TARIHI: Taƙaitaccen Tarihin Shehu Tijjani (RA)

Alhamdulillah…

Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, tsira da abincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bishi a kan tafarkinsa har zuwa ranar sakamako, yarda ta Allah ta tabbata ga shugaban Waliyyai Shehu Ahmadu Tijjani da kuma Khalifarsa Muɗ alaƙi Shehu Ibrahim Niasse da ma dukkanin masu imani baki ɗ aya.

Bayan haka, wannan taƙaitaccen tarihi ne na rayuwar Shehin Dariƙar Tijjaniyya, wato Abul Abbas Ahmadu ɗ an Muhammad Attijjaniy.

Sunansa dai shi ne Ahmadu, kuma shahararren laƙabinsa shi ne Tijjani, ana kuma yi masa alkunya da Abul-Abbas, sunan mahaifinsa Mahammadu ɗ an Mukhtaru, sunan mahaifiyarsa kuma A’isha ‘yar Muhammad Sanusi.

An haifi shehu Ahmadu Tijjani a garin Aini Madhi, cikin ƙasar Aljeriya a yanzu, a ranar 13 ko 14 ko 15 ga watan Safar na shekara ta 1150 bayan hijira, kuma ya fito ne daga dangi da suka saba da hidimar ilimin addini da karantarwa, laƙabinsa na Tijjani jinginawa ne zuwa ga ƙabilar da mahaifiyarsa ta fito wato TIJJANATA, kuma da yake dangin mahaifiyar tasa sun fi na mahaifinsa shuhra, sai shehu ya fi jingina kansa zuwa gare su har laƙabin Tijjani ya kama shi.

Shehu Tijjani ya kasance kyakkyawa ne da kowa ke son gani, farin Balarabe mai kewayayyiyar fuska mai manyan idanu da dogon hanci da yalwar baki, kansa na da yalwa cike kuma da baƙin gashi wanda yake sauka har ƙeya, yana da dogon wuya da hasken fata mai sheƙi, yana da fararen haƙora kuma tsaka-tsaki ne a tsayinsa. Waɗ anda suka gan shi ma dai suna cewa ya yi kama ƙwarai da gaske da kakansa Annabi sallallahu alaihi wasallam.

Shehu Tijjani ya rayu a tsakanin mahaifiyarsa da mahaifinsa har zuwa rasuwarsu, ya yi neman ilimi tuƙuru tun da ɗ anyar ƙuruciya cikin wata irin himma mai ban-mamaki, kuma ya bayyana cewa shi mai albarka ne da Allah ya nufa da wata baiwa ta musamman, domin tun yana da shekaru bakwai da haihuwa ya samu haddar Alƙur’ani mai girma da ruwayar Warshu, a hannun malaminsa mai suna shehu Muhammad bin Hamwu, sannan bayan ya haddace Alƙur’ani mai girma kuma sai ya cigaba da karatun ilimin addini a wajen wannan malami, Shehu Tijjani ya karanta littattafan sanin Shari’ar Muslinci a hannunsa, kamar Iziyya da Risala da Askari da waninsu, ya kuma cigaba da karatu a hannun wasu malaman bayan shi, an ce ya karance littafin Mukhtasar khalil a hannun Shehu Mabruku bin Bu’afiya, wanda kuma shi Shehu Mabrukun nan ya rasu ne fa a lokacin da Shehu Tijjani yana ɗ an shekara 16 da haihuwa, hakan na nufin shehu Tijjani ya ƙure fannin fiƙhu tun bai wuce shekaru goma sha shida ba a duniya. Shehu Tijjani ya ƙure dukkan malaman da ke kurkusa ta fuskar ilimi da karatu tun yana ƙarami, kuma ya soma ba da fatawa tun wannan hali na ƙanƙanta.

