Tarihin Gasar Cin Kofin Duniya A Takaice

Kofin Duniya

Ana shirya gasar cin kofin kwallon kafa na duniya ne a cikin ko wacce shekaru hudu, gasar cin kofi ta farko an tsara ta a shekara 1930 a kasar Uruguay inda aka yi wasan karshe tsakanin mai masaukin baki da kasar Argentina, kuma Uruguay din ta samu nasarar lashe kofin.

An yi karo na biyu na gasar a shekarar 1934 a kasar Italiya, inda Italiya ta dauki kofin bayan ta doke kasar Chekoslobakiya sannan an yi gasa ta uku a Faransa a shekara 1938 a wannan karo ma Italiya ce ta lashe kofin bayan ta doke Hungary a wasan karshe.

Daga wannan shekara sai aka dakatar da tsara gasar, saboda barkewar yakin duniya na biyu. Sai a shekarar 1950 bayan kwanciyar hankali ta dawo a duniya, Brazil ta shirya gasa ta hudu inda Uruguay ta lashe kofin.

Sannan an yi gasa ta biyar a kasar Switzerland a shekara 1954, karon farko Jamus ta Yamma ta zama zakara bayan ta cinye tawagar ‘yan wasan kasar Hungary a fafatawar wasan karshe da suka yi.

Shekaru hudu bayan wannan kungiyoyin kwallo su ka hadu a kasar Swedin nan Brazil ta ci kofin sannan a shekara ta 1962 kasar Chile ta karbi bakuncin wassan, kuma Brazil ta gaji kanta da kanta a matsayin zakara ta shekarar.

A shekara 1966 Birtaniya ta shirya gasar kuma ita ta ci kofin, sai kuma a shekara ta 1970 Medico ce ta shirya wasan kwallon na duniya kuma Brazil karo na uku ta dauki kofin, sannan sai Jamus ta sake maimaita daukar kofin karo na biyu a shekara 1974 a wasan da ta shirya.

Sai kuma a shekarar 1978 kasar Argentina ta shirya gasar kuma ita ta ci kofin karo na farko, bugu da kari a shekara hudu bayan hakan Sipaniya ta shirya gasar kuma Italiya ta kwaci kofin daga hannun Argentina.

A shekara 1990 Italiya ta dauki bakuncin gasar kuma kasar Jamus ta ci kofin bayan ta doke Argentina sannan a shekara 1994 an yin wasan a Amurka a nan Brazil karo na hudu ta samu nasara.

Kasar Faransa ta dauki nauyin gasar karo na 16, kuma a karon farko ita ta lashe kofin sai kuma a shekara ta 2002 kasashen Koriya ta Kudu da Japan su ka hada karfi domin shirya gasar a nan ma Brazil ta dauko

kofin.

Kasar Jamus ta dauki nauyin shirya gasar a shekara ta 2006, inda Italiya ta samu nasara. Sai kuma wanda a ka buga a kasar Afirka ta Kudu, inda karon farko kasar Sipaniya ta samu nasara lashe kofin. A shekara ta 2014 kasar Brazil ce ta shirya gasar cin kofin kuma kasar Jamus ce ta lashe bayan ta samu nasara a kan tawagar ‘yan wasan kasar Argentina da Messi yake jagoranta. Sai kuma a shekara ta 2018 kasar Rusha ta dauki nauyin gasar kuma kasar Faransa ta lashe.

A yanzu dai kasashe suna nan suna ta shiryawa domin ganin sun samu damar halartar gasar wadda za’a fafata a kasar Katar a shekara ta 2022 mai kamawa kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta tsara.

Kasar da ta dauki nauyi da Wadda ta lashe kofin da sakamako

Wadda ta dauki nauyi     Wadda ta lashe                sakamako

 

2018 Russia                        Faransa                            Faransa 4-2 Croatia

 

2014 Brazil                           Jamus                              Jamus 1-0 Argentina

 

2010 Afirka ta Kudu             Spain                                  Spain 1-0 Netherlands

 

2006 Jamus                        Italiya                                  1-1, bugun fenarati da Faransa 5-3

 

2002 Japan / S. Korea     Brazil                                       Brazil 2-0 Jamus

 

1998 Faransa                     Faransa                                 Faransa 3-0 Brazil

 

1994 Amurka                     Brazil                                     0-0, bugun fenarati da Italiya 3-2

 

1990 Italiya                         Jamus                                   Jamus 1-0 Argentina

 

1986 Mexico                      Argentina                               Argentina 3-2 Jamus

 

1982 Spain                          Italiya                                     Italiya 3-1 Jamus

 

1978 Argentina                 Argentina                                 Argentina 3-1 Holland

 

1974 Jamus                        Jamus                                        Jamus 2-1 Holland

 

1970 Medico                      Brazil                                         Brazil 4-1 Italiya

 

1966 Ingila                         Ingila                                        England 4-2 Jamus

 

1962 Chile                           Brazil                                        Brazil 3-1 Czechoslobakia

 

1958 Sweden                    Brazil                                             Brazil 5-2 Sweden

 

1954 Switzerland             Jamus                                               Jamus 3-2 Hungary

 

1950 Brazil                          Uruguay                                           Uruguay 2-1 Brazil

 

1946 ba a yi ba

 

1942 ba a yi ba

 

 

1938 Faransa                     Italiya                                                                    Italiya 4-2 Hungary

 

1934 Italiya                         Italiya                                                                    Italiya 2-1 Czechoslobakia

 

1930 Uruguay                    Uruguay                                                               Uruguay 4-2 Argentina

Exit mobile version