Connect with us

TATTAUNAWA

Tarihi Shi Ne Shugaban Kowane Karatu  – Malam Ibrahim Khalil

Published

on

 

  • Ya Ce Abinda Ya Kada Kwankwaso A 2003 Ne Ya Kada Shekarau A 2011

A tattaunawa ta musamman da Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya ke cigaba da yi da fitaccen malamin addinin Islama kuma dan siyasa a jihar Kano, MALAM IBRAHIM KHALIL, duk mako, a wannan satin mun dora daga inda mu ka tsaya, inda malamin ya ke cigaba da bayanin misalai kan batun yadda a ka haihu a ragaya lokacin da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya tandara tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, da kasa a zaben 2003. Ga yadda malamin kum adan siyasa ya dora da bayani:

 

Kamar misali, gwamnan jihar Kano, Abubakar Rimi, ya yi aiki mai yawan gaske, amma saboda farfagandar siyasa ba za ka ji a na yabon sa ba, sai dai ka ji kawai an yabi Alhaji Audu Bako ko ka ji wani gwamna ya na zamaninsa ‘yan ba-ni-na-iya su ce ba a taba yin kamarsa ba. Farfaganda ta rufe Abubakar Rimi har ma ba a cewa ya yi wata bajinta a cikin wata 30 kacal da ya yi ya na mulkin jihar Kano. Shi ma gwamnan da ya ke kai da ya tafi, idan wani ya zo sai a ce ba a yi kamarsa ba.

To, kan maganar zaben 2003, malamai sun mara wa jam’iyya ANPP baya ne, saboda gwamnatin da ta ke kai ta PDP a lokacin ta ki fahimtar mutane. Da gwamnatin PDP a wancan lokacin ta fahimci mutane ta yi siyasa ta gane abinda su ke so, da ba za su je su zabi ANPP ba. To, duk lokacin da mai mulki ya ki ya fahimci jama’ar kasarsa; jama’ar kasarsa ga abinda su ke so, ga inda hankalinsu ya ke, amma ya ki karbar wannan abin, mai mulki idonsa ya rufe ya tafi a kan abinda ya ke so, to zai ga ba daidai ba kuma zai taimaki ’yan hamayya su samu goyon baya. Kamar misali, ita jam’iyyar ANPP din da ta zo ta kafa gwamnati sakamakon ita jam’iyyar PDP da ta ke da gwamnati ta sauraron jama’ar Kano su fahimci juna, ta yi watsi da tunaninsu, ta yi gaban kanta, ba ita ANPP din ta samu goyon baya ba, wacce da ita ce maras rinjaye? Amma ita ANPP din da ta hau daga 2003 har zuwa 2011 ita ma da ta ki fahimtar abinda mutane su ke so, ta ki ta saurare su, ta yi abinda PDP ta yi a 2003, ba ga shi an kifar da ita ba, ko? To, ai haka al’amura su ke. Don haka kullum abinda mutane ba sa tsayawa su kalla shi ne, meye ya haifar da kaza da kaza. Idan da PDP ta fahimci mutanen Kano, ta gane tunaninsu, ta yi mu su mu’amular da ta dace ta siyasa ta basira ta hikima, to da ANPP ba za ta zo a 2003 ba, kamar yadda ita ma ANPP da ta fahimci mutane ta yi siyasa, ta yi basira, ta yi karatun ta-nutsu, ta fahimci abinda ya afku a kan PDP a 2003, to da a 2011 ANPP ta yi nasara. To, amma ita ma sai giyar mulki ba ta ba ta dama ba.

Shi ya sa tarihi shi ne shugaban kowane karatu. Idan ba ka karanta tarihi ba, ba za ka gina rayuwar yau ba, ba kuma za ka fahimci gobe ba. Don haka shi ne sai a rika cewa ai malamai ne su ka kawo Malam Ibrahim Shekarau, a’a, ba wai malamai sun kawo ANPP ba ne ko sun kawo gwamna ba ne, a’a, malamai da jama’ar kasa gwamnatin PDP ta ki fahimtar su ne, ta ki sauraron su ne, ta ki yin abinda su ke so. Shi kuma dan adam duk lokacin da ba ka ba shi dama a kan abinda ya ke so ba, to zai yi nasa. Kamar ruwa ne; idan ba ka yiwa ruwa hanya ba, to zai yiwa kansa. Kamar mutum ne, idan ya zamana yaro ya na zaune ba ka sa shi wani aiki ba, to zai samar wa kansa aiki. Kamar yara ne da su ke shaye-shaye tunda ba a yi mu su wani abu da zai taimaki rayuwarsu ba, to za su yi abinda su ke ganin shi zai taimake su, shi ne su yi shaye-shaye ko su yi sace-sace. Duk ranar da ba a ba wa mutum damar da ya ke bukata ba, kuma ba ka fahimtar da shi ba, shikenan sai ya yi abu daidai fahimtarsa. Kamar jariri ne lokacin da uwarsa ta bar shi, ya ga babu mai yi ma sa wasa, shi kuma ya yi ta wasansa shi kadai babu mai taya shi, ya yi ta yin duk abinda zai yi babu wanda ya damu da shi, ya gaji da yi wasan kuma ya rasa abokin wasa kuma bau wanda ya kula shi, sai ya fashe da kuka; dole a zo a saurare shi.

 

To, amma ba ka jin cewa, hali ne na shugabanni su yiwa al’umma abinda ya ke shi ne mafi alheri ko da kuwa a lokacin ba su fahimce su, in ya so daga bisani sa gane?

To, ai ita giyar mulki idan ba ka da babban ma’auni; babban ma’auni shi ne ilimi na addini da hankali. Idan ba ka da wannan sai ka fadi. Meye hankali? Tarihi, fahimta, gane al’amura, kallon abu da fadi, tsayawa ka yi tunani mai zurfi. Shi ya sa addinin Musulunci da ilimi da hankali ya ke tafiya. Koyaushe Kur’ani ya na maganar ilimi ya na maganar hankali. To, mafi yawan lokaci masu mulki ba sa aiki da ilimi da hankali, su na yin aiki ne da abinda su ke ji na giyar mulki da jin mazuga su na zuga su su na cewa ai sai abinda su ka ce, sai abinda su ka ga dama za a yi. To, wannan giyar shi ya sa a ke cewa mafi yawan mutane giyar mulki ta na bata su.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: