Abu Hidaya" />

Tarihin Bikin Bianou A Agadez Ta Nijar

Gabatarwa

A bisa al’ada duk shekara mutanen garin Agadez da ke Jamhuriyar Nijar kan yi wani biki da a ke kira bikin Bianou, kuma su kan gayyaci mutane daga sassa daban-daban na duniya ciki kuwa har da ‘yan jaridun duniya tare da kungiyoyi, gami da hukumomin da su ke na al’adu ne.

Mene Ne Bianou?

 

Bianou sallah ce ta Abzinawa mutanen Agadez. Su na fara yin wannan bikin tsawon wasu kwanaki, amma manyan ranakun bikin su ne ranakun Tasu’a da Ashura, don a na fara bikin tun ranar 17 ga watan Zhul-hijja ne. An ce bikin ya samo asali tun iyaye da kakanni.

Mene Ne Tarihin Bianou A Takaice?

A hakikanin zance babu wanda zai ce ga shekarar da a ka soma bikin Bianou a garin Agadez, amma dai an tabbatar da cewa tarihin bikin Bianou ya samo asali tun shekaru masu yawa, kuma a na yin wannan biki ne saboda kwaikwaiyon Ma’aiki (SAW)a lokacin da ya yi hijira daga Makka zuwa Madina, inda mutanen Madina su ka fito su ka tare shi da murna. Wasu kuma su ka ce Bianou biki ne kawai na al’ada da a ke yi, don samun nishadi da kuma raya al’adar kasar, don bayyanawa duniya karfin da matasa su ke da shi a garin Agadez. Da wani ya ke karin bayani game da wannan magana ya ce, “ma’anar Bianou shi ne a yi ta rawa sai gari ya waye”. Wannan shi ne tarihin Bianou a takaice.

Maraicen Ado

Ita wannan rana mai suna Maraicen Ado mata ne ke yin kwalliya da yamma su fito gari, amma kafin yammacin wannan rana ko wane gida a na yin abinci nau’ika daban-daban, amma da alkama kuma akwai wadanda su ke ajiyar naman kai da kuma kashin bayan ragon layyarsu, inda a wannan rana su ke fitowa da shi su gyara a ci. Zuwa yammacin sai kuma samari da Tambari tTambari shi ne shugaban da ya ke jagorantar masu yin bikin) su ma su fito a shiga kada tambura (manyan ganguna), a yi ta rawa har zuwa wani tudu da a ke kira tudun Bianou. Wannan rana ita ce kamar ranar bude Bianou ko kuma jajiberin sallar Bianou. Kuma a wannan yammaci maza ke tafiya kwanan daji.

Kwanan Daji

Kamar yadda na fada a baya, a na fara bikin Bianou tun 17 ga watan Zhul-hijja, amma manyan ranakun bikin guda uku ne, su ne kamar haka:

1Maraicen Ado

2 Ranar sallar Bianou

3 Ranar kare wasa ko Tudun makera

To, kamar yadda bisa tsarin da al’adar Bianou ta tsara da an gama maraicen ado sai mazaje masu sha’awar kwanan daji su shirya su wuce daji domin kwana a can don yin shirin washe gari wadda a ke yi wa lakabi da ranar sallar Bianou sunan dajin da a ke zuwa dajin Alansis ya na nan kilo mita biyar da garin Agadez. Dajin dauke ya ke da bishiyun dabinai da kuma ’yan bukkokin mutane mazauna dajin.

Abubuwan Da A Ke Yi A Dajin

Da ya ke masu kwanan dajin sun kasu kashi biyu, akwai mutanen Gabas da kuma na Yamma, don haka ko a dajin ka shiga sai ka fara wuce mutanen yamma sannan za ka iske mutanen gabas.

Abubuwan da a ke yi a wannan dare yawanci a kan dora girki wanda kwamitin masu kula da shirya wannan biki su ke daukar nauyin yi, wasu kuma su kan taho da abincinsu tun daga gida a kunna wuta a gefe a yi ta hira har gari ya waye, to amma yanzu masu wasa kan je daga cikin gari a kunna wutar lantarki a yi wasanni da wakoki har wani adadi na dare, sannan a koma makwanci.

Zuwa da safe kuma sai a ci abinci a yi shiri a nufo gari. ‘Yan yamma su ke fara yin gaba sannan yan gabas na biye da su. Dalilin da ya sa a ke wannan kwanan daji shi ne don raya waccan Sunnar ta Ma’aiki inda wadanda su ka yi wannan kwanan daji da safe za su yi shiga ta al’ada su shigo gari su na kada tambari da akanzam (Akanzam wani karamin bandiri ne) su na waka da rawa, su kuma mutanen gari su fito su tarbe su. Kowannesu ya na rike da ganyen dabino su na jinjina mu su tare da yi mu su lale marhaban, kamar dai yadda ya faru a lokacin hijirar Ma’aiki (S.A.W) daga Makka zuwa Madina.

