Connect with us

Madubin Rayuwa

Tarihin Kabilar Kalenjin Da Farin Jemagen Da Ya Sa Su Hijira

Published

on

Wadanda suka yi imanin cewa, Fatalwar matattu kan iya shiga sha’aninsu na yau da kullum.    

A wannan mako mun kewaya muka kuma kutsa cikin duniya, inda muka ci karo da mutanen kalenjin, filin namu na yau zai sada ku ne da mutanen kalenjin da ke zama a tsaunukan rift na sashen kasar kenya.

A kiyasi za su kai mutum kimanin miliyan 4.9 a kidayar da aka yi na shekarar 2009. Sun rabu kashi-kashi, akwai su kipsigis, Nandi, keiyo, marakwet, sabaot, pokots, tugen, terik, da kuma ogiek/dorobo. Duk amma yaren na kalenjin suke yi. Asalin su daga chan wata kasa ne da ake kira da Emet ab Burgei. Ma’anarsa kasa mai zafi.  An ce sun yi hijira ne zuwa kudu ta inda suka bi ta dutsen Elgon ko tulwet ab kony a cikin kalenjin nan wasu suka yada zango wasu kuma suka kara gaba don neman kasa mai albarka. Kabilar keiyo da mara kwet suka zauna a tsaunin kerio da tudun cherangani, pokot kuma a arewa da dutsen Elgon kafin kuma daga bisani suka bazu a wuraren Arewacin Baringo. Chan ma a Baringo tugan suka ware daga cikin nandi da kipsigi.

A lokacin farin kemeutab reresik ma’ana Farin jemage, an ce a lokacin wannan farin jemage ne ya kawo ciyawa wadda aka Dauka a matsayin Alherin da zai kawo karshen yunwa, ya kuma nuna musu hijira ya dace a yi zuwa wuri mai yalwar ciyawa don haka mutanen tugen sai suka yi hijira zuwa wuraren tudun tugen su kuma kipsigi da nandi zuwa rongoi dan kipsigi da nandi an ce tare suke. Sun yi zama sosai har na tsawon karni daya kafin daga bisani rabuwa ta zama musu dole.

Kabilar kalenji isowarsu kenya an sansu da noma da kiwo, suna kiwon shanu, tumaki, da Awaki da kuma noma.

Addini

A yau kabilar ta kalenji masu riko ne da addini, don kuwa kusan ko wane mutum yana da addininsa ko musulunci ko kuma addinin kiristanci. Suna da Coci, kamar su Africa Inland Church (AIC) akwai kuma Church of the Probince of Kenya (CPK) a karshe kuma akwai Roman catholic church.

Su ma suna da addininsu na gargaji inda suka yarda da Ubangijinsu Asis ko Chaptalel wadda a wurinsu yake a matsayin rana, duk da cewa ita rana ba ita Ubangijin na su kai tsaye ba, kasan Asis akwai Elat, wadda shi ne ke ba da umurnin tsawa da kuma walkiya.

Sun yi imanin cewa Fatalwar matattu  kan shiga sha’anin su na yau da kullum, don haka dole ana dan ba su cin hancinsu nama, giyar da suke kira koros, sai kuma matsafa wadda ake kira da orkoik su ma an yi imani cewa, suna da ikon saka wa ayi ruwa, ko kuma karshen ambaliyar ruwa. Amma fa sai dai in manya ko kakanni ne kadai kan iya ba da labarin wannan addini nasu na gargajiya don kuwa Yanzu sun zama tarihi.

Sutura

A al’adance su kan dinka kayan su ne daga fatar dabbobin gida, ko kuma na jeji daga mazansu har matansu kan makala dan kunnen da aka hada da karafu masu nauyi har yakan ja kunnen ya sa yayi tsayi har zuwa kafada. Amma a Yanzu sun canza zuwa kayan zamani

 Abinci

Ugali, abinci ne da ake yi da garin masara, alkama ko kuma gero. Shi ne abincinsu sannanne kamar sauran kabilun Kenya, su ma suna amfani da hannunsu wajen cin abinci kamar wannan Ugali din akan ci da daffaffen koren ganye kamar Kale.

Nama kuwa suna cin gasasshiyar Akuya, Saniya, ko Kaza. Sai kuma mursik wata madara da ake ajiyar ta a wuri na musamman.

Kamar in mutum ya girma a kan yi masa wani bikin da ake kira ‘tumdo’ wadda a nan ake kaciya maza da mata duka ana musu wannan biki.  A al’adance akan yi  bikin ne bayan ko wace shekara bakwai, inda akan yi wa ‘yan shekarar da aka yi wa bikin suna da ‘ipinda. Bayan kaciya Sai a yi wa matasan ‘yar lakcha a kan girma, sai kuma su shiga shekarun mayaka inda za’a fara koya musu dabarun fada.  Shi kuma kaciya wa matan yana nuna cewa sun isa aure kenan.

 Auratayya

Aure abu ne mai muhimmanci a al’adar Kalanjin. Bayan aure maza kan dawo da matayensu cikin danginsu har ila yau suna rayuwar gandu duk da Yanzu yanayin arziki ya ja baya, dan Yanzu sadaki ma kadai ya zama aiki a wurinsu, da dama daga cikinsu, don haka rayuwar mata da mijin ta da yara shi aka fi yi, rayuwar gandu yayi karanci. Da yara da yawa a wurinsu bai wa ne don haka a kan haife su da yawa, amma a Yanzu yaran zamani sun fi son su haifi kadan za’a iya alakanta hakan da matan Yanzu da suka zabi aiki fiye da haihuwa da renon yara da kuma dubi da yadda tarbiya da ilimantar da yaran yayi tsada.

Maza kan yi aikin karfi kamar su noma, gini, kiwo da dai sauran su, inda mata kuma kan yi sauran aikace-aikacen gida A bangaren noma kuwa su kan yi shuka.  Yawancin mutanen Kalenjin mutane ne na karkara wadda ba su da wutar lantarki, ko kuma ruwan famfo.  Suna gininsu na gargajjya da laka da kashin shanu, shi kuma saman bukka a rufa da ciyawa.
Advertisement

labarai