lafuzza masu bata zuciya. Badon komai ba sai saboda Sarki Ibrahim Dabo ya nemi Dantunku ya cire hannunsa daga sha’anin kabilar wadade, sai kuwa yace da sarki Ibrahim Dabo sam ba zan cire hannusa daga mutanen da yake da alaka dasu ba.
Shi Dantunku shine sarkin Kazaure, kuma tare akayi yak’in jihadi dashi har aka samu nasarar karde iko da Kano, inda aka tabbatar dashi a matsayin sarkin Kazaure. Amma daga baya sai wasu dalilai suka sanya ya soma yunkurin yin bore
Bayan anyi wannan, sai Sarki Ibrahim Dabo ya tafi Sokoto domin kai ziyarar ban girma ga sarkin musulmi. A lokacin sai kuwa Dantunku ya soma aikewa ga yankunan maguzawa cewar yana neman taimakonsu domin suyiwa fulani masu sarautar Kano bore.
Abu fa kamar wasa, kafin wani lokaci Dantunku ya tara gagarumar zuga har ya zamo yana yunkurin kwace iko da gabashi da kuma yammacin Kano.
Wannan yasa dole sarki Ibrahim Dabo ya shirya zama da kwamitin malamai inda suka yanke shawarar cewa a tura runduna domin takawa Dantunku burki tun da wurwuri.
Rundunar farko ta tashi ta nufi yankin garin bichi Bisa jagorancin Madaki, sai da suka isa garin Danzabuwa, sannan suka hadu da dakarun Dantunku. Anan aka gwabza wani kwarya-kwaryan yaki wanda kowanne cikin rundunonin biyu sai da yaji jiki, sannan aka rabu.
Madaki yaja zuga sukayi yamma, daga bisani suka hade da Mallam Ali da Mallam Bakatsine dukkaninsu da tawagar mayaka, sannan suka komo garin mazan gudu suka yada zango.
Da dare sai ga rundunar Dantunku itama ta sauka a wannan guri, mai cike da tururuwar mayaka.
Gari na wayewa rundunonin biyu suka fuskanci juna, kafin daga bisani suka rinchade da fada.
A wannan yakin ne Gwani Hafizu Muhammad masanin alkurani maigirma ya rasu, sannan an kashe musulmai masu yawa ciki harda Mallam Ali, aka kame wasu a matsayin fursononin yaki tare da kone gidajen dukkan musulman dake yankin.
Hakika rundunar sarki Ibrahim Dabo tayi gagarumar asara a wannan yaki.
Daga nan fa sai yanayi ya soma tsamari ga fulani. Runduna ta koma baya babu nasara, gashi kuma Dantunku sai yayibar mayaka yakeyi, mutanen da suka koma musulunci bisa tsoron karfin fulani suka soma samun sakewa da damar komawa ainihin al’adarsu ta baya. Zaman Kano ya soma zama abu mai wahala saboda tsoron mahara masu kamen fursunonin yaki da kuma fargabar yaki.
An ce ana haka sai Sarki Mallam Ibrahim Dabo ya shiga Halwa a gidansa.
Kadi Muhammad zangi ya ruwaito a Littafinsa ‘Taykidil Akbar’ cewar sai da Sarkin ya shafe shekaru biyu a wannan halwa a gidansa wanda babu mai shiga wurinsa sai bayi masu yi masa hidima kurum. Babu abinda yakeyi sai neman nasara daga Allah ta’ala. Daga nan ne ya fito.
Da fitowarsa sai ya yanke shawarar kafa sansanoni biyu domin samar da tsaro ga Kano. Ya aike da runduna dawakin Tofa, daya kuma ya aike da ita Ungogo.
Babu jimawa ne sai ga Dantunku yayo hawa, ya nufo Kano da yaki, amma da isarsa Ungogo sai sadaukan Sarki Dabo suka tareshi da yaki. Allah cikin ikonsa ya basu nasara inda suka koreshi tare da watsa tawagarsa.
Daga nan sai Sarki Dabo ya sake kafa wasu sansanonin a Dan madafo, da Mariri da Tankarkar. Sannan yasa aka shiga atisayen horas da dakaru dabarun yaki.
Baya da haka yasa aka tara masa dakarunsa wuri daya, yazo garesu tare dayi musu jawabi. Yayi zantuka masu sanya dakiya a zukata garesu, ya janyo ayoyin alkurani da hadisai masu karfafa zuciya ga dukkan mai shirin yin jihadi, sannan ya nemi suyi shirin yaki gagarumi..

Yaki A Santalmawa, Jijitar, Sankara Da Kunchi Tare Da Kwache Garin Rano

Daga nan sai rundunar yaki ta cigaba da tunkarar Daular Dantunku. Sannu a hankali suka riski garin Gasakole, inda aka fafata yaki gagarumi da rundunar Dantunku. Rundunar Sarki Ibrahim Dabo tayi nasara tare da sake nausawa suna masu fuskantar Kazaure.
Suka isa Santalmawa, nan ma suka gwabza yaki tare da kwace ikon garin daga sadaukan Dantunku. Daga nan sai gasu a garin Jijitar, nan ma suka gwabza yaki kuma suka sake samun nasara.
A garin Sankara ne dakarun Sarki Ibrahim Dabo suka samu gagarumar nasara, saboda shirin da Dantunku yayi musu ta hanyar tara damin sadaukai a garin da niyyar yi musu sukuwar sallah. Aka nada wani mai suna Ardo Hunturke jagoran runduna.
Koda jagorar rundunar Sarki Ibrahim Dabo maisuna mallam Ali yaji wannan labari sai shima yayi shiri, ya kara tattaro dakarun dake biyayya da sarki Ibrahim Dabo daga kabilun fulani, hausa da kanuri, sannan ya zube su a wuri daya cikin shirin ko-ta-kwan.
Ai kuwa Kwatsam sai ga mutanen dantunku sun kawo musu hari, babu bata lokaci sai yaki ya darke.
Ci gaba a shafi na 25
Ci gaba daga shafi na 14

An ce ko mutum daya daga rundunar mallam Ali bai rasa ransa ba, amma sun karkashe abokan gabarsu da dama tare da watsasu inda suka ruga izuwa iyakokin daulolin Borno da Damagaram domin tsira da rayukansu.
Baya da haka, anyi yaki a Malikawa, anan ma fulani sunci gagarumar nasara sun kuma samu ganima.
Daga nan sai akace sarki Ibrahim Dabo yayo hawa izuwa garesu. Yayi musu wa’azi da jinjina, sannan ya tashi Mallam Ali da runduna ta tafi kunchi ta buga yaki da dakarun garin tare da kwace shi daga hannun sadaukan Dantunku.
Bayan nan ne sai sarki Ibrahim Dabo ya juyo da runduna da nufin komowa Fagge don ya yada zango kafin yaki ya kare. Amma sai labari ya iskeshi cewar Dantunku yayi shiri da mutanen fagge zasu tara itatuwa su kunna wuta idan dare yayi, wanda zai nuna alamar sadaukansa ne suka sauka a wurin, in yaso sai a shammaci dakarun Sarki Ibrahim Dabo a kawo musu hari ta baya.
Ai kuwa dajin haka sai suka zauna cikin shirin kota kwana. Suka isa fagge da dare, suka tarar anyi kamar yadda aka sanar musu.
Babu jimawa kuwa sai ga runduna ta auko musu da yaki, amma da yake cikin shiri suke, sai suka ce dawa Allah ya haɗamu ba daku ba, nan danan wuri ya rinchaɓe, har safe ana yaki, sannan rundunar da ɗantunku ya aiko ta ruga cikin rashin nasara, suka bar kayayyakin amfani masu yawa a matsayin ganima ga dakarun fulani.
Bayan yaki ya kare, dakarun sun cigaba da zama cikin shirin tsammanin koda Dantunku zai kawo musu hari da kansa, amma dai hakan bata auku ba.
Daga nan sai suka riskarwa garin Rano da yaki. Daman kuwa yana ɗaya daga garuruwan da fulani basu karɓe ikon suba a zamanin jihadinsu, don haka masarautar ta zamo dandalin da ake shiryawa fulani bore.
Sarkin Rano mai suna Barwa ya tarbe su da yaki, amma babu wata fafatawa gagaruma aka kasheshi tare da kwace ikon kasarsa baki ɗaya.

