Kibaku kamar yadda aka rubuta shi iri-iri ne na Cibak. Cibak shi ne ainihin tushen sananniyar al’ummar Arewa maso Gabas, Chibok. Saboda haka, Kibaku ainihin Cibak ne ko kuma an fassara shi iri daban-daban kamar kowane dayan masu zuwa: Chibuk, Chibok, Chibbak, Chibbuk, Kyibaku, Kibbaku, Kikuk. Harshe ne na Afro-Asiatic wanda kusan mutane 200,000 ke magana da shi a Nijeria. Ana magana da Cibak a kananan Hukumomin Askira / Uba, Chibok da Damboa da ke Kudancin Jihar Borno a Nijeriya.
Ginshikin mutanen Kibaku
Dangane da al’adar baka, Kibaku hadakar kabilanci ce ta Babir / Bura, Kanuri, Kilba, Margi, Shuwa, da Fulani. Sun zo tsaunukan Chibok ne tun daga kusan karni na 18 lokacin da Daular Kanem-Bornu ta wargaje. Jihadin karni na 19 da kuma hare-haren bayi zai tilasta wa kabilu da yawa kaura daga wurarensu na asali zuwa sababbin wurare domin neman mafaka. Kuma a sakamakon haka, tsaunukan Chibok sun kasance mazaunan Pulai / Warga wadanda suka zo daga hanyar biyu Kithla (Biu) da Kwanda wadanda suka zo daga Konduga, Tstitihil daga Maiba, Karagu daga Birnin Ngazargamu da sauran wurare.
Mutanen Kibaku wadanda a dabi’ance ba su da tsoro kuma jarumai ne, sun hada da dangi daban-daban har guda 38 wadanda suka hada da Pulai, Mungai, Tsitihil, Whuntaku Pirkiu, Midiraku, Kagyau, Kwapul, Kwangwala, Gaskil, Ngiwar, Kwapurai, Njir -Dawa, Aduwarama da Hirpaya. Wadannan kungiyoyin daban-daban ne suka kafa kabilar Kibaku kuma suka habaka yaren Kibaku. Ko ma dai yaya, ba su mallaki wata hukuma ta musamman ba. Suna zaune kawai a cikin al’ummomin masu cin gashin kansu.
Kibaku da Tsarin Gargajiya
Bisa ga al’adar baka, an bayyana cewa a wani zamanin da ya gabata, idan wani sarki a Biu ya mutu, sabon basaraken wanda zai dauki matsayin wadanda suka tafi a kan dauke shi zuwa Chibok don yin wani abin girmamawa kafin a rantsar da su. Bayan isowarsa, “‘Yar Chibok” za ta taimaka masa don hawa dutse (da ake kira’ Muyar Patha ‘) a cikin garin Wantaku kuma za a yi masa nasiha game da shi kafin a mayar da shi Biu don yin nadin sarautar.
Ga mutanen Kibaku, a zamanin da ana kiran Sarakunansu da “Mai” (wanda a wasu lokuta ake fassara shi a ma’anar Hausa da ‘Mai shi’ ko ‘Wanda ya yi’ ko ‘Wanda yake da shi gwargwadon mahallin). Saboda haka, idan aka ambaci mutum misali da ‘Mai Unguwa’, ana nufin ‘Mai garin’ ko ‘wanda yake da garin’. Daga cikin farkon ‘Mais’ na mutanen Kibaku akwai Mai Jatau, Mai Njaba, Mai Gana. A cikin ‘yan kwanakin nan, ko da yake, Mais an mai da shi ya zama shugaban gundumar karkashin Masarautar ta Borno.
Yana da muhimmanci a kuma lura cewa, kamar yawancin kabilu a duk fadin Nijeriya, shugabancin dangi tsakanin mutanen Kibaku ya dogara da shekaru.
Labarin Kibaku Mai Ban Sha’awa da Burgewa.
Mutanen Kibaku suna da labari na musamman guda daya da suka dauka tsawon lokaci kamar haka:
Kibaku ya taba samun sarki wanda wurin zamansa yake a kan duwatsu kuma yana da gadon sarauta wanda aka ba wa talakawansa damar zuwa kawai ta wurin zama suna fuskantar kansa. Ba a ba wa talakawansa damar su dube shi ba saboda haka, ba su taba dubansa ba. Amma Turawan Ingila sun zo ne cikin ikonsu don yi wa mutane mulkin mallaka kuma a lokacin da abin ya ba da mamaki cewa Chibok ba za ta iya jure karfin Ingilishi ba, wannan sarki ya yanke shawarar bacewa cikin tsaunuka na dindindin maimakon mika wuya ga ikon mulkin mallaka. Dalilin bacewar Sarki ya bayyana a cikin wadannan kalmomin:
“Idan sarki ba zai iya zama sarki kamar yadda sarki ya kamata ya zama sarki ba, babu sarki gaba daya,”
Gaskiya mai ban sha’awa Game da Mutanen Kibaku.
Wani abin ban sha’awa da aka bayyana game da mutanen Kibaku a Chibok shi ne wuri na karshe a Nijeriya da zai mika wuya ga turawan Ingila. Kuma ga mutanen Kibaku, wannan abin alfahari ne; alama ce ta rashin tsoro da jarumtaka.