Connect with us

ADABI

Tarihi: Mulkin Fulani A Kano, Da Gwagwarmayar Rikon Sarauta

Published

on

Cigaba daga makon jiya

 

Sarki Abdullahi Dan Ibrahim Dabo

 

Lokacin da Allah yayiwa sarkin Kano Usmanu dan Ibrahim Dabo rasuwa, sai sarkin musulmai na zamnin Aliyu dan Muhammadu Bello ya aiko da nadin kanin mamacin Abdullahi, wanda yake shima dane ga marigayi Sarki Ibrahim Dbo.

Koda hawansa sai baiyi wasu sauye-sauye ba, domin kuwa dukkan wasu mukamai daya tarar ya barsu, sannan duk wanda ya rasu a cikin fadawansa ya cigaba da sanya da ko danuwa yayi gadon wannan kujera.

Sarki Abdullahi mutum ne wanda ya tsaya kai da fata wajen tsaida gaskiya da adalci tare da tabbatar da tsaro na rayuka da dukiyoyin kanawa.

Sannan kuma an bayyana shi a matsayin mutum mai son yaki, wanda sa’ar da yahau mulki ya tara dawakai masu yawa ga mabiyansa sannan ya rinka jagorantar dakarun izuwa wajen ganuwar gari don yin atisayen yaki ta hanyar jera sadaukai sahu-sahu bisa dawakai sannan surinka tafiya da gudu suna garba bindigoginsu kamar suna tunkarar wasu gungun jama’a. Haka aka rinkayi tsawon watanni.

To daman idan ba’a manta ba, a wannan lokaci ana cikin zullumin fitinar da Buharin Hadeja ke tayarwa a kasar hausa. Don haka da Sarki yaga dakarunsa sun samu shiri mai kyau, sai ya tara su, yayi musu nasiha da wa’azi gami da karfafa guiwar daura aniyar yakin jihadi da Buharin Hadeja.

Sarkin Ya sanar musu da cewa matsawar Buhari ya kawo samame Kano, to tabbas wajibin sune subishi kwararo kwararo su cimma masa da yaki.

Ina ya Allah babu ya Allah, sai Buhari ya samu labarin shirin dakarun Kano da atisayen da sukayi. Don haka sai ya firgita, ya kawar da kai game da kawo samame garesu.

Amma sa’ar da yaji cewar sarki Abdullahi ya tafi sokoto domin kaiwa sarkin musulmi ziyarar girmamawa, sai kuwa yace dawa aka hadashi idan ba da Kano ba.

Shine ya kwararo cikin kasar Kano, yana tafe yana kwatar dukiya har wani gari nai suna Kademi dake gundumar Gaya.

Ya kame bayi, tare da kwace dukiyar jamaa, sannan yayi sauri yabar Kano yayin da yaji sarki Abdullahi yana tafe.

Da sarkin ya dawo sai aka sanar masa ta’asar da Buhari yayi. Sarki ya cizi yatsa, yace watau wannan shakiyi yana tsoron ai gamuwa gaba da gaba shine yake mana haka, to kuwa zamu cimma masa da yaki

Anyi haka babu jimawa sai sarki ya soma shirin yaki da Buhari, amma kafin a tafi sai ga takarda daga Buhrin yan neman sulhu da afuwa daga gareshi da kuma sarkin musulunci. Har da cewa a shirye yake ya shigo cikin mujahidai a rinka tafiya yakin jihadi dashi. (Sabod a lokacin yunwa da kishirwa ta fara galabaitar dashi da jam’aarsa, don haka yake neman mafaka).

Ganin haka sai sarkin ya tara jama’arsa ya bayyana musu abinda ke cikin takardar Buhari tare da neman shawarwarinsu.

A wajen sai rayoyi suka bambanta, wasu sukace sam kada a baiwa takardarsa amsa, kada a aikewa sarkin muslmi wannan sako, sannan a Kori ɗan aikensa da marmaza.

Amma sai wasu sukace kada ayi haka, domin zama lafiya yafi komai dadi a duniya.

Daga nan sai aka yanke cewar a mikawa Allah wannan lamari tunda an gaza samun matsaya. Don haka sarki ya sallamesu.

Kashe gari ya kira wasu daga cikin ‘yan majalisarsa, ya sanar musu da cewa ya yanke shawarar zai aikewa Buhari amsa yama mai cewa ya gamsu da wannan lamari, amma ɗan aikensa ya dawo nan da ranar alhamis domin tattaunawa, tayadda idan bada gaske bane, ɗan aiken bazai sake dawowa ba.

Sai duk suka aminta da wannan dabara ta sarki.

Aka baiwa dan aiken Buhari sako ya koma gareshi.

Da ranar da aka sanya tazo, sai kuwa ga ɗan aike ya komo ga sarki Abdullahi.

Don haka sai sarki ya anshi tubansa, ya aikewa sarkin musulmi Ahmadu sakon yadda sukayi da Buhari da numa lamarin tubansa.

An ce an samu zama lafiya da wannan sulhu na wani lokaci, amma daga baya sai Buhari ya sake komawa ruwa inda ya komo da fitinarsa sabuwa.

Buhari ya sake tashi tsaye yana cinye garuruwa.

An ce yacinye wani gari mai suna Jarma Disa tare da kwace dukiyoyin mutane da kuma kone gidardajinsu.

Sannan sai ya cinye wani garin shima mai suna Tashena.

Bayan yayi haka sai ya karasa garin Tsakuwa ya yada zangonsa acan.

Daga nan kuma sai ya nufi wani gari mai suna Birnin Babuje, ya shiga fada da dakarun garin da niyyar kwace iko dashi, amma cikin rashin nasara suka tarwatsa rundunarsa, suka sareshi da takobi da kuma sukarsa da mashi.

An ce a kasa dakarunsa suka jashi suna fatutikar tsira da ransu,

sannan daga baya suka ɗaukeshi izuwa Hadeja inda baifi kwanaki uku ba ya rasu.

Buharin Hadeja ya rasu ba tare da yayi gaba da gaba da sarkin Kano Abullahi ba a Fagen fama.

Wata nasarar da sarkin ya sake samu kuma itace ta korar sarkin Damagaran da akayi bayan ya kwace daura ya shige ciki yayi kaka-gida.

Wannan sai ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a zukatan jama’a ainun saboda hare-haren da yakan kawo jefi-jefi ga kanawa.

 

Za mu cigaba a makon gobe insha Allah.

 

Advertisement

labarai