Mahaifin Shehu Tijjani da Mahaifiyarsa sun rasu ne a rana guda cikin wata annoba, a shekara ta 1166 bayan hijira, kuma a wannan shekara ne suka yiwa Shehu Tijjani aure kafin rasuwar tasu. Shehu Tijjani ya cigaba da maida hankalinsa zuwa ga ilimin sufanci da neman sanin Allah tun daga wannan lokaci, kuma daga bisani da ya soma samun bakin zaren, sai ya shauƙantu zuwa ga haɗ uwa da bayin Allah masana Allah waɗ anda za su sada shi da muradinsa, shi ya sa bayan shekarunsa sun kai 21 da haihuwa, sai ya nemi afuwar matarsa ya sauwaƙe mata, ya kama hanya cikin sahara don neman saduwa da muradin nasa, kamar yadda dama bayin Allah irin sa suka saba. A wannan fita Shehu Tijjani ya haɗ u da mazaje da dama, waɗ anda suke manya ne a walittaka da sufanci, kuma dukkansu ya amfanu da su kuma suma sun amfanu da shi. Daga irin manyan da ya haɗ u da su akwai shehu Mahmudu Alkurdiy wanda ya sadu da shi a Misra ‘Egypt’ a yanzu, kuma a wajensa Shehu Tijjani ya karɓ i Ɗ ariƙar Khalwatiyya, sannan ya yi wa shehu albishir da cewa zai samu matsayi babba a cikin walittaka. Haka na daga cikinsu akwai Shehu Muhammad binil Hasan wanda yaiwa shehu Tijjani Bushara da cewa zai taka muƙamin da shehu Aliyus Shazali ya taka, akwai Shehu Ahmadus Saƙali, da wasunsu da dama. Wani abin mamaki shi ne: Shehu Tijjani na zuwa wajen waɗ annan mazaje ne domin neman ya amfanu da abin da suke da shi na ilimi da ma’arifa, amma saɓ anin haka da zarar sun soma tattaunawa da shi, sai sama ta koma ƙasa, su zama su suke amfanuwa da shi saboda yawan baiwarsa ta ilimi da fahimta da hikimar magana.

Himmar Shehu Tijjani ta ja shi zuwa ga yin Aikin Hajji da kuma ziyarar kakansa Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam a shekara ta 1196 kuma shehu Tijjani ya tafi yana mai cigaba da abin da ya fara na bibiyar bayin Allah a kan hanyar tafiyarsa zuwa Makkah, ya shiga Makkah a shekara ta 1197 kuma ya yi Aikin Hajji a wannan shekara, a nan ne kuma ya je ziyarar Shehu Abdullahil Hindiy, sai dai ya tarar ya shiga khalwa basu sadu ba, amma sun yi musayar wasiƙu tsakaninsu, ya kuma tabbatar wa Shehu Tijjani cewa shi ne magajin sirrikansa baki ɗ aya. Bayan kammala Hajji sai shehu Tijjani ya shiga madina inda ya ziyarci Annabi sallallahu alaihi wasallam, a nan ne kuma ya sadu da Shehu Abdulkarimus Sammanu, sannan Shehu Tijjani ya kuma kamo hanya ya biyo sahara don komawa gida bayan kammala Hajji da ziyara, a kan hanyarsa ne kuma ya soma ganin Annabi sallallahu alaihi wasallam a karo na farko cikin tarihinsa, ya ga Annabi ido da ido, ya ce da shi ka bar dukkan wani Waliyyi da ka yi ratayo da shi, Ni ne shehinka Ni ne mai yi maka madadi, sannan ya umarce shi da karanta Istigfari 100 da salatin Annabi 100 kullum safe da yamma.. Wannan shi ne abu na farko da aka soma a Ɗ ariƙar Tijjaniyya, daga bisani a shekara ta 1200 bayan Hijira. Annabi sallallahu alaihi wasallam ya cikasa masa da Hailala 100, sannan aka bashi Wazifa da Zikirin Juma’a, sannan aka umarce shi da ya ba da waɗ annan wuridai ga wanda duk ya nema daga cikin jama’a, sannan Annabi ya yi masa alƙawarin cewa shi zai zama ƙofar tsiran dukkan wanda yai ruko da Ɗ ariƙarsa.

Bayan dawowar Shehu Tijjani, ya tare ne a garin Fas babban birnin Maroko a yanzu, kuma a nan ya cigaba da rayuwa har zuwa wa’adinsa ya cika.

Shehu Tijjani ya sayi bayi mata guda biyu ya ‘yanta su kuma ya aure su, su ne: Sayyida Mabruka da Sayyida Mubaraka, kuma da su ya rayu har suka Haifa masa ‘ya’ya, Shehu Tijjani ya rasu ya bar waɗ annan mata da kuma ‘ya’yansa biyu: Sayyidi Muhammadul Kabir da Sayyidi Muhammadul Habib, ya kuma rasu ne a shekara ta 1230 bayan Hijirah yana da shekaru 80 a duniya, Allah ya bamu daga cikin albarkarsa.

Wal Abdulillah…

Muhammad Nazifi Bichi, Malami ne a Sashen Nazarin Larabci na Jami’ar Bayero da ke Kano.

08066929640

mnbichi.ara@buk.edu.ng

 

Exit mobile version