Ranar Sallar Bianou Ko Daukar Tazidai

Ita kuma wannan rana ita ce rana ta biyu a manyan ranakun Bianou kuma ita ce babbar ranar da kowa ya ke yin kwalliya da abinci don nuna murnarsa. A wannan rana kowa kan fito rike da tazidai (ganyen dabino), don tarbar mazajen da su ka yi kwanan daji. A kuma ranar ne kusan gabadaya a ke zagaye gari. Amma kafin a shiga gari malamai kan tarbi mazajen Bianou a wajen gari a yi addu’o’i, sannan sai a shiga gari da gidajen iko (mahukunta) a na kada mu su tambari da akanzam tare da rera wakoki. Yawanci gidajen da a ke zuwa wasu kan bayar da abinci ko fura a sha. Bayan an gama wannan zagaye sai kuma a wuce gidan Sarkin Agadez (Sultan) a gaishe shi. Shi kuma sarki ya yi nasa jawabin. Sai kuma a wuce zuwa cikin gari a yi ta wasanni da rawa da juyi har zuwa yamma, sai a ajiye sai kuma gobe.

Ranar Kare Wasa Ko Tafiya Tudun Makera

Ita wannan rana ta kare wasa ko tafiya tudun makera ita ce rana ta uku daga cikin manyan ranakun Bianou kuma ita ce rana ta karshe a wannan biki. Wasu ma kan kira ta da ranar cikon shekara. Ita wannan rana ba kowa ne ke fitowa ba. Akasari ma ranar matasa sun fi yawa a ciki kuma dalilin da ya sa a ke Bianou a wannan rana shi ne domin a tafi Tudun Makera, saboda ’yan Makera a garin Agades sun kokawa sarki cewa ba a zuwa wurinsu a na yi mu su wasan Bianou, domin su na gabas da gari. Don haka sarki ya sanya a dinga zuwa a na yi mu su nasu wasan, don inganta da armashin wannan biki, amma kafin a kai ga tafiya Tudun Makera sai an zagaya gari a na yin wasa kamar kowacce rana ta Bianou, inda mata da maza su ke fitowo su na kallo su na yabawa samarin da su ka yi kwalliyar birgewa, kamar yadda a ke hawan sallah a arewacin Nijeriya. Zuwa can yamma sai a wuce Tudun Makera a yi wasa. Daga nan kuma an gama Bianou sai wata shekarar. Don haka ne ma a ke kiran wannan rana da wannan rana da ranar kare wasa. Har ila yau a wannan rana ne ’yan gabas da yamma su ke Randayya (wato nuna bajinta ko gasar rawa, kida da kuma kwalliya).

Agadez dai ita ce jiha ko kuma yankin da ya fi kowanne yanki girma a Nijar, wanda girmansa ya kai murabba’in kilo mita 634,209, wato kwatankwacin kashi 52 cikin 100 na girman Nijar bakidaya.Yankin Agadez ya hada da hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Ayir mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama’ar yankin Abzinawa ne; akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa. Babbar sana’ar jama’ar yankin ta asali ita ce cinikin gishiri da dabino. Sai dai a shekarun 1990 harkar bude ido ta zama wata babbar sana’ar yankin. Haka nan karfen ma’adanin Uranium da a ke samu a garin Arlit na samawa Nijar kashi 20 cikin dari na kudin shigar da ta ke samu. A ‘yan shekarun bayan sun sha fama da ta’adaccin tawaye da fari (rashin albarkar noma) da a ka rika samu wadanda su ka kai yankin ga shiga wani hali na durkusar da tattalin arzikin yankin, amma yanzu komai ya na dawowa daidai, musamman ziyarar baki ‘yan kasashen waje da kuma bunkasar tattalin arzikin yankin mutanen Agadez; mutane masu son baki da kuma girmama su.

Su na da guraren tarihi masu yawa kamar babban masallacin Agadez da Tafadak da Tchirro da Arlit da dutsen Bagazam wadanda su ke cike da abubuwan al’ajabi.

Rabi’u Muhammad, wanda a ka fi sani da Abu Hidaya mazaunin birnin Kano ne a Tarayyar Najeriya, ya halarci bikin Bianou a Jamhuriyar Nijer. Za a iya samun sa a +2348065025820 ko abuhidya@gmail.com

Exit mobile version