Yaki Da Dantunku A Garin Danyaya

Bayan shekara ɗaya, sai Dantunku ya shiga neman taimakon sarakuna na kusa dashi masu irin akidunsa, inda ya tara gagarumar tawagar sadaukai. Sannan yayi hawa da kansa ya nufo Kano.
A bakin tafkin sabon ruwa rundunoni biyu suka haɗu suna fuskantar juna a ranar wata lahadi sha shida ga watan rabiyul awwal. Mutanen ɗantunku a hagu yayin da rundunar Sarki Ibrahim dabo take a dama.
Bayan anyi cirko-cirko ns ɗan lokaci, sai kuma aka shiga faɗa da juna. Masu kibbau na harbawa, mazaje kuma suka shiga saran abokan gaba da masu gami da takubba.
A na haka sai aka ga kura ta turtuke, tayiwa wajen duhuwa na tsawon lokaci.
Bayan ta lafa sai akaga sarki Ibrahim Dabo ya bayyana a wurin shima yana saran abokan gaba da kansa. Wannan abu sai ya raunana zukatan Dantunku da mutanensa, suka tarwatse da gudu.
An ce ganimar da aka kawowa Sarki Ibrahim dabo a wannan rana gagaruma ce, wadda ta haɗa da bayi mata, dawakai, da kayan faɗa masu daraja.
Daga nan fa Dantunku ya zamo ya kunyata a idon duniya, yayinda sunan Sarki ibrahim Dabo ya ɗaukaka a birni da kauyuka, har maguzawa ma da kansu sun tsorata da sha’aninsa, har kuma akai masa lakabi da chigari.
Kunji asalin kirarin da akewa Kano mai taken Kano ta dabo cigari.
Bayan nan sai Dantunku ya saduda. Ya tura takarda ga Sarkin musulmi Muhammadu Bello a sokoto yana mai nana tubansa a fili, sannan ya aike da Arɗo Hunturɓe ya nema masa afuwa da yafiya a gurin sarki Ibrahim Dabo.
Shikenan kuwa sai aka yafe masa, ya zamo ya tuba daga boren da yayi, ya kuma koma musulmi cikakke.
Wanda ya tuba na karshe daga waɗanda sukayi bore ga sarki Ibrahim Dabo shine wani sarki mai suna Kashakori.

Sarki Ibrahim Dabo Jarimi Ne, Mai Kwazo Da Gwarzantaka A Fagen Fama

A na ce ma sa saifullahi saboda kafurai da dama sun mutu daga kaifin takobinsa.
Ya kashe ‘yan taadda masu yiwa addinin Allah bore da ‘yanfashi masu kwace dukiyoyin mutane babu adadi.
Da kansa yake hawa ya jagoranci yaki domin cinye gari. Kuma bai taɓa fita yaki baici nasara ba.
A zamaninsa ya tarawa Kano gagarumar dukiya. Ya tara bayi da dawakai da kayan faɗa masu ɗimbin yawa.
Ya shimfiɗa adalci, an kuma samu zama lafiya, har takai mutane na barin kofofinsu da dare basa tsoron ɓarawo. Dabbobi kuwa na yawatawa a gari ba tare da maisu ba.
Sannan saboda kwanciyar hankali mutum na iya tasow tun daga Kukawa ta daular Borno ya riski Kano babu fargabar fashi. Haka kuma tun daga Kano har ya riski tafkin kwara yana cikin aminci.
Sarki Ibrahim Dabo ya mulki Kano na tsawon shekaru 26 da watanni 2 da kwanaki 15. Ya rasu a ranar wata jumu’a, 9 ga watan safar gabannin sallar jummu’a.
A wannan rana, mutanen Kano sun ɗauka karshen duniya ne yazo, don haka kowannensu mutuwa zaiyi, saboda tsananin kauna da shauki da girma-mawar da suke masa.
Allahu Akbar. Allah yajikansa da rahama.
Shi bafillatani ne mai kyan sura, wanda ya fito daga jinsin sulluɓawa.
Sulluɓawa kuwa jam’i ne na sulluɓe, kalmar da akace an samo ta daga kakansu ko ace asalin wanda zuriyar ta fito daga tsatsonsa mai suna Sisillo. Shikuwa Sisillo, ai miji ne ga bafullatanar nan ta jinsin Toronkawa mai suna Chippowo, kanwa ga bafullatani batoranke Mallam Usmanu Toroddo, waɓda yake kakan-kakan shehu Usmanu Mujaddadi ɗan fodio.
Don haka ake ɗaukar jinsunan sulluɓawa da toronkawa na fulani a matsayin ‘yanuwan juna. (Ado-Kurawa 1989:45-49).
Asalin sulluɓawa wangarawa ne, watau ana iya cewar kakanninsu ne suka taɓa zuwa Kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Kanajeji har suka kawowa garin musulunci. Amma suna da alaka da yarukan Mandigo dana Mandika na yankunan Mali.
Sunan asalin yarensu shine wakore, daga baya suka nutse cikin fulatanci yayinda suka mAn ce yarensu suke yara fulbe (Usman 1974: 168-169).
Izuwa yanzu kuwa yana da wuya ko a gidan sarautar Kano da jikokin marigayi mallam Ibrahim Dabo ke mulka kaji ana fulatanci, domin tuni sun rikiɗe izuwa hausa zuryan.
An kuma samu cewar jinsin sulluɓawa, sunfi kowanne jinsi tsari mai kyau acikin kabilun fulani tun kafin jihadin shehu Usmanu, domin kuwa suna da shugabancinsu mai suna ‘Sarkin Sulluɓawa’ a duk inda suke.
Kuma a zandam suka soma zama, daga bisani suka rinka kwararowa yankunan katsina, zariya, sokoto da rima da sauran yankunan hausawa.
Sannan kuma, tun da jimawa suna rike ne da addinin musulunci bisa kyakkyawar turba. Don haka da yakin jihadi ya ɓarke, ‘yan kaɗan daga cikinsu ne suka goyi da bayan sarkin gobir, amma mafi yawansu suna cikin waɗanda suka bada gagarumar gudunmuwa wajen samun nasara, don haka nema ɗansu ya samu zamowa sarkin Kano.

Sarki Usmanu Dan Ibrahim Dabo

Bayan Allah ya karɓi ran sarki Ibrahim dabo, sai sarkin musulmi na lokacin Aliyu ɗan Muhammadu Bello ya naɗa Usmanu ɗan marigayi Sarki Ibrahim dabo a matsayin sarkin Kano.
An ce shekaru uku akayi cif ana zaune lafiya da farkon mulkinsa, daga nan kuwa sai musifu suka rinka bayyanuwa.
Da fari dai wani mai suna Hamza shine ya soma yin bore. Ya tara tawaga yana kai farmaki ga mutane, amma daga bisani sai yabar Kano izuwa kasar Bauchi. Amma duk da haka dai sarkin ya kafa runduna ya ajiyeta a Rumo ya sanya wani barde Guru na jagorantar ta.
An gama wannan kenan sai kuma da wani ɗan ta’adda daga Haɗeja ya bijiro yana uzzurawa mutane.
Can, Sai kuma ga sarkin Damagaram shima ya kunno da tasa fitinar.
Shi sarkin Damagaram ya sauka ne a Chiromawa tare da shafe watanni biyu yana kame mutane a matsayin fursunoni. Har sai da aka yake shi yana wannan garin sannan aka zauna lafiya.
An gama wannan kenan sai kuma ga Sarakunan Gobir, katsina dana Damagaram sun haɗa karfin dakaru suka nufo Kano da yaki.
Suka nufo Kano suna kashe musulmai.
An ce sun sauka a ‘dukawa’ ne tare da kashe dukkan musulmi da rushe gidajensu dake wurin. Amma sai Allah ya kuɓutar da musulmin Kano suka koma da baya haka siddan ba tare da wani dalili ba.
Hakika a zamanin Sarkin Kano Usmanu, Kano tasha wahalar yaki da rashin nasara daban-daban.
A zamaninsa ne Mallam Dabo Dambazau ya rasu, sai sarkin ya naɗa ɗansa mai suna Muhammadu kwairanga ya hau karagarsa. Haka ma da Madaki Ummaru ya rasu, sai ya naɗa ɗan uwansa Muhammadu Hadiri mukaminsa. Sannan da Alkali Ashafa ya rasu, nan ma sai ya naɗa Mallam Muhammadu Zangi a mukaminsa.
Kai bama suba, duk wani mai mukami daya rasu a zamaninsa sai daya naɗa ɗansa ko ɗan uwansa a kujerarsa, saboda cigaba da abinda mahaifinsa ya ɗorar.
Shi kuwa wancan bahaɗeje mai suna Buhari daya tashi fitinarsa sai daya kashe mutane da yawa, maza da mata da kananun yara.
Shine ma ya halaka jikan shehu Usman Danfodio mai suna Hassan ɗan Dambo. Don haka wasu ke danganta halayyarsa data Mu’awiyya wanda ya halaka jikan Manzon Allah (s.a.w).
Sannan kuma ya halaka mahaddata alkurani da dama.
A karshe sai Allah ya yiwa Sarki Usmanu ɗan Ibrahim Dabo rasuwa ana tsaka da wannn fitina bayan ya shafe shekaru 9 da watanni 9 yana mulkar kanawa.
Da fatan Allah yajikansa amin.

Za mu cigaba a makon gobe in sha